Wata Sabuwa Ta Bullo, An Yi Hasashen Abin da Sojojin Amurka Za Su Yi a Najeriya

Wata Sabuwa Ta Bullo, An Yi Hasashen Abin da Sojojin Amurka Za Su Yi a Najeriya

  • Manjo Janar Ijioma N. Ijioma (mai ritaya) ya ja hankalin yan Najeirya da kada su yi tsammanin sojojin Amurka za su fita fagen yaki
  • Ya ce sojojin da Amurka ta turo Najeriya za su taimaka ne ta wasu fannonin amma ba za su fita su yi gaba-da-gaba da 'yan bindiga ba
  • Ya kuma bukaci 'yan Najeriya da su tuhumi shugabanninsu kan yadda aka iya tura jiragen sojoji Benin don murkushe shirin juyin mulki

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Bayan turo sojojin Amurka zuwa Nijeriya domin taimakawa wajen yakar ta’addanci, tsohon Daraktan Ayyuka na Hedikwatar Rundunar Sojin Kasa, Manjo Janar Ijioma N. Ijioma (mai ritaya), ya yi gargadi ga ’yan Nijeriya.

Tsohon babban sojan ya bukaci yan Najeriya da kada su sa ran cewa dakarun Amurka za su fuskanci ’yan bindiga kai-tsaye a fagen fama.

Kara karanta wannan

Zance ya kare, hedkwatar tsaro ta yi magana kan sojojin Amurka da aka turo Najeriya

Sojojin Amurka.
Dakarun sojojin Amurka na shirin hawa jirgi domin fita aiki Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Sojojin Amurka sun shigo Najeriya

A makon jiya ne Amurka ta turo wata karamar tawagar sojojinta zuwa Najeriya domin taimaka wa wajen yaki da ta'addanci, kamar yadda Tribune Nigeria ta kawo.

Shugaban rundunar Amurka mai kula da Afirka (AFRICOM), Janar Dagvin R. M. Anderson, ya bayyana cewa tawagar na dauke da wasu dakaru masu kwarewa na musamman.

Ya ce an dauki wannan mataki ne don karfafa hadin gwiwa tsakanin Najeriya da Amurka bayan kasashen biyu sun amince cewa akwai bukatar kara kaimi don dakile ta’addanci.

Janar Ijioma ya caccaki gwamnatin tarayya

Yayin da yake tsokaci kan zuwan sojojin Amurka, Manjo Janar Ijioma ya zargi shugabannin Nijeriya da rashin kishin kasa na gaske wajen fuskantar ’yan bindiga da ’yan ta’adda.

Jaridar Vanguard ta ruwaito tsohon sojan na kara jaddada cewa sojojin Nijeriya ne kawai za su iya murkushe 'yan ta'addan a karshe.

A cewarsa, da a ce gwamnatin tarayya ta bi yakin Biafra na shekarar 1967 da "lallashi" kamar yadda ake yi wa ’yan bindiga da Boko Haram a yau, "to da tuni an dade da samun Jamhuriyar Biafra."

Kara karanta wannan

Da gaske sojojin Amurka sun cafke Sheikh Ahmed Gumi a filin jirgi? Gaskiya ta yi halinta

Mene ne dalilin Amurka na turo sojoji Najeriya?

Tsohon Janar din ya bukaci ’yan Najeriya da su tuhumi shugabanninsu kan dalilin da ya sa ake bi da ’yan ta’adda cikin sauki da lalama.

"Amurka ba ta sanya rayukan sojojinta cikin hadari a banza," in ji shi, inda ya bukaci ’yan Najeriya su tambayi wace irin yarjejeniya ce ko diyya ke tsakanin Nijeriya da Amurka.

Ya kuma tambayi dalilin da ya sa aka tura jiragen yakin Nijeriya kasar Benin cikin gaggawa don dakile yunkurin juyin mulki, amma ’yan bindigan da ke kashe mutane kullum ke ci gaba da cin karensu ba babbaka.

Shugaba Tinubu.
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da Shugaba Donald Trump na Amurka tare da sojoji Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Wane aiki sojojin Amurka za su yi?

Manjo Janar din ya jaddada cewa:

"Sojojin Amurka ba za su fito filin daga don yin yaki da yan bindiga ba. Nauyin kakkabe mahara yana wuyan Rundunar Tsaron Nijeriya ne.
"Abin da sojojin Amurka za su yi kawai shi ne bayar da horo, bayanan sirri, da tallafin kayan aiki da na fasaha, amma ba za su fita filin daga a fafata da su ba."

Kara karanta wannan

Tirkashi: An yanke wa tsohon manajan banki hukuncin daurin shekaru 490 a kurkuku

Hedkwatar tsaro ta tabbatar da zuwa sojojin Amurka

A wani rahoton, kun ji cewa Hedkwatar tsaron Najeriya ta yi karin haske kan batun turo sojoji kasar Amurka domin taimakawa wajen yaki da ta'addanci.

Hedkwatar tsaron ta kuma share tantamar mutane, inda ta ce Amurka ta shigo da sojojin ne bisa tsari da girmama ’yancin Nijeriya.

Hedkwatar Tsaron ta tabbatar wa 'yan kasa cewa duk wata mu'amala da take yi da abokan hulda na kasashen waje tana yin ta ne don kare muradin kasa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262