Ana Jimamin Harin Kwara, 'Yan Boko Haram Sun Kashe Sojojin Najeriya
- 'Yan ta'addan Boko Haram sun shirya wani harin kwanton bauna kan dakarun sojojin Najeriya a jihar Borno da ke Arewa maso Gabas
- Tsagerun 'yan ta'addan sun shirya kwanton baunan ne lokacin da sojojin ke kan hanyar kai daukin gaggawa a cikin daji
- Harin ya jawo an samu asarar rayukan sojoji wadanda suke sadaukarwa wajen kare kasar nan daga barazanar 'yan ta'adda
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Borno - Ana fargabar cewa sojoji huɗu sun rasu bayan harin da ’yan Boko Haram suka kai musu a jihar Borno.
'Yan ta'addan na Boko Haram sun kai musu harin na kwanton bauna ne a Auno, kusa da Jakana a kan titin Maiduguri–Damaturu a jihar Borno.

Source: Twitter
Jaridar The Punch ta kawo rahoton cewa lamarin ya faru ne a daren Alhamis, 5 ga watan Fabrairun 2026 da misalin karfe 10:50 na dare.
Yadda 'yan Boko Haram suka kashe sojoji
Wasu sojojin da ke aiki a yankin sun ce an yi wa dakarun kwanton bauna ne a lokacin da suke kan hanyarsu ta kai ɗauki ga abokan aikinsu da aka kai musu hari.
Wani soja da ya nemi a sakaya sunansa, ya bayyana a ranar Juma’a cewa ’yan ta’addan sun shirya kwanton bauna mai tsanani, inda suka yi amfani da nakiyoyi da ake sarrafawa.
"Mun rasa sojoji a wurin. Sun yi musu kwanton bauna daren jiya. Dakarun sun je domin kai ɗauki, kuma sojoji huɗu suka mutu nan take."
"Wurin da abin ya faru shi ne bayan ka wuce Jakana daga Damaturu, akwai wani ƙauye mai suna Auno ƙarƙashin Bataliya ta 3. Boko Haram sun kai harin ne da misalin 10:50 na dare."
"Sojojin da aka kashe su ne wadanda ake ajiyewa don ko ta kwana, idan aka kai hari, su ake tura wa don kai ɗauki. A kan hanyarsu ne Boko Haram suka yi musu kwanton bauna mai tsanani da nakiyoyin da ake sarrafawa.”

Kara karanta wannan
Ana fama da rashin tsaro, 'yan sanda sama da 5,000 za su ajiye aiki, an ji dalili
- Wani soja
An rasa rayukan sojoji a Borno
Wani jami'in tsaro ya bayyana sunan ɗaya daga cikin waɗanda suka rasu da Saidu, yana mai bayyana shi a matsayin soja mai barkwanci da annashuwa, jaridar TheCable ta kawo labarin.
"Ni da Saidu muna zama a bariki ɗaya. Mutum ne mai barkwanci sosai. Suna kan hanyarsu ta ceto wasu sojoji da ake kai musu hari ne lokacin da suka faɗa cikin tarkon kwanton baunar."
- Wani jami'in tsaro
Me hukumomi suka ce game da harin?
Kokarin jin ta bakin mai magana da yawun Operation Hadin Kai, Laftanar Kanal Sani Uba, bai yi nasara ba.

Source: Original
Kakakin na Operation Hadin Kai bai ɗaga waya ba kuma bai kira daga baya ba har zuwa lokacin da aka haɗa wannan rahoto.
Auno, wanda ke da nisan kilomita 24 daga Maiduguri a kan titin Maiduguri–Damaturu, ya dade tana fuskantar matsanancin rashin tsaro.
Ana ɗaukar shi a matsayin hatsabibin wuri na ayyukan ’yan Boko Haram/ISWAP, inda ake yawan kai hare-hare kan shingayen sojoji da fararen hula a ’yan kwanakin nan.
Sojoji su dakile harin 'yan bindiga
A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun sojojin Najeriya da ke aikin samar da tsaro a jihar Sokoto sun samu nasara kan 'yan bindiga.
Sojojin na rundunar Operation Fansan Yamma sun dakile wani hari da ’yan bindiga suka kai kauyen Kola da ke karamar hukumar Salame.
Hakazalika, rundunar ta samu nasarar kwato tumaki 48 da ’yan bindigan suka kwashe daga hannun mazauna kauyen a yayin harin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

