Akwai Kura: Kungiya Ta Bukaci Tinubu Ya Kori Ministansa, an Jero Dalilai
- Wasu kungiyoyin fararen hula sun bukaci shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da ya sallami daya daga cikin ministocinsa daga aiki
- Kuniyoyin wadanda suka yi zanga-zanga, sun bayyana dalilan da suka sa ya kamata a sallami Olubunmi Tunji-Ojo daga mukaminsa
- Sun bayyana cewa tun da dadewa ya kamata a yi garambawul ga Majalisar ministocin domin cire Olubunmi Tunji-Ojo daga kujerarsa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Wasu 'yan gwagwarmaya sun mika kokon bararsu ga shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu.
'Yan gwagwarmayar karkashin kungiyoyin fararen hula sun bukaci Mai girma Bola Tinubu ya kori Olubunmi Tunji-Ojo daga mukamin Ministan harkokin cikin gida.

Source: Twitter
Kamar yadda tashar Trust Tv ta ruwaito, kungiyoyin sun gudanar da zanga-zanga a ranar Juma'a, 6 ga watan Fabrairun 2026.
Masu zanga-zangar sun bukaci Tunji-Ojo ya yi koyi da tsohuwar Ministar kudi, Kemi Adeosun da tsohon Ministan kimiyya da fasaha, Uche Geoffrey Nnaji, ta hanyar yin murabus.
Kiraye-kirayen Tinubu ya kori Ministan gida
A yayin wannan sabuwar zanga-zanga, mutanen da ke ikirarin zama ’yan ƙungiyoyin farar hula sun ce takardun shaidar karatun Tunji-Ojo ba su inganta ba, kuma a cewarsu bai cancanci ya rike mukamin gwamnati ba.
Sun yi zargin cewa takardar shaidar NYSC da Tunji-Ojo ya gabatar lokacin da aka naɗa shi Minista kuma majalisar dattawa ta tantance shi a ƙarƙashin gwamnatin APC, na ɗauke da kura-kuran bayanai ko kuma ta bogi ce.
Masu zanga-zangar sun ce shirun da ake gani daga gwamnatin Tinubu hujja ce ta yadda take nuna haƙuri da cin hanci da rashawa iri-iri.
Sun kuma bayyana cewa ci gaba da barin Tunji-Ojo a mukaminsa babban nakasu ga kasa ne, ganin cewa Najeriya na da mutane masu yawa masu cancanta, nagarta da gaskiya, musamman a ma’aikatar da ake sa ran za ta jagoranci kirkire-kirkire.
NYSC ta tabbatar da sahihancin takardar
Sai dai kuma, hukumar NYSC ta riga ta tabbatar a shekarar 2023 cewa takardar shaidar NYSC da Tunji-Ojo ya gabatar a gaban majalisar dattawa ingantacciya ce, jaridar Premium Times ta kawo labarin.

Kara karanta wannan
Tun kafin a yi nisa, an sauke gwamna daga matsayin shugaban kwamitin taron APC na kasa
Duk da haka, wani bincike da wata babbar kafar watsa labarai ta gudanar ya nuna wasu tambayoyi kan takardar NYSC ɗin da Tunji-Ojo ya gabatar, wanda ya kasance tsohon ɗan majalisar wakilai ne.

Source: Facebook
Tunji-Ojo ya ce ya yi hidimar NYSC ne daga Nuwamba 2019 zuwa Nuwamba 2020, amma baya duba takardar shaidar, ta nuna cewa an fitar da ita ne a Fabrairu, kuma Janar Birgediya Yushau Ahmed ne ya sanya hannu a kai, alhali kuwa ya zama Darakta Janar na NYSC ne a watan Janairu.
Wannan lamari ya haifar da shakku game da sahihancin takardar, kasancewar NYSC kan fitar da takardar shaidar kammala hidima nan take bayan an gama shirin, kuma ba ta sake fitar da takarda idan ta ɓace ko ta lalace.
Limami ya yi wa Tinubu addu'o'i
A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya halarci bikin daurin auren 'ya'yan karamin Ministan tsaro, Bello Matawalle.
Limamin da ya jagoranci daurin auren ’ya’yan Bello Matawalle, Farfesa Luqman Zakariyah, ya bayyana Shugaba Bola Ahmed Tinubu a matsayin uba ga kowa.
Babban limamin masallacin ya yi addu’a da fatan mulkin Shugaba Bola Tinubu ya zama sanadin dawo da fata ga marasa galihu a cikin al’umma.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
