Gaskiya Komai Dacinta: Sarkin Musulmi Ya Fadi Abubuwa da Ke Ruruta Rashin Tsaro
- Mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammadu Sa'ad Abubakar, ya yi karin haske kan matsalar rashin tsaron da ake fama da ita
- Sarkin Musulmin ya nuna illar da ke tattare da yin watsi da matasa wadanda ke rayuwa a cikin al'umma ba tare da samar musu da abin dogaro da kai ba
- Hakazalika ya bayyana cewa karfafa matasa ta hanya koya musu sana'o'i ba karamin amfani zai yi wa al'umma ba
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Sokoto - Mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammadu Sa’ad Abubakar III, ya yi magana kan matsalar rashin tsaron da ake fama da ita.
Sarkin Musulmin ya yi gargaɗin cewa ci gaba da yin watsi da matasa na iya ƙara yawaitar laifuffuka, shaye-shayen miyagun kwayoyi da matsalar tsaro a faɗin Najeriya.

Source: Facebook
Jaridar Daily Trust ta ce Sarkin Musulmi ya bayyana hakan ne a wajen ƙaddamar da shirin talabijin mai suna The Hustle Reality Show, wanda aka yi wa laƙabi da “Buge-Buge”, wanda ƙungiyar Search for Common Ground ta shirya a Sokoto.
Mai alfarma Sarkin Musulmin ya samu wakilcin Farfesa Sambo Wali Junaidua wajen kaddaamar da shirin.
Sarkin Musulmi ya yi magana kan matasa
Ya jaddada cewa ci gaba da zuba jari wajen ƙarfafa matasa ta hanyar koyon sana’o’i, kasuwanci da tsarin ba da jagoranci, na da matuƙar muhimmanci wajen tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a ƙasa.
Sarkin Musulmin ya bayyana cewa matasan da ba su da aiki kuma suke cikin takaici sun fi saurin faɗawa cikin laifuffuka da sauran munanan ɗabi’u.
A cewarsa, ƙarfafa matasa ba kawai nauyi ne na ɗabi’a ba, illa wata muhimmiyar dabarar saka jari ce ga makomar kasa.
"Ba za mu bari gwiwoyinmu su sare ba. Idan aka yi watsi da matasa, sakamakon hakan yana shafar al’umma baki ɗaya. Amma idan aka shagaltar da su yadda ya dace, suna zama jakadun zaman lafiya, aiki tukuru da cigaban ƙasa.”
- Alhaji Muhammad Sa'ad Abubakar III
Wace shawara Sarkin Musulmi ya ba gwamnati?
Sarkin Musulmin ya kuma yi kira ga masarautu, hukumomin gwamnati da shugabannin al’umma da su ɗauki matakai na gaggawa wajen samar da damammaki da za su bai wa matasa damar zama masu dogaro da kai kuma masu amfani ga al’umma.

Kara karanta wannan
Ta fashe: An cafke malaman Musulunci 2 kan zargin jibgar almajiransu har da makami
“Horon matasanmu domin su iya dogaro da kansu na daga cikin hanyoyin da suka fi tasiri wajen kare makomarsu da kuma karfafa kasa gaba ɗaya."
- Alhaji Muhammad Sa'ad Abubakar III

Source: Facebook
Mataimakin gwamna ya yabawa shirin
A nasa jawabin, mataimakin gwamnan jihar Sokoto, Alhaji Idris Muhammad Gobir, wanda kwamishinan tsare-tsare da kasafin kuɗi, Dr. Abubakar Muhammad Zayyana, ya wakilta, ya bayyana shirin a matsayin wanda ya zo a kan lokaci.
Mataimakin gwamnan na Sokoto ya ce shirin ya yi daidai da tsarin manufofi tara na Gwamna Ahmad Aliyu kan ƙarfafa matasa.
Ya ce shirin na da gagarumar dama wajen inganta tsaro, bunƙasa tattalin arziƙi da rage rashin aikin yi a jihar, yana mai jaddada cewa ƙarfafa matasa na daga cikin muhimman hanyoyin magance matsalar tsaro.
Sarkin Musulmi ya mika bukata wajen Tinubu
A wani labarin kuma, kun ji cewa Mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammadu Sa'ad Abubakar III, ya bukaci Shugaba Bola Tinubu ya ziyarci Kasuwar Daji da ke jihar Neja.
Ya ce ziyarar za ta taimaka wajen kwantar da hankalin jama’a da kuma hana yiwuwar daukar fansa bayan kisan mutanen da ba su ji ba, ba su gani ba.
An yi kiran ne dai bayan da 'yan bindiga dauke da makamai suka je kasuwar, suka hallaka mutanen da ba su san hawa ba, ba su san sauka ba.
Asali: Legit.ng
