Tashin Hankali: Ƴan Bindiga Sun Kai Sabon Hari Benue, Sun Kashe fiye da Mutum 10
- Wasu 'yan bindiga da ake zargin makiyaya ne sun kashe mutane 13 tare da sace mata a harin da suka kai kasuwar Anwase dake jihar Benue
- Wannan hari yana zuwa ne kwanaki biyu bayan an kashe wasu mutane 16 a yankin Abande dake karamar hukumar Kwande, a jihar
- Jami’an tsaro sun isa yankin domin tabbatar da zaman lafiya yayin da daruruwan mutane ke tserewa daga gidajensu saboda tsoron hare haren
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Benue - Wasu mahara da ake zargin makiyaya ne sun kashe aƙalla mutane 13 a wani sabon hari da suka kai kasuwar Anwase dake Jihar Benue.
Maharan sun afka wa kasuwar ne dake gundumar Mbaikyor a ƙaramar hukumar Kwande, inda suka yi garkuwa da mata masu yawa tare da ƙona rumfuna.

Source: Getty Images
'Yan bindiga sun kai sabon hari Benue
Ibi Andrew, mataimakin shugaban ƙaramar hukumar Kwande, ya tabbatar wa kafar watsa labarai ta Channels TV cewa an kashe mutane 13.
Ya ƙara da cewa shugaban ƙaramar hukumar tare da jami'an tsaro sun riga sun isa yankin domin dawo da doka da kuma hana ƙarin hare-hare.
Wani shaidan gani da ido ya bayyana cewa maharan sun fito ne daga wani dutse dake kusa, inda suka bude wuta kan mai uwa da wabi.
Wannan harbi ya jefa jama'a cikin rudani, wanda hakan ya ba maharan damar sace mata tare da tserewa da su zuwa cikin tsaunuka.
Duk da wannan ta'addanci, rundunar ƴan sandan Jihar Benue ba ta fitar da sanarwa ba tukuna domin tabbatar da ainihin abin da ya faru.
Hare-haren 'yan bindiga a kauyukan Benue
Kakakin rundunar, Udeme Edet, ba ta amsa saƙonnin wayar salula da aka tura mata ba domin jin ƙarin bayani kan matakan da aka ɗauka.
Wannan ta'addancin yana zuwa ne kwanaki biyu kacal bayan da wasu mahara suka kashe mutane 16 a yankin Abande dake Kwande.
A harin Abande, wanda ya faru ranar Talata, maharan sun buɗe wa mutane wuta a kasuwa, sannan suka kwashe miliyoyin nairori na ƴan kasuwa.
Lawrence Akerigba, tsohon kansila a yankin, ya bayyana cewa maharan sun kashe har da wani kwamandan jami'an ƴan sanda masu kwantar da tarzoma (MOPOL).

Source: Original
Mutane sun fara tserewa daga gidajensu
Wadannan hare-hare sun tilasta wa dubban mazauna yankunan Turan da sauran maƙwabta guduwa daga gidajensu domin neman tsira daga takobin ƴan bindigar.
Akerigba ya koka da cewa har yanzu ana neman wasu mutanen da suka ɓace, yayin da jami'an tsaro ke kwashe gawarwaki zuwa Jato-Aka.
Mazauna yankin sun bayyana cewa tsaro yana ƙara taɓarbarwa, domin ba su da wani wurin neman mafaka ko tabbacin samun kariya.
A halin yanzu, al'ummar yankin Kwande suna cikin zullumi yayin da suke kira ga gwamnatin tarayya da ta ɗauki matakin gaggawa kafin komai ya lalace.
'Yan bindiga sun kashe mutane 10 a Kwara
A wani labari, mun ruwaito cewa, 'yan bindiga sun kaddamar da mummunan hari a garuruwan Woro da Nuku dake ƙaramar hukumar Kaiama a jihar Kwara.
A yammacin ranar Talata, 3 ga Fabrairu, 2025 ne aka ce maharan suka farmaki garuruwan, inda suka kashe aƙalla mutane 10 tare da jikkata wasu da dama.
Baya ga kisan kai, maharan sun kona gidaje da dama, lamarin da ya sa mutane da yawa rasa matsugunansu, kamar yadda rahoton ya nuna.
Asali: Legit.ng


