Hotuna: Shugaba Tinubu Ya Sanya Labule da Gwamna Uba Sani a Aso Rock Villa
- Shugaba Bola Tinubu ya gana da Gwamna Uba Sani a fadar Aso Rock bayan sun halarci daurin auren 'ya'yan ministan tsaro, Bello Matawalle
- Ganawar tasu ta zo ne awanni bayan wasu masu ibada da aka sace a Kaduna sun shaki iskar 'yanci daga hannun azzaluman yan bindiga
- Har yanzu fadar shugaban kasa ba ta fitar da takamaiman bayani kan makasudin tattaunawar sirrin da shugabannin biyu suka yi a yammacin yau ba
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya karɓi bakuncin gwamnan jihar Kaduna, Mai Girma Uba Sani, a wata ziyara ta musamman da ya kai masa a fadar Aso Rock Villa, Abuja.
Shugaba Tinubu ya sanya labule da Gwamna Uba Sani ne jim kaɗan bayan sun halarci sallar Juma'a a babban Masallacin Ƙasa dake Abuja.

Kara karanta wannan
Bayan Abba ya shiga APC, Shugaba Tinubu zai yi aikin titin Naira biliyan 19 a Kano

Source: Twitter
Tinubu a daurin auren 'ya'yan Matawalle
Mai magana da shugaban kasa, Bayo Onanuga ne ya sanar da ganawar shugabannin biyu a cikin wata sanarwa da ya fitar a shafinsa na X a yammacin Juma'a, 6 ga Fabrairu, 2026.
A masallacin Juma'a, Tinubu, Uba Sani sun halarci ɗaurin auren ƴaƴan Karamin Ministan tsaro, Bello Matawalle, guda tara, wanda ya tara jiga-jigan ƴan siyasar ƙasar nan.
Bayan Shugaba Tinubu da Uba Sani, taron daurin auren ya sami halartar mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau Jibrin, da kuma ministan tsaro, Janar Christopher Musa.
Legit Hausa ta rahoto cewa wasu gwamnoni da suka halarta sun haɗa da Abba Kabir Yusuf na Kano, Babagana Zulum na Borno, da kuma Ahmed Aliyu na Sakkwato.
Tinubu ya sanya labule da Uba Sani
Bayan kammala wannan taro na aurar da ƴaƴa tara ne, Shugaba Tinubu da Gwamna Uba Sani suka nufi fadar Aso Rock Villa domin gudanar da tasu tattaunawar.

Kara karanta wannan
Limami ya kalli Bola Tinubu, ya yi masa wasu addu'o'i a gaban manyan kasa a Abuja'
Wannan ganawar tasu tana zuwa ne awanni bayan da wasu masu ibada da aka sace a Kaduna suka shaki iskar ƴanci daga hannun ƴan bindiga.
An sako mutanen ne bayan kwashe kwanaki a hannun maharan, lamarin da ya janyo farin ciki da kuma godiya ga Allah a tsakanin al'ummar jihar Kaduna.
Duk da cewa wannan nasara ta samu, har yanzu akwai ƙalubalen tsaro dake buƙatar haɗin gwiwa mai ƙarfi tsakanin gwamnatin tarayya da kuma gwamnatin Kaduna.

Source: Twitter
Me Tinubu da Uba Sani suka tattauna?
Masu lura da al'amura suna ganin cewa sako waɗannan mutane na iya kasancewa ɗaya daga cikin abubuwan da suka sanya wannan ganawar ta zama mai mahimmanci.
Har zuwa wannan lokaci, fadar shugaban ƙasa ko gwamnatin Kaduna ba su fitar da takamaiman bayani kan abubuwan da shugabannin biyu suka tattauna ba.
Masana siyasa na ganin cewa ganawar ba za ta rasa alaƙa da yanayin tsaron jihar da kuma wasu tsare-tsaren ci gaba da Shugaba Tinubu ke shirin aiwatarwa ba.
Imran Muhammad, mai tallafawa shugaban jam'iyyar APC na kasa a kafofin sada zumunta ya wallafa a shafinsa na X cewa:
"Tattaunar ta shafi batun tsaro a jihar Kaduna, inda Gwamna Uba Sani ya yi wa shugaban kasa bayani kan yadda aka ceto masu ibada da aka sace a ranar 18 ga Janairu, 2026 a majami'un da ke garin Kurmin Wali, karamar hukumar Kajuru.
"Gwamnan ya kuma bada bayani kan ayyukan hadin gwiwa da ake yi tsakanin hukumomin tsaron jiha da na tarayya da suka taimaka aka kubutar da masu ibadar."
Kalli hotunan ganawar a nan kasa:
'Za a zabi Tinubu a Kaduna a 2027'
A wani labari, mun ruwaito cewa, Gwamna Uba Sani ya sanar da goyon bayan Kaduna ga tazarcen Shugaba Bola Tinubu a 2027 saboda wasu dalilai da ya lissafo.
Gwamnan jihar na Kaduna ya ce Tinubu ya yi wa Kaduna duk wani gata da ake bukata, ciki har da gina layin dogo na zamani da ya lakume biliyoyin Naira.
A cewar Uba Sani, jam'iyyar APC mai mulki a jihar da kasa za ta samu akalla mabiya miliyan uku a yayin da take rajistar mambobi a intanet, gabanin zaben 2027.
Asali: Legit.ng
