'Yan Bindiga Sun Kutsa Har Gida, Sun Sace Babban Limami a Kaduna

'Yan Bindiga Sun Kutsa Har Gida, Sun Sace Babban Limami a Kaduna

  • 'Yan bindiga dauke da makamai sun kai hari a wani kauye na jihar Kaduna da ke yankin Arewa maso Yammacin Najeriya
  • Tsagerun 'yan bindiga sun shiga har cikin gida sun yi awon gaba da babban limamin masallacin Juma'a tare da wasu mutane daban
  • Mutanen yankin sun koka da cewa duk da yawan hare-haren da ake kawo musu, jami'an tsaro sun ki waiwayarsu don kawo musu dauki

​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Kaduna - ’Yan bindiga dauke da makamai sun yi garkuwa da wani babban limamin masallacin Juma’a a jihar Kaduna.

'Yan bindigan sun sace babban limamin masallacin Juma'ar ne na kauyen Janjala, Malam Bello Abdullahi, da ke karamar hukumar Kagarko ta jihar Kaduna.

'Yan bindiga sun sace mutane a Kaduna
Gwamnan jihar Kaduna, Sanata Uba Sani Hoto: @ubasanius
Source: Facebook

Jaridar Aminiya ta kawo rahoton cewa 'yan bindigan sun sace Malam Bello Abdullahi ne tare da wani jagoran Fulani a yankin, Alhaji Shehu Bello da kuma wata mata.

Kara karanta wannan

Masu ibada da aka sace a Kaduna, sun fadi yadda rayuwa ta kasance a hannun 'yan bindiga

'Yan bindiga sun addabi kauyuka da hare-hare

'Yan bindiga sun kai hare-hare wasu kauyuka da dama a yankin da suka hada da Gidan-Makeri, Iddo, Kohoto da Janjala a cikin 'yan kwanakin nan, inda suka yi garkuwa da mutane tare da yin awon gaba da shanu.

Hare-haren na 'yan bindiga kan mazauna kauyen Kohoto, da ke makwabtaka da Janjala, sun tsere daga matsugunansu a ranar Asabar.

An sace babban limami a Kaduna

Wani shugaban al’umma da ke yankin ya tabbatar da aukuwar harin na 'yan bindiga a ranar Laraba, 4 ga watan Fabrairun 2026.

Ya bayyana cewa ’yan bindigan sun sake kai hari a daren Talata, 3 ga watan Fabrairun 2026 da misalin karfe 9:00 na dare.

Shugaban al'ummar ya ce 'yan bindigan sun yi garkuwa da babban limami da jagoran Fulani tare da wata mata a yayin harin da suka kawo.

Wata majiya ta bayyana cewa ’yan bindigan, sun je kauyen ne cikin adadi mai yawa dauke da bindigogi kirar AK-47.

Kara karanta wannan

Sarki ya fasa ƙwai, ya faɗi kuskuren sojoji, DSS da ya jawo kisan mutum 75 a Kwara

Majiyar ta kara da cewa 'yan bindigar sun fara kutsawa gidan babban limamin kafin su wuce gidan jagoran na Fulani.

Harin ya jefa al’ummar yankin cikin firgici, inda mazauna da dama suka tsere daga matsugunansu.

Mutane na bukatar dauki

Jagoran al’ummar ya nuna takaicinsa kan yawaitar hare-hare a yankin, inda ya bayyana cewa ya sha mika kokon bararsa ga jami'an tsaro, amma ba a kawo musu dauki ba.

'Yan bindiga sun sace babban limami a Kaduna
Taswirar jihar Kaduna, tarayyar Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Ya bayyana cewa mutanen yankin na cikin barazana kuma jami'an tsaro ba su yi komai a kai ba duk kuwa da cewa kokarin tuntubar wadanda ake da su a Kagarko.

Hakazalika, Wata majiya da ta nemi a sakaya sunanta daga masarautar Kagarko, ta tabbatar da aukuwar hare-haren.

Ta ce fadar masarauta ta riga ta kai rahoton lamarin ga hukumar karamar hukumar Kagarko, tare da nuna rashin daukar matakin tsaro.

'Yan bindiga sun kashe mutane

A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu mugayen 'yan bindiga dauke da makamai sun kai harin ta'addanci a jihar Katsina.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kashe mutane 10, sun kona gidaje a sabon harin da suka kai Kwara

Tsagerun 'yan bindigan sun kai harin ne a wanda ya yi sanadiyyar kashe mutane masu yawa, lalata gidaje da shaguna da motoci a karamar hukumar Faskari.

Mummunan harin da yan bindigan suka kai a kauyen Doma na yankin Tafoki ya raba mutane da yawa da muhallansu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng