Trump Ya Jawo Magana bayan Wallafa Obama da Matarsa a Siffar Birrai
- Shugaban Amurka Donald Trump ya wallafa bidiyo da ke nuna Barack Obama da matarsa Michelle a matsayin birai
- Bidiyon ya sake tayar da ce-ce-ku-ce kan zaɓen shugaban ƙasa na 2020 da Trump ya sha kaye a hannun Joe Biden
- Jama’a da manyan ’yan siyasa sun soki bidiyon, suna zargin Trump da nuna wariyar launin fata da nuna bakin fata a matsayin biri
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
United States of America – Shugaban ƙasar Amurka, Donald Trump, ya jawo hankalin duniya bayan wallafa wani bidiyo a kan tsohon Shugaba Barrack Obama da matarsa.
Shugaba Donald Trump ya wallafa Obama da matarsa Michelle matsayin birrai da aka kirkira ta hanyar fasahar AI.

Source: Facebook
Bidiyon da Obama ya wallafa a shafinsa na Truth Social ya tayar da kura mai yawa, inda aka rika bayyana shi a matsayin abin kyama da rashin mutunci.
Donald Trump ya sake jawo magana
Trump ya wallafa bidiyon ne da asubahin ranar Juma’a, 6 ga watan Fabrairu, 2026 tare da wasu wallafe-wallafe guda biyu da ke zargin maguɗi a zaɓen shugaban ƙasa na 2020.
A wancan zabe, Joe Biden ne ya yi nasara, kuma kafin ya zama Shugaban kasa ya taba aiki tare da Barack Obama a shekarar 2009.
A cikin bidiyon, wani masani kan tsaro ta intanet mai suna Phil Waldron ya yi ikirarin cewa an gano wasu “makirci” a lokacin ƙirga ƙuri’u a zaɓen 2020.

Source: Getty Images
Ya ce jihohi biyar masu muhimmanci sun dakatar da ƙirga ƙuri’u a lokaci guda, lamarin da ya haifar da shakku a zukatan masu kallon bidiyon.
Waldron ya kuma yi zargin cewa an yi amfani da na’urorin ƙirga ƙuri’u masu dauke da manhajojin tafka maguɗi.
Ana zargin magudi a zaben su Trump
Ya ce bayan da aka ci gaba da ƙirga ƙuri’un, sai aka samu gagarumin ƙaruwa da ya karkata sakamakon zuwa ga Joe Biden.
A cewarsa:
“Lokacin da aka koma rahoto da ƙirga ƙuri’u, sai aka samu ƙarin ƙuri’u da ya fi karkata ga Joe Biden.”
Rahotanni sun nuna cewa Trump ya wallafa bidiyon sau biyu a shafinsa, abin da ya kara hura wutar muhawara a kafafen sada zumunta.
A karshen bidiyon ne aka nuna Barack Obama da Michelle Obama a matsayin birai da ke rawa cikin nishadi, suna rawa da wakar “The Lion Sleeps Tonight,” wata shahararriyar waka daga fim ɗin Disney na The Lion King.
Ofishin yada labaran gwamnan jihar California, Gavin Newsom, ya fitar da sanarwa yana sukar bidiyon.
Sanarwar ta ce:
"Mummunan hali daga Shugaban ƙasa. Dole ne kowanne dan jam’iyyar Republican ya yi Allah wadai da wannan.”
Trump ya girmama matar Tinubu
A baya, kun ji cewa uwargidan Shugaban Najeriya, Sanata Oluremi Tinubu, ta gana da Shugaban Amurka Donald Trump yayin taron addu'a karo na 74 a Amurka da aka gudanar a Capitol.
A yayin taron, an gayyaci Remi Tinubu ta hau dandalin taron tare da Trump, lamarin da ya ja hankalin mahalarta daga kasashe daban-daban, inda ya jinjina mata.
Tump ya yi amfani da damar wajen yabawa uwargidan shugaban Najeriyar, yana mai bayyana ta a matsayin mace mai daraja da ake girmama wa, kuma babbar fasto.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


