Magana Ta Kare: Malaman Musulunci Sun Fadi Ranar Fara Azumin Watan Ramadan
- Ƙungiyar Limamai da shugabannin Musulunci a yankin Yarabawa ta sanar da ranar da za a fara gudanar da azumin watan Ramadan
- Malaman sun ce an ɗauki ranar ne bisa ƙididdigar taurari da ƙudurin tarukan Musulunci na duniya baki daya wanda ya dace
- Ramadan zai cika kwanaki 30, yayin da za a ake tsammanin ga jinjirin Shawwal ranar 19 ga Maris, 2026
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Ibadan, Oyo - Yayin da al'ummar Musulmi ke dakon fara azumin watan Ramadan, shugabannin addinin sun fara ankarar da mutane.
Shugabannin addinin Musulunci karkashin Ƙungiyar Limamai a yankin Yarabawa sun sanar da ranar fara azumin watan Ramadan na shekarar 2026.

Source: Facebook
Yaushe za a fara 'azumin' Ramadan?
Babban Muftin Yarabawa, Sheikh AbdulRasaq AbdulAzeez Ishola, shi ne ya karanta sanarwar ga manema labarai bayan kammala taron, cewar The Nation.

Kara karanta wannan
Ta fashe: An cafke malaman Musulunci 2 kan zargin jibgar almajiransu har da makami
Sun bayyana cewa azumin zai fara ne a ranar Laraba, 18 ga watan Fabrairu, 2026, bayan taro da suka gudanar a birnin Ibadan, jihar Oyo.
Taron ya samu halartar manyan shugabannin Musulunci da suka hada da Shugaban Ƙungiyar Limamai, Babban Limamin Ibadan, da kuma manyan limamai daga jihohin Ogun, Osun, Ondo da sauran jihohin Kudu maso Yammacin Najeriya.
A cikin sanarwar da aka fitar bayan taron, ƙungiyar ta ce an zaɓi ranar fara azumin ne bisa ƙididdigar ilimin taurari da kuma ƙudurin kalandar Musulunci da aka amince da su a duniya.
Ƙungiyar ta bayyana cewa haduwar wata da rana na watan Ramadan zai faru ne a ranar Talata, 17 ga Fabrairu, 2026, da misalin ƙarfe 1:01 na rana agogon Najeriya.
Hakan, a cewar ƙungiyar, ya tabbatar da cewa azumi ya dace a fara shi washegari, wato ranar Laraba, 18 ga Fabrairun 2026.

Source: Original
Kwanaki nawa ake sa ran za a yi azumi?
Sun kara da cewa wannan matsaya ta biyo bayan shawarwarin tarukan Musulunci na kasa da kasa da aka gudanar a biranen Istanbul, Paris da sauran wurare, inda malamai da masana ilimin taurari suka amince da amfani da sahihiyar ƙididdiga wajen tantance watannin Musulunci.
Ƙungiyar ta kuma sanar da cewa azumin Ramadan na wannan shekara zai cika kwanaki 30, kamar yadda PM News ta ruwaito.
Sun bayyana cewa ba za a iya ganin jinjirin watan Shawwal a ranar 18 ga Maris, 2026 ba, wanda ke nuna cewa ba za a kammala azumi bayan kwanaki 29 ba.
A cewarsu, jinjirin watan Shawwal, wanda ke nuna ƙarshen Ramadan, zai bayyana ne a ranar Alhamis, 19 ga Maris, 2026.
Saboda haka, Musulmi za su kammala azumi na kwanaki 30, kuma ba za a yi Sallar Idi da wuri ba.
A ƙarshe, ƙungiyar ta yi kira ga Musulmi da su shirya azumin Ramadan ta fuskar addini, tare da gudanar da ibada cikin zaman lafiya, haɗin kai da fahimtar juna.
An fara hasashen ranar fara azumin Ramadan
Mun kawo muku cewa ana sa ran al'ummar Musulmi za su fara azumin Ramadan na shekarar 2026 ne a ranar 19 ga watan Fabrairun 2026.
Har ila yau, sa'o'in da Musulmi za su dauki azumi zuwa shan ruwa za su kasance matsakaita tsakanin awa 12 zuwa 13 a mafi yawan kasashen duniya.
Yanayin kaka da sanyi zai taimaka wa Musulmi gudanar da ibada cikin sauki ba tare da fuskantar tsananin kishirwa ko wahalar zafi ba.
Asali: Legit.ng
