Ana Binciken Ministan Tinubu da Ya Yi Murabus bayan Zargin Aiki da Takardun Bogi
- Hukumar ICPC ta fara bincike kan zargin aiki da takardun karatu da na NYSC na bogi da ake dangantawa da tsohon ministan kimiyya da fasaha, Uche Nnaji
- Rahotanni sun nuna cewa ICPC ta rubuta wasika zuwa ofishin sakataren gwamnatin tarayya da majalisar dattawa domin neman takardun da Nnaji ya gabatar
- Masu sharhi na cewa tsohon ministan na iya fuskantar hukunci a gaban kotu idan binciken ya tabbatar da cewa ya aikata laifin da ake tuhumarsa da shi
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Abuja – Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Kasa, ICPC, ta fara wani sabon bincike kan tsohon Ministan Kimiyya da Fasaha, Uche Nnaji, bisa zargin aiki da takarun shaidar karatu da na NYSC na bogi.
Rahoton ya ce bayan kwana uku kacal da wallafa binciken, Uche Nnaji ya ajiye mukaminsa na minista, lamarin da ya jawo muhawara daga ‘yan Najeriya da dama da ke ganin murabus din bai wadatar ba.

Source: Twitter
Binciken da ake ya biyo bayan wani rahoto da kafar yada labarai ta Premium Times ta wallafa a watan Oktoban 2025 da ya ce Nnaji ya yi amfani da takardun bogi.
An fara binciken ministan Tinubu
Majiyoyi masu tushe sun shaida cewa ICPC ta rubuta wasika zuwa ga Sakataren Gwamnatin Tarayya, George Akume, inda ta bukaci a mika mata dukkan takardun da Uche Nnaji ya gabatar lokacin nadinsa a matsayin minista.
Haka kuma, an bayyana cewa hukumar ta tuntubi Majalisar Dattawan Najeriya domin neman irin wadannan takardu, matakin da ke nuna cewa binciken ya shiga wani sabon mataki mai zurfi.
Masu sharhi kan harkokin shari’a na ganin wannan mataki na ICPC na iya kaiwa ga gurfanar da tsohon ministan a gaban kotu, musamman idan aka tabbatar da sahihancin zargin da ake masa.
Ana kira a gurfanar da Uche Nnaji
Tun bayan fitowar binciken, ‘yan Najeriya da dama sun bukaci a gurfanar da Uche Nnaji, suna cewa bai dace a ce ya yi murabus kawai ba idan aka yi la’akari da dokokin kasar da ake zargin ya karya.
Wasu kungiyoyin farar hula sun jaddada cewa barin lamarin a matakin murabus zai iya sa sauran jami’an gwamnati aikata laifin, tare da raunana yaki da cin hanci da rashawa a kasa.

Source: Twitter
A cewarsu, bin diddigin doka da oda kan irin wannan zargi yana da muhimmanci wajen tabbatar da gaskiya da rikon amana a tsarin mulki.
Hukumar ICPC ta yi shiru
Duk da haka, ICPC ba ta fitar da sanarwa a hukumance ba dangane da binciken. Lokacin da aka tuntubi kakakin hukumar, John Odey, ya ce ba zai iya magana kan batun ba kasancewar yana hutu.
Odey ya bayyana cewa sai bayan dawowarsa ofis a mako mai zuwa zai iya tabbatar da sahihancin rahotannin da ke yawo, yana mai rokon a sake tuntubarsa nan gaba.
Nnaji ya yi murabus daga minista
A wani labarin, kun ji cewa Ministan kimiyya da fasaha na kasa, Uche Nnaji ya tabbatar da cewa ya yi murabus a wata takarda da ya fitar.
Fadar shugaban kasa ta bayyana cewa shugaba Bola Ahmed Tinubu ya karbi takardar murabus din kuma yana masa fatan alheri.
Uche Nnaji ya yi murabus ne a daidai lokacin da ake kira ga shugaba Tinubu ya sallame shi a bakin aiki kan zargin aiki da takardun bogi.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

