Tinubu Ya Fadada Shirin Tallafawa Mata zuwa Mutum Miliyan 25

Tinubu Ya Fadada Shirin Tallafawa Mata zuwa Mutum Miliyan 25

  • Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya sanar da fadada shirin Nigeria for Women Programme domin ya shafi mata miliyan 25 a fadin kasar nan
  • Rahoto ya ce an kaddamar da wani dandali na zamani da zai hada mata da hanyoyin samun kudi, kwarewa, kasuwanci da tallafin gwamnati
  • Gwamnatin tarayya da jihohi sun jaddada hadin gwiwa wajen tabbatar da nasarar shirin da kuma karfafa rawar da mata ke takawa a kasa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana aniyar gwamnatinsa ta kara bai wa mata muhimmanci ta hanyar fadada shirin bunkasa tattalin arzikin mata zuwa mutane miliyan 25 a fadin Najeriya.

Shugaban ya sanar da hakan ne yayin kaddamar da wani dandali na zamani da aka kirkira domin saukaka wa mata damar samun tallafi a fannoni daban-daban.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya kausasa harshe kan harin 'yan ta'adda a Kwara, ya dauki mataki

Kashim Shettima yayin kaddamar da shirin tallafawa mata
Yadda aka kaddamar da shirin tallafawa mata miliyan 25. Hoto: Kashim Shettima
Source: Facebook

A sakon da mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya wallaffa a X, ya bayyana cewa ya wakilci shugaba Tinubu wajen kaddamar da shirin.

An fadada shirin tallafin matan Najeriya

Shugaba Tinubu ya bayyana cewa shirin wani muhimmin ginshiki ne na manufofin gwamnatinsa na hada kan jama’a da bunkasa tattalin arziki.

Shugaba kasar ya ce Najeriya ba za ta iya cimma ci gaba mai dorewa ba matukar ba a sanya mata a cikin tsare-tsaren kasa baki daya ba.

A cewarsa, bai dace a ci gaba da nuna rashin kulawa ga rawar mata ke takawa a Najeriya ba, domin su na taka muhimmiyar rawa wajen gina kasa.

Jawabin Tinubu kan shirin mata

A cikin wata sanarwa da Mataimakin Shugaban Kasa ya fitar ta bakin hadiminsa, Stanley Nkwocha, Shugaba Tinubu ya jaddada cewa duk kasa da ke wulakanta mata na jefa kanta cikin hatsari.

Ya ce gwamnatinsa ta fahimci wannan gaskiya tun tuni, shi ya sa ta bai wa mata manyan mukamai tare da daura musu alhakin jagorantar muhimman al’amura.

Kara karanta wannan

Fadar shugaban kasa ta jero wadanda suka jefa mutane a kangin talauci a Najeriya

Nkwocha ya wallafa a X cewa shugaban ya kara da cewa kaddamar da shirin a matakin kasa shaida ce ta kudurin gwamnati na ganin an cika alkawarin da aka dauka ga mata.

Sabon dandali na zamani ga mata

Bayan gwajin shirin a jihohi shida, wanda ya amfanar da fiye da mata miliyan daya, gwamnatin tarayya ta yanke shawarar fadada shirin zuwa fadin Najeriya.

A karkashin fadada shirin, an bullo da manhajar Happy Woman App Platform, wadda aka ce tsari ne mai tsaro da zai hada mata da damammakin samun kudi, koyon sana’o’i, shiga kasuwanni, kariya da tallafin jin kai.

Mahalarta kaddamar da shirin tallafin mata a Abuja.
Mata da suka halarci shirin tallafa musu a Abuja. Hoto: Kashim Shettima
Source: Facebook

Shugaban ya bayyana cewa shigar da jama’a cikin harkokin zamani ya zama wajibi, musamman domin inganta ayyukan gwamnati da karfafa gogayya a matakin kasa da kasa.

A bangaren jihohi kuma, Mataimakin gwamnan Jihar Katsina ya tabbatar da kudurin gwamnatocin jihohi na bayar da gudunmawar kudi domin nasarar shirin.

Najeriya ta kawo shiri ga matasa

A wani rahoton, kun ji cewa Gwamnatin tarayya ta kawo shiri na musamman domin habaka tattalin arzikin matasa akalla miliyan 10.

Kara karanta wannan

Tinubu ya tura bataliyar sojoji Kwara bayan kashe Musulmai sama da 100

Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ne ya kaddamar da shirin a fadar shugaban kasa, inda ya ce zai habaka tattalin arzikin kasa.

A bayanin da ya yi, Kashim Shettima ya sanar da cewa mata da matasa za su fi cin gajiyar sana'o'in da za a koyar a karkashin shirin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng