Ta Fashe: An Cafke Malaman Musulunci 2 kan Zargin Jibgar Almajiransu har da Makami

Ta Fashe: An Cafke Malaman Musulunci 2 kan Zargin Jibgar Almajiransu har da Makami

  • Hukumar NSCDC ta kama malaman addinin Musulunci guda biyu bisa zargin cin zarafin wasu daga cikin almajiransu
  • Rahoto ya nuna cewa malaman sun yi amfani da adda mai zafi wajen dukan yaran, lamarin da ya jikkata bayansu da duwawunsu sosai
  • Hukumar ta ce laifin ya saba da dokar kare haƙƙin yara, kuma wadanda ake zargi sun amsa laifi, za a gurfanar da su a kotu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abeokuta, Ondo - Hukumar tsaro ta NSCDC ta ce jami’anta sun kama malaman addinin Musulunci biyu a jihar Ondo.

An cafke malaman a garin Owo a jihar Ondo, bisa zargin gallaza wa yara ƙanana biyu da ke hannunsu da nufin karatu.

An kama malaman Musulunci 2 a Ondo
Wasu malaman Musulunci, Adebodun Muideen, Oladejo Musiliu. Hoto: NSCDC Ondo State Command.
Source: Facebook

Hakan na cikin wata sanarwa da ya fitar, jami’in hulɗa da jama’a na NSCDC a jihar Ondo, Daniel Aidamenbor ya fitar wanda TheCable ta samu.

Kara karanta wannan

Bayan mummunan hari a Kwara, Tinubu ya sanya labule da Gwamnan jihat a Abuja

Sunayen malaman Musuluncin da aka cafke

Aidamenbor ya bayyana sunayen wadanda aka kama a matsayin Adebodun Muideen na makarantar 'Al-Balaagul-Mubeen Arabic and Islamic Centre', da kuma Oladejo Musiliu daga 'Abdullah Arabic and Islamic Centre'.

Aidamenbor ya ce an kama mutanen ne bayan wani rahoto da kungiyar kare haƙƙin yara, ta kai wa hukumomin tsaro game da abin da ya faru.

Ya ce an gano lamarin ne a ranar Laraba, lokacin da wani malamin aji ya lura da raunuka da dama a jikin yaran, inda nan take ya sanar da kungiyar kare haƙƙin yara.

Binciken farko ya nuna cewa an turo yaran, wadanda iyayensu ke zaune a jihar Osun ne domin koyon karatun Alƙur’ani tare da ilimin boko.

Sanarwar ta kara da cewa matsalar ta fara ne lokacin da daya daga cikin yaran ya dawo gida dauke da wayar Vivo, amma ya kasa bayyana yadda ya samu wayar.

Ana zargin malamana Musulunci da duka dalibansu
Taswirar jihar Ondo da aka cafke malaman Musulunci 2. Hoto: Legit.
Source: Original

Malaman sun amsa laifuffukansu

Kakakin hukumar NSCDC ya ce yayin tambayoyi, an ambaci sunan ɗan uwansa na biyu, lamarin da ya sa malamai suka yi amfani da adda suka yi wa yaran duka a bayansu da duwawunsu, wanda hakan ya haddasa mummunan rauni.

Kara karanta wannan

Kwankwaso ya girgiza kan harin 'yan ta'adda a Kwara, ya ba gwamnati mafita

Sanarwar ta ce:

“Wannan abin da suka yi ya sabawa dokar kare haƙƙin yara ta ƙasa da kuma dokar kare yara ta jihar Ondo.”

Aidamenbor ya kara da cewa wadanda ake zargin sun amsa laifinsu, kuma za a gurfanar da su a gaban kotu bisa laifin duka da cin zarafin yara, cewar Tribune.

Ya gargadi makarantu na addini, iyaye da masu kula da yara da su guji hukunta yara ta hanyoyin da ba bisa ka’ida ba, yana mai jaddada cewa:

"Duk wani nau’in tashin hankali ga yara, ko da da wace hujja aka yi shi, laifi ne a karkashin dokar Najeriya.”

An kama malamin Musulunci a Oyo

Kun ji cewa 'yan sanda sun cafke wani malamin addinin Musulunci dauke da wani abu da ake zargin naman jikin dan Adam ne a jihar Oyo.

Kakakin rundunar yan sandan jihar Oyo, Adewale Osifeso ya ce malamin ya shaida masu cewa a jihar Lagos ya sayi naman.

Bugu da kari, yan sandan Oyo sun kwato wata mota a wurin binciken ababen hawa bayan direba ya fita ya gudu.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.