Gwamna Ya Kunyata Matarsa a bainar Jama’a bayan Ta Yi Kokarin Kin Sumbatarsa
- Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, ya jawo ce-ce-ku-ce bayan ya kauce wa sumbatar da matarsa ta yi masa a wani taro
- Bidiyon ya kara rura wutar muhawara, musamman a lokacin da ake fama da rikicinsu na siyasa da Ministan Abuja, Nyesom Wike
- ‘Yan Najeriya sun samu mabambantan ra’ayoyi kan lamarin, wasu suna ganin bai dace a nuna soyayya a bainar jama’a ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Ibadan, Jihar Oyo – Gwamnan Jihar Oyo, Seyi Makinde, ya jawo hankalin ‘yan Najeriya bayan wani bidiyo ya kunyata matarsa a taro.
Bidiyon ya nuna yadda ya kauce wa sumbatar da matarsa, Tamunominini Makinde ta yi masa a wani taron jama’a da aka yi

Source: Twitter
Bidiyon da tayar da maganganu
An gano ta a bidiyon da shafin Yabaleftonline ya wallafa a X tana kokarin sumbatar mijinta amma gwamnan ya kauce har sau biyu, lamarin da ya jawo muhawara a tsakanin jama’a.
Bidiyon ya bazu a kafofin sadarwa inda mutane suka tofa albarkacin bakinsu game da abin da ya faru.
Taron ya samu halartar manyan mutane a kasa ciki har da tsofaffin gwamnoni da masu rike da mukamai a gwamnati.
Martanin 'yan Najeriya game da bidiyon
Lamarin kin sumbatar da matarsa a bainar jama’a ya kara dagula ce-ce-ku-cen da ke kewaye da gwamna Makinde, inda ‘yan Najeriya suka rika bayyana ra’ayoyinsu daban-daban.
Adedotun Kehinde:
"Ba kowa ne yake da sha'war irin haka a bainar jama'a ba, hakan bai dace da kowa ba."
ZephyrKing ya ce:
"Abin dariya, me yasa wani dan karamin faifan bidiyo zai tayar da kura har haka, amma maganar gaskiya ko a bainar jama'a, bai kamata mutum ya kunyata masoyinsa ba irin haka, ina fatan suna zaman lafiya"
Zoey ya ce:
"Mutane suna da daukar zafi kan bidiyo na dakika biyar, Makinde gwamna ne ba wani dan wasan kwaikwayon Nollywood ba, yana wurin aikinsa na Gwamna mai baki fiye da 1,600.
"A taron akwai tsofaffin gwamnoni 17, kuma yana bakin aiki ne a hukumance wasu ba su aminta da nuna kauna a cikin jama'a ba musamman a irin wannan taro, don Allah a bar shi ya huta."

Kara karanta wannan
Masana'antar fina finai ta girgiza, ƴar wasar fim ta bar duniya bayan fama da jinya
Wani ya kare gwamnan, yana cewa ba kowa ne ke son nuna soyayya a bainar jama’a ba, musamman idan akwai yara da kuma la’akari da matsayin gwamna.
Wasu ko cewa suka yi aure ba a auna shi da nuna soyayya a bainar jama’a ba, sai dai yadda ma’aurata ke mu’amala da juna a sirrance.
Sarki ya kunyata Mai Martaba a taro
A baya, an ji cewa an samu wata hatsaniya a wurin wani taro da manyan sarakunan kasar Yarbawa biyu suka halarta a Ibadan, babban birnin jihar Oyo.
Lamarin ya faru ne lokacin da Olubadan na kasar Ibadan ya iso wurin taron, ya zauna a wurin da aka tanadar masa kusa da Alaafin.
Sarakunan gargajiya na Ibadan sun nuna fushinsu kan rashin girmamawar da Alaafin ya nunawa Olubadan a wurin taron.
Asali: Legit.ng
