Ana Fama da Rashin Tsaro, 'Yan Sanda Sama da 5,000 Za Su Ajiye Aiki, An Ji Dalili

Ana Fama da Rashin Tsaro, 'Yan Sanda Sama da 5,000 Za Su Ajiye Aiki, An Ji Dalili

  • Rundunar 'yan sandan Najeriya da ke taimakawa wajen samar da tsaro za ta rasa wasu daga cikin jami'an da ke aiki karkashinta a shekarar 2026
  • Fiye da jami'an 'yan sanda 5,000 ne ake sa ran za su ajiye aikinsu bayan sun kwashe shekaru suna hidimtawa kasar nan
  • An ba su shawara su tabbatar da daidaita bayanan da ke cikin takardunsu domin gujewa samun matsala wajen karbar hakkokinsu na fansho

​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Kano - Hukumar kula da fanshon ’yan sandan Najeriya ta bayyana adadin jami'an da za su yi ritaya daga aiki a shekarar 2026.

Hukumar ta bayyana cewa fiye da jami’an ’yan sanda 5,000 ake sa ran za su yi ritaya daga aiki a shekarar 2026.

Jami'an 'yan sanda 5,000 za su ajiye aiki a 2026
Sufeto Janar na 'yan sanda, Kayode Egbetokun da wasu jami'an 'yan sanda Hoto: @PoliceNG
Source: Twitter

Jaridar Daily Trust ta ce mataimakin kwamishinan ’yan sanda (DCP) Sani Doki Yusuf, wanda shi ne Kwamishinan fanshon ’yan sanda a hedkwatar rundunar da ke Abuja, ne ya bayyana hakan.

Kara karanta wannan

Mutanen da aka sace suna tsakiyar ibada a Kaduna sun bar hannun 'yan bindiga

An wayar da kan jami'an 'yan sanda

Ya bayyana hakan ne yayin wani shirin wayar da kai da aka gudanar a Kano ga tsofaffin jami’an ’yan sanda da kuma waɗanda aka tsara za su yi ritaya a 2026.

Kwamishinan ya ce an shirya shirin ne domin tunatar da jami’an muhimmancin samun cikakkun takardu da daidaitattun bayanai, yana mai cewa yawancin matsalolin da ake fuskanta a batun fansho na faruwa ne sakamakon bambance-bambance a bayanan sirri.

Ya yi kira ga jami’an da ke aiki da waɗanda suka riga suka yi ritaya da su sabunta bayanansu, domin kauce wa jinkiri wajen karɓar hakkokin fansho, jaridar Leadership ta kawo labarin.

"Manufar wannan shiri ita ce tunatar da abokan aikinmu muhimmancin daidaita takardun fanshonsu domin kauce wa matsaloli. Jami’ai da dama na fuskantar ƙalubale a yau saboda ba su sabunta takardunsu yadda ya kamata ba.”

- Sani Doki Yusuf

'Yan sanda na samun matsala wajen fansho

Sani Yusuf ya bayyana cewa bambance-bambance a sunaye da sauran bayanan sirri, wanda sau da yawa ke faruwa sakamakon sauye-sauyen da jami’ai ke yi a tsawon aikinsu, sun kasance babban ƙalubale wajen sarrafa fansho, lamarin da ya sa ake buƙatar ci gaba da wayar da kai a faɗin ƙasa.

Kara karanta wannan

Sarki ya fasa ƙwai, ya faɗi kuskuren sojoji, DSS da ya jawo kisan mutum 75 a Kwara

Ya kara da cewa, duk da cewa hukumar ta riga ta biya hakkokin fansho ga tsofaffin jami’ai da dama, akwai fiye da jami’an ’yan sanda 5,000 da ake sa ran za su yi ritaya a shekara mai zuwa a faɗin ƙasar nan.

'Yan sanda za su yi ritaya a shekarar 2026
Sufeto Janar na 'yan sandan Najeriya, Kayode Egbetokun Hoto: @PoliceNG
Source: Twitter

An gayyato masana kan harkar fansho

Hakazalika ya ce shirin wayar da kan, wanda ya haɗa da ƙwararrun masana harkar fansho, zai taimaka wa jami’ai su fahimci ka’idojin fansho tare da rage nauyin da ke kan hukumar.

“Saƙona gare su shi ne su koma rundunoninsu su tabbatar an kammala tsara dukkan takardun fanshonsu yadda ya kamata."

- DCP Sani Doki Yusuf

'Yan sanda sun kama malami

A wani labarin kuma, kun ji cewa jami'an rundunar 'yan sandan jihar Osun sun cafke wani babban limamin masallacin Juma'a.

Jami'an 'yan sandan sun kama babban limamin ne na masallacin Jumu'a na Ummu Hanni Adigu da ke yankin Ogo-Oluwa a birnin Osogbo, tare da wasu mutum uku.

Dakarun 'yan sanda sun kama su ne biyo bayan mutuwar wani mai fentin mota, Najeem Hammed, bayan wani rikici da ya faru tsakaninsa da masu ibada

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng