Rasuwar Sanata Ta Girgiza Majalisar Dattawa, Ta Yi Zama na Musamman don Girmama Shi
- Iyalai da 'yan uwan marigayi Sanatan Enugu ta Arewa, Okechukwu Ezea sun halarci zaman Majalisar Dattawa tare da gawarsa
- Majalisar dattawa ta yi zama na musamman domin karrama marigayin, tare da yi masa addu'o'in samun rahama na addinin Musulunci da Kiristanci
- A watan Nuwamban 2025 aka tabbatar da rasuwar Sanata Ezea yana da shekaru 62 da haihuwa, amma har kawo yanzu ba a birne gawarsa ba
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Majalisar Dattawa, a zamanta na ranar Laraba, ta yi jimami tare da girmama marigayi Okechukwu Ezea, sanatan da ya wakilci mazaubar Enugu ta Arewa.
Idan za ku iya tunawa da Sanata Ezea ya riga mu gidan gaskiya ranar 18 ga watan Nuwamba, 2025, yana dan shekara 62.

Source: Twitter
An kai gawar Sanata Ezea zauren Majalisa
Kafin fara zaman na musamman, an ajiye gawar marigayin a harabar zauren majalisar domin jami'ai da abokan aiki su yi masa bankwana, kamar yadda Premium Times ta kawo.
Matar marigayin, ’ya’yansa, da danginsa sun halarci zaman bayan da majalisar ta dakatar da dokarta ta 12 domin ba wa baki damar shiga zauren.
Rasuwar sanata ya girgiza Majalisar dattawa
Shugaban masu rinjaye na majalisar, Sanata Opeyemi Bamidele, shi ne ya gabatar da kudirin karrama marigayin. Ya bayyana cewa mutuwar sanatan ta zo musu da matukar kaduwa.
"Wannan mutuwa ta raba mu da mutum mai natsuwa kuma mai kishin kasa, Najeriya ra ti rashin bawan Allah da ya yi imani da adalci da kuma hidimar jama'a," in ji Bamidele.
Ya kara da cewa Ezea babban dan kasuwa ne da ya bada gudunmawa a sassa daban-daban na gwamnati da kamfanoni masu zaman kansu, yana mai bayyana shi a matsayin gwarzo.
Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya bayyana cewa majalisar tana cikin matukar jimami, inda ya kira marigayin a matsayin amintacce, wanda ya yi aiki tukuru.
Shi ma Mataimakin Shugaban Majalisar, Sanata Barau Jibrin, ya bayyana shi a matsayin "mutumin kwarai" wanda ke tsayawa kan abin da ya yi imani da shi.

Source: Facebook
Majalisa ta girmama marigayi Sanata Ezea
Bayan an kwashe kusan sa'o'i uku ana fadin alhairan marigayin, majalisar ta gudanar da addu'o'i na addinin Musulunci da Kiristanci domin nema masa gafara, tare da yin shiru na minti daya don karrama shi.
Haka kuma, majalisar ta yanke shawarar aika tawaga ta musamman domin ta'aziyya ga iyalansa da gwamnatin jihar Enugu da kuma aika wata babbar tawaga da za ta halarci jana'izarsa ta karshe.
A karshen zaman, sanatocin sun bi sahu daya-bayan-daya domin duba gawar abokin aikin nasu a karon karshe, kamar yadda The Nation ta ruwaito.
An yi jana'izar Sanata Godiya Akwashiki
A wani rahoton, kun ji cewa Shugaban Majalisar Dattawan, Sanata Godswill Akpabio, tare da mataimakinsa, Barau Jibrin sun halarci jana'izar abokin aikinsu, Sanata Godiya Akwashiki.
An gudanar da jana’izar ne a Cocin St. Williams Catholic Cathedral da ke birnin,' Lafiya, jihar Nasarawa inda manyan shugabanni daga sassa daban-daban na ƙasar suka halarta.

Kara karanta wannan
An samu sabani tsakanin Majalisar Dattawa da ta wakilai wajen gyara dokar zaben Najeriya
Da yake jawabi a wurin jana'izar, Sanata Barau Jibrin ya ce Majalisar Dattawa ta yi babban rashi sakamakon mutuwar Akwashiki.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

