Kwankwaso Ya Girgiza kan Harin 'Yan Ta'adda a Kwara, Ya ba Gwamnati Mafita

Kwankwaso Ya Girgiza kan Harin 'Yan Ta'adda a Kwara, Ya ba Gwamnati Mafita

  • Ana ci gaba da jimamin kisan gillar da 'yan ta'adda suka yi wa wasu mutane a kauyukan jihar Kwara da ke yankin Arewa ta Tsakiya
  • Hare-haren ta'addancin sun jawo asarar rayuka sama da 100 na mutanen da ba su san hawa ba, ba su san sauka ba
  • Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya bi sahun yin Allah wadai kan mummunan harin, tare da ba shawararsa ga gwamnatin tarayya

​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Kano - Tsohon ɗan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP, Rabiu Kwankwaso, ya yi tir da mummunan hare-haren da aka kai wa al’ummomin Woro da Nuku a karamar hukumar Kaiama ta jihar Kwara

Kwankwaso ya bayyana kisan gillar a matsayin dabbanci, yana mai gargaɗin gwamnatin tarayya da kada ta ɗauki lamarin tabarbarewar tsaro da wasa.

Kwankwaso ya yi Allah wadai da harin Kwara
Tsohon dan takarar shugaban kasa na NNPP, Rabiu Musa Kwankwaso Hoto: Rabiu Musa Kwankwaso
Source: Facebook

Rabiu Musa Kwankwaso ya yi Allah wadai da hare-haren ne a wani rubutu da ya yi a shafinsa na X a ranar Laraba, 4 ga watan Fabrairun 2026.

Kara karanta wannan

Kalaman Kwankwaso na taimaka wa Abba Kabir a shari'ar 2019 sun jefa shi a matsala

'Yan ta'adda sun kashe mutane a Kwara

Hare-haren, da suka faru a yammacin ranar Talata, 3 ga watan Fabrairun 2026 sun yi sanadin mutuwar jama’a da dama, tare da tilasta wa al’ummomi da yawa barin muhallansu.

Lamarin da ya janyo ƙorafi a faɗin ƙasa da kuma sabon fargaba kan yaɗuwar ƙungiyoyin ta’addanci zuwa yankunan da a baya suke cikin kwanciyar hankali.

Me Kwankwaso ya ce kan harin Kwara?

Da yake mayar da martani kan hare-haren, Kwankwaso ya ce ya shiga bakin ciki da firgici matuƙa bayan jin labarin yawan mutanen da suka rasa rayukansu a hare-haren.

"Na ji matukar bakin ciki da firgici kan rahoton kisan gillar akalla mutane 162 da ba su ji ba, ba su gani ba a al’ummomin Woro da Nuku na jihar Kwara.”

- Rabiu Musa Kwankwaso

Da yake yin Allah-wadai da harin, tsohon gwamnan na jihar Kano ya bayyana lamarin a matsayin aikin ta’addanci da bai kamata a bari ya samu gurbi a ko ina cikin kasar nan ba.

Kara karanta wannan

Shaidar EFCC ta yi bayani kan alakar Yahaya Bello da zargin almundahar N80bn

“Wannan mummunan hari abin Allah-wadai ne kwarai. ’Yan ta’adda ne suka aikata shi, kuma bai kamata a lamunta ko a bari ya bunkasa a kowane sashe na kasarmu ba."

- Rabiu Musa Kwankwaso

Sanata Kwankwaso ya yi gargadi

Ya yi gargaɗi cewa kungiyoyin 'yan ta'adda na faɗaɗa ayyukansu zuwa yankunan da a baya suka kasance cikin zaman lafiya, lamarin da ke kara nauyi a kan hukumomin tsaro.

“Kamar yadda na dade ina gargaɗi, bai kamata gwamnatin tarayya ta iya yin sakaci da waɗannan abubuwa ba. Waɗannan ƙungiyoyin 'yan ta'adda na ci gaba da shimfiɗa ayyukansu zuwa yankunan da a baya suke da zaman lafiya da tsaro."
“Da kowace rana da ta wuce, nauyin da ke kan rundunar sojojinmu na kara tsananta, kuma buƙatar ɗaukar mataki mai ƙarfi, haɗin kai da gaggawa na ƙara zama dole."

- Rabiu Musa Kwankwaso

Kwankwaso ya yi ta'aziyya kan harin Kwara
Jagoran Kwankwasiyya, Sanata Rabiu Mua Kwankwaso Hoto: Rabiu Musa Kwankwaso
Source: Facebook

Magudun Kwankwasiyya ya yi ta'aziyya

Kwankwaso wanda ya ziyarci yankin Kaiama a mota lokacin yakin zaben 2023 ya kuma miƙa ta’aziyyarsa ga iyalan waɗanda abin ya shafa da al’ummar jihar Kwara.

“Ina miƙa ta’aziyya ta daga zuciya ga iyalan waɗanda suka rasa rayukansu, daukacin al’ummar jihar Kwara da gwamnatin jihar a wannan mummunan al’amari."

Kara karanta wannan

Sarki ya fasa ƙwai, ya faɗi kuskuren sojoji, DSS da ya jawo kisan mutum 75 a Kwara

“Allah Ya ji ƙan waɗanda suka rasu, Ya kuma ba duk masu jimami haƙuri da juriyar wannan babban rashi."

- Rabiu Musa Kwankwaso

Tinubu ya dauki mataki kan harin kwara

A wani labarin kuma, kun ji cewa Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya tura sojoji sakamakon harin da 'yan ta'adda suka kai a jihar Kwara.

Tinubu ya bayyana cewa ya umarci tura bataliyar sojojin Najeriya zuwa kauyen Woro da ke karamar hukumar Kaiama a jihar Kwara, biyo bayan mummunan harin.

Shugaban kasar ya ce sabon rundunar sojojin da aka tura za ta jagoranci Operation Savannah Shield domin murkushe ‘yan ta’adda da kuma kare al’ummomin da ba su da kariya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng