Bayan Kusan Shekaru 50, Uba Sani Ya Kaddamar da Hanya a Garin Kaduna
- Gwamna Uba Sani ya kaddamar da titin Pambeguwa–Kahutu–Kauru mai tsawon kilomita 22 bayan kusan shekaru 50 ana jira
- Sabon titin da jama'a suka shafe tsawon lokaci suna fafutukar a yi, zai rage nisan tafiya daga awa guda zuwa kasa da mintuna 12
- Gwamnatin Kaduna ta ce tana aiwatar da manyan ayyukan hanyoyi 140 a fadin jihar yayin da ta ke kokarin sauke nauyin jama'a
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kaduna – Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya share hawayen al’ummomin da ke kan hanyar Pambeguwa–Kahutu–Kauru.
Mutanen yankunan sun shafe kusan shekaru 50 suna fatan samun ingantacciyar hanya. Amma sai a ranar Talata, 3 ga watan Fabrairu, 2026 burinsu ya cika.

Source: Facebook
Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa a wannan rana ne Gwamnan Kaduna, Uba Sani ya kaddamar da titin kwalta mai tsawon kilomita 22 da ke hada kananan hukumomin Kubau da Kauru.
An kaddamar da hanya a Kaduna
Jaridar The Nation ta ruwaito cewa yake jawabi a wajen bikin kaddamarwar, Gwamna Uba Sani ya tuno da cewa a ranar 27 ga Agusta, 2024, lokacin da ya zo domin fara aikin gina titin.
Sai dai a cewarsa, a ranar Talata tafiyar ta dauki kasa da mintuna 12, sakamakon kammala aikin titin da jama'a suka dade suna fatan a gina masu.
Gwamnan ya bayyana cewa Karamar Hukumar Kauru na daga cikin kananan hukumomi 12 da ba su amfana da ko aikin hanya daya ba a cikin shekaru 12 da suka gabata.
Ya jaddada cewa gwamnatocin baya sun fahimci muhimmancin wannan hanya tare da yin kokarin gina ta, amma saboda dalilai daban-daban, aikin bai taba kammaluwa ba.
Uba Sani:
“Lokacin da muka fara aikin wannan titi a ranar 27 ga Agusta, 2024, mun dauki alkawari ga al’ummar wadannan yankuna. A yau mun dawo ba da uzuri ko bayani ba, sai dai da kammalallen aiki da ke magana da kansa."

Kara karanta wannan
Yadda aka gyara Tudun Biri bayan sojojin Najeriya sun yi kuskuren jefa bam a taron Maulidi
Uba Sani ya yi alkawarin gina titi
Gwamna Uba Sani ya kuma yi alkawarin gina titunan cikin gari a Kauru tare da kawo karshen kusan shekaru 20 na rashin wutar lantarki da yankin ke fama da shi.

Source: Facebook
Ya tunatar da cewa tun bayan hawansa mulki, gwamnatinsa ta fara wani shiri mai fadi da tsari na sabunta ababen more rayuwa.
A cewarsa:
“Mun fara gina hanyoyi 140 da suka kai tsawon kilomita 1,335 a dukkannin yankunan sanatan Jihar Kaduna guda uku.”
Gwamnan Kadunan ya ce sabon titin Pambeguwa–Kahutu–Kauru zai rage cunkoso, saukaka zirga-zirga, da rage kudin sufuri.
Ya kara da cewa jami’an da ke aikin gaggawa, dalibai, manoma da ‘yan kasuwa za su amfana matuka.
Hadimar Gwamnan Kaduna ya sha da kyar
A baya, kun samu labarin cewa hadimar Gwamna Uba Sani, Hon. Rachael Averik, ta tsallake rijiya da baya bayan da wasu ‘yan bindiga suka kai mata hari a yankin Kudancin Kaduna.

Kara karanta wannan
Mutum 2 sun mutu a hanyar zuwa jana'izar mataimakin gwamnan da ya rasu a Najeriya
Rahotanni sun nuna cewa Hon. Rachael Averik ta tsira daga harin cikin koshin lafiya, sai dai direbanta da kuma wani dan sanda da ke tare da ita sun samu raunuka.
Lamarin ya faru ne a ranar Alhamis, 2 ga watan Janairu, 2025, a tsakanin kauyukan Tsauni Majidadi da Gani da ke karamar hukumar Sanga ta jihar Kaduna.
Asali: Legit.ng
