Harin Kwara Ya Kara Muni, Adadin Mutanen da Suka Rasa Rayukansu Ya Haura 80

Harin Kwara Ya Kara Muni, Adadin Mutanen da Suka Rasa Rayukansu Ya Haura 80

  • Adadin mutanen da suka rasa rayukansu a farmakin da 'yan bindiga suka kai kauyukan Woro da Nuku a karamar hukumar Kaiama, jihar Kwara ya karu
  • Mazauna yankin sun bayyana cewa mutanen da aka gano sun mutu a harin sun kai kimanin 86, ciki har da 'ya'yan Sarkin Wuro guda biyu
  • Bayanai sun nuna cewa an tura jami'an tsaro zuwa yankin domin dawo da zaman lafiya da farauto 'yan bindigar da suka aikata wannan danyen aiki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kwara, Nigeria - Adadin wadanda suka riga mu gidan gaskiya a harin da ’yan bindiga suka kai ranar Talata a kauyukan Woro da Nuku da ke karamar hukumar Kaiama a jihar Kwara ya karu zuwa mutum 86.

Majiyoyi da dama sun ce har da ’ya’yan Sarkin Woro guda biyu a cikin wadanda ’yan bindigar suka kashe tare da kona fadar basaraken, gidajen jama’a, da shaguna kurmus.

Kara karanta wannan

Ana murna sulhu ya fara aiki, 'yan bindiga sun shiga gari sun kashe akalla mutune 20

Jihar Kwara.
Taswirar jihar Kwara da ke Arewa ta Tsakiya a Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Wata majiya ta shaida wa jaridar Leadership cewa maharan sun kashe mutane da yawa, kuma adadin na kara karuwa.

"Yanzu haka wadanda aka kashe sun wuce 40, kuma sojoji da masu gadin daji sun mamaye kauyukan biyu," in ji majiyar.

Mutanen da aka kashe sun haura 80

Sai dai wani tsohon dan majalisar dokokin jihar Kwara kuma shugaba a yankin Kaiama, Hon. Aliyu Mande, ya jaddada cewa adadin ya fi haka.

"Dan uwana, adadin wadanda suka mutu ya wuce 40, kimanin mutum 86 ne, har da ’ya’yan Sarki biyu. Daya daga cikin ’ya’yan Sarkin da aka kashe ya kammala karatu a makarantar koyon aikin jinya a shekarar 2025," in ji Mande.

Shi ma wani mazaunin kauyen Woro, Alh. Usman Ibrahim Woro, ya bayyana cewa mutane 80 ne suka riga mu gidan gaskiya a lissafinsa.

Yadda yan bindiga suka yi ta'adi a Kwara

Tun farko dai, tashar Channels tv ta ruwaito cewa ’yan bindigar sun kaddamar da harin ne da misalin karfe 5:30 na yammacin ranar Talata.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun bankawa fadar mai martaba sarki wuta, sun kashe bayin Allah a Kwara

Rahotanni sun nuna cewa a rahoton farko, an tabbatar da cewa 'yan ta'addan sun hallaka mutane 10 kafin adadin ya karu.

Gwamnan Kwara.
Gwamnan jihar Kwara kuma shugaban gwamnonin Najeriya, AbdulRahman AbdulRazaq Hoto: @AARahman
Source: Facebook

Babban Mataimaki ga Gwamnan jihar Kwara kan harkar Tsaro, Alh. Muhideen Aliyu, ya tabbatar da faruwar lamarin a lokacin da yake tattaunawa da yan jarida ta wayar tarho.

Rahotanni sun nuna cewa tuni aka tura dakarun sojoji da masu gadin daji zuwa kauyukan Woro da Nuku domin kakkabe ragowar ’yan bindigar da ke yankin.

Mahara sun kashe mutane 20 a Katsina

A wani labarin, kun ji cewa ’yan bindiga sun kai hari yankin ƙaramar hukumar Faskari da ke Jihar Katsina , inda suka kashe mutane da dama, suka kuma lalata gidaje da shaguna.

Shugaban ƙaramar hukumar Faskari, Sirajo Daudawa, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce ana zargin harin na ɗaukar fansa ne kuma maharan sun kashe akalla mutane 20.

A cikin wata sanarwa da kakakin rundunar ’yan sandan jihar, Abubakar Sadiq, ya fitar a daren Talata, ya ce DPO na yankin ya jagoranci dakarunsa tare da hadin gwiwar sojoji da dakarun C-Watch zuwa garin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262