Ana Murna Sulhu Ya Fara Aiki, 'Yan Bindiga Sun Shiga Gari Sun Kashe Akalla Mutune 20

Ana Murna Sulhu Ya Fara Aiki, 'Yan Bindiga Sun Shiga Gari Sun Kashe Akalla Mutune 20

  • 'Yan bindiga sun kai hari garin Doma da ke karamar hukumar Faskari a jihar Katsina, sun kashe mutane kuma sun gona gidaje
  • Shugaban karamar hukumar Faskari, Sirajo Daudawa ya ce akalla mutane 20 aka kashe a harin duk da sun yi sulhu da 'yan bindiga
  • Rundunar 'yan sanda ta bayyana cewa ta tura jami'an tsaro zuwa yankin kuma komai ya daidaita zuwa yanzu

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Katsina, Nigeria - ’Yan bindiga sun kai hari yankin ƙaramar hukumar Faskari da ke Jihar Katsina, inda suka kashe mutane da dama, suka kuma lalata gidaje, shaguna, da motoci.

Rahotanni sun nuna cewa wannan mummunan hari da yan bindigar suka kai ya raba mutane da yawa da muhallansu.

Jihar Katsina.
Taswirar jihar Katsina da ke Arewacin Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Tashar Chanels tv ta tattaro cewa lamarin ya faru ne a garin Doma, yankin Tafoki, da ke karamar hukumar Faskari da misalin ƙarfe 4:30 na yammacin ranar Talata.

Kara karanta wannan

Harin 'yan bindiga a Katsina ya girgiza majalisa, ta mika bukata wajen Tinubu

Yan bindigan, waɗanda ke ɗauke da makamai har da bindigu ƙirar AK-47, sun mamaye garin ne watanni biyar bayan cimma yarjejeniyar zaman lafiya.

An kashe mutane 20 a harin Doma

Shugaban ƙaramar hukumar Faskari, Sirajo Daudawa, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce ana zargin harin na ɗaukar fansa ne.

Ya ce:

"Wannan yanayi abin takaici ne kwarai. Ba mu sami wani mummunan hari ba cikin watanni biyar da suka gabata, sai wannan da muka tsinci kanmu a ciki.
"Mun rasa aƙalla mutane 20. Miyagun sun ƙone gidaje da motoci da dama, mun sanar da jami’an tsaro, amma abin takaici babu wanda ya iya isa wurin sai bayan ’yan bindigar sun gama abin da suka ga dama.
"Yanzu dai an kwashe gawarwakin waɗanda aka kashe zuwa yankin Tafoki, kuma za a birne su gobe (Laraba) da safe."

Martanin rundunar 'yan sanda

A nasa ɓangaren, Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Katsina, Bello Shehu, ya jajanta wa iyalai da abokan arziƙin waɗanda harin ya shafa, kamar yadda Premium Times ta kawo.

Kwamishinan ya yi Allah-wadai da harin, sannan ya ba da umarnin tura ƙarin jami'ai don hanzarta bincike da kuma kamo waɗanda suka aikata hakan.

Kara karanta wannan

A rana guda, 'yan bindiga sun kashe fiye da mutane 50 a wasu jihohin Arewa 2

A cikin wata sanarwa da kakakin rundunar ’yan sandan jihar, Abubakar Sadiq, ya fitar a daren Talata, ya ce DPO na yankin ya jagoranci dakarunsa tare da hadin gwiwar sojoji da dakarun C-Watch zuwa wurin da abin ya faru.

Yan sanda.
Jami'an rundunar yan sandan Najeriya a bakin aiki Hoto: @PoliceNG
Source: Getty Images

Sai dai rundunar ta bayyana cewa, kafin jami’an su isa, maharan sun riga sun harbe mutane 13 har lahira, kuma sun tsere daga wurin. To sai dai jami'an sun tabbatar da cewa yanzu komai ya daidaita a yankin.

'Yan bindiga sun farmaki 'yan gidan biki

A wani labarin, kun ji cewa wasu 'yan bindiga sun farmaki 'yan gidan biki a yankin karamar hukumar Kankara ta jihar Katsina.

Bayanai sun nuna cewa yan bindigar sun kashe akalla mutane biyu daga tawagar masu zuwa biki a harin yayin da wasu da dama, ciki har da amarya, suka jikkata.

Harin ya zo ne a daidai lokacin da gwamnatin jihar Katsina ke shirin sakin mutane 70 da ake zargi da hannu a ayyukan ta’addanci.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262