Bayan Turo Sojoji, Amurka Za Ta Bude Ofishin Jakadanci Mafi Girma a Najeriya

Bayan Turo Sojoji, Amurka Za Ta Bude Ofishin Jakadanci Mafi Girma a Najeriya

  • Amurka za ta kashe kimanin dala miliyan 537 wajen gina ofishin jakadancin da zai zama mafi girma a duniya a birnin Legas, Najeriya
  • Akalla yan Najeriya 2,500 ne ke samun ayyukan yi a wurin ginin dake ci gaba da gudana a halin yanzu, kuma da yiwuwar kaddamarwa a 2028
  • Ana ganin matakan Donald Trump kan korar bakin haure ba za su shafi wannan babban aiki da Amurka ke yi a fannin diflomasiyya a Najeriya ba

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Legas - Gwamnatin Amurka ta tabbatar da cewa aikin ginin sabon ofishin jakadancinta a Legas, wanda aka zuba dala miliyan 537, zai kammala kuma a fara amfani da shi a farkon shekarar 2028.

Wannan ginin, mai hawa 10, yana kan fili mai faɗin eka 12.2, kuma ana sa ran zai zama ofishin jakadancin Amurka mafi girma a duniya idan an kammala shi.

Kara karanta wannan

Kwamitin Sarkin Musulmi ya yi magana kan duba watan Ramadan 2026

Amurka za ta bude ofishin jakadanci mafi girma a duniya a birnin Legas
Shugaban kasar Amurka, Donald Trump a cikin motar kwasar shara. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Tasirin ginin ofishin Amurka ga Najeriya

Wannan babban aiki ba kawai ya shafi gina ofishi ba ne, jaridar Punch ta ce aikin zai kawo gagarumin ci gaba ga tattalin arziƙin Najeriya ta hanyar zuba jari da samar da ayyukan yi.

  • Zuba jari: An kiyasta cewa aikin zai jawo zuba jarin dala miliyan 95 kai-tsaye cikin tattalin arziƙin cikin gida na Najeriya.
  • Ayyukan yi: Aƙalla ƴan Najeriya 2,500 ne ke aiki a wurin, waɗanda suka haɗa da injiniyoyi, magina, leburori, da masu fasaha daban-daban.
  • Kwarewa: Ma'aikata suna samun horo na musamman kan fasahar gine-gine ta zamani da ƙa'idodin tsaro na duniya.

A halin yanzu, ginin ya kai matakin ƙarshe na hawa na 10, inda ma'aikata ke ci gaba da aikin shafa siminti a jikin katangu, da gina gada da hanyoyin da suka haɗa yakin da ginin.

Matakan Trump da fargabar korar 'yan Najeriya

Duk da wannan babban jari da Amurka ke zubawa a Najeriya, akwai damuwa a tsakanin ƴan Najeriya dake zaune a Amurka sakamakon tsauraran matakan shige-da-fice na shugaba Donald Trump.

Kara karanta wannan

Majalisar Amurka ta ki hakura, za a kuma zama kan zargin kisan kiristoci a Najeriya

Shugaba Trump ya sanya hannu kan jerin dokoki da nufin dakatar da bai wa yaran da aka haifa a Amurka izinin zama ɗan ƙasa idan iyayensu ba su da izinin zama a kasar, sannan ana barazanar korar ƴan Afirka dake zaune ba tare da izini ba.

Hukumomin Amurka a Najeriya sun bayyana cewa wannan ginin alama ce ta ƙarfin dangantakar dake tsakanin ƙasashen biyu wadda ta kwashe shekaru 65.

A cewarsu, manufofin cikin gida na Amurka ba za su shafi manyan ayyukan da suka tsara a Najeriya ba, domin an gina su ne don amfani na dogon lokaci, in ji rahoton The Cable.

An ce fiye da 'yan Najeriya 2,500 ne ke yin aiki a wurin da Amurka ke gina ofishin jakadancinta a Legas.
Taswirar jihar Legas, inda Amurka ke gina katafaren ofishin jakadanci mafi girma a duniya. Hoto: Legit.ng
Source: Original

Matsayin aikin ofishin a halin yanzu

Ginin wanda aka fara a shekarar 2022, da farko an yi tsammanin kammala shi a 2027, amma sabon jadawali ya nuna cewa sai 2028 ne za a soma aiki a ofishin.

Kwararrun ma'aikata kusan hudu ne ke kula da ɓangarori daban-daban na ginin, inda wasu ke gina babban ofishin, wasu kuma ke aikin hanyoyin sadarwa na yankin.

Masu lura da al'amuran yau da kullum sun bayyana cewa wannan ofishi zai sauƙaƙa ayyukan biza da kuma harkokin kasuwanci tsakanin Amurka da Najeriya.

Amurka ta turo karin sojoji Najeriya

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun bankawa fadar mai martaba sarki wuta, sun kashe bayin Allah a Kwara

A wani labari, mun ruwaito cewa, Amurka ta aiko da wasu rukunin sojoji zuwa Najeriya, domin ƙara haɗin gwiwa wajen yaƙar ta’addanci a kasashen Yammacin Afirka.

Majiyoyi suka ce matakin ya biyo bayan yarjejeniya tsakanin kasashen biyu cewa ana buƙatar ƙarin matakai kan barazanar ’yan ta’adda.

Gwamnatin Najeriya ta tabbatar da zuwan sojojin, yayin da take kara musanta zargin cin zarafin Kiristoci, tana mai cewa kowa na shan wahala daga matsalar tsaro.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com