Muhimman Abubuwa 5 da Bincike Ya Gano kan Shirin Juyin Mulkin da Aka Yi a Najeriya
A karshen watan Janairu, 2026, hedkwatar tsaron Najeriya ta fito ta tabbatar da labarin da aka jima ana yadawa game da yunkurin hambarar gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Tun a watan Oktoban 2025 aka fara yada jita-jitar cewa hukumomin tsaro sun damke wasu sojoji 16 da ake zargi da hannu a yunkurin yi wa Shugaba Tinubu juyin mulki.

Source: Twitter
Daily Trust ta ruwaito cewa bayan kimanin watanni uku da bullar wannan labari, hedkwatar tsaro ta tabbatar da lamarin, inda ta ce an kammala bincike kuma an mika rahoto ga shugaban kasa.
Kwamitin da rundunar sojin Najeriya ta kafa, ya gano abubuwa da dama game da wannan makarkashiya da aka shirya da nufin kawar da zababbiyar gwamnati a Najeriya.
Tun bayan mika wannan rahoto, aka fara samun bayanai kan abubuwan da binciken ya gano, da duka masu hannu a cikin shirin, kayan aikin da aka saya da wadanda aka shirya tura wa lahira.

Kara karanta wannan
Malami da fararen hula 4 da aka kama da zargin hannu a yunkurin juyin mulki a Najeriya
A wannan rahoton, mun tattaro muku muhimman abubuwan da bincike ya gano kan yunkurin juyin mulkin da aka yi a Najeriya, ga su kamar haka:
1. Mutane 40 ke da hannu a shirin
A binciken da aka gudanar tare hadin gwiwar rundunar sojojin kasa da Hukumar Tsaron Farin Kaya ta DSS, an gano cewa mutane 40 da suka kushi sojoji, fararen hula da tsofaffin sojoji na da hannu a shirin.
Legit Hausa ta kawo muku jerin sunayen duka wadanda binciken da ya gano suna da hannu a kitsa juyin mulkin, wanda suka hada da Birgediya Janar, Kanal, Laftanal Kanal da sauransu.
Vanguard ta wallafa cewa an fara kama wasu daga cikin wadanda ake zargin tun watan Oktoba, 2025, bayan samun bayanan sirri da ke nuna yiwuwar shirye-shiryen kifar da gwamnati ta karfi.
2. Wanda aka gano ya kitsa juyin mulkin
Rahoton binciken da aka gudanar wanda jaridar Punch ta tattaro ya nuna cewa wani Kanal mai aiki a rundunar sojin kasa ne ake zargi da jagorantar yunkurin juyin mulki.
An gano Kanal Mohammed Ma'aji a matsayin babban jagora a yunkurin juyin mulki da bai yi nasara ba kan gwamnatin Shugaba Tinubu.
Janar C.G Musa ya ce jami'in ya fara kitsa wannan makarkashiya ne bayan gaza samun karin girma duk da ya zauna jarabawa karin matsayi sau da dama a gidan soja.
Rahoton ya ce Kanal din ya juya damuwar da ya ke ciki zuwa wata dabara ta jawo mutane cikin shirinsa, inda ya fara tuntubar jami’ai daga rundunar sojin kasa, ruwa da ta sama.

Source: Facebook
3. Shirin kashe manyan shugabanni
Har ila yau, masu binciken sun gano cewa wadanda suka kitsa juyin mulkin sun shirya kashe manyan shugabanni da jami'an gwamnatin Najeriya.
A rahoto da ya bayyana bayan mika rahoton bincike, wadanda aka yi shirin kashe su sun haɗa da Shugaba Tinubu, Kashim Shettima, Shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, da kuma Shugaban majalisar wakilai, Rt. Hon. Tajudeen Abbas.
A wata hira da tashar Channels tv ta yi da Ministan Tsaro, Janar C. G Musa (mai ritaya), ya ce shi kansa yana daga cikin mutanen da wadanda ake zargi suka tsara kama shi, ko su kashe shi.
Binciken ya nuna cewa sun yi shirin tura su lahira a ranar da dukkaninsu suke cikin ƙasar, sannan a kama manyan hafsoshin tsaro a tsare su domin kafa gwamnatin soja.
4. Sayen motoci samfurin SUV
Jami'an da suka gudanar da bincike sun gano cewa wadanda ake zargi da kulla makarkashiyar kifar da gwamnatin Tinubu sun sayi motoci guda 32 samfurin SUV, domin taimaka musu wajen aiwatar da shirinsu.
Majiyoyin tsaro da ke da masaniya kan lamarin sun shaida wa jaridar Premium Times cewa masu bincike sun gano hujjojin sayen motocin.
'Daya daga cikin majiyoyi ta bayyana cewa an gano takardun shaidar sayayya, gami da rasidi da bayanan hada-hadar kudi a lokacin gudanar da bincike.
Ana zargin an yi amfani da motocin wajen jigilar jami’an da ke cikin shirin ba tare da janyo hankalin jama’a ba, da kuma gudanar da sintiri na leken asiri.
5. An kwato manyan makamai
Wani karin shiri da bincike ya gano wadanda ake zargi sun yi, shi ne sayen manyan makamai, motocin yaki da za su yi amfani da su wajen aiwatar da manufarsu.
Bayanan da suka fito bayan kammala bincike sun tabbatar da cewa masu bincike sun ƙwato motocin ɗaukar bindiga guda biyu da bindigogin harbo jiragen sama.
Haka zalika an kwato bindigogin PKT, bama-baman RPG, bindigogin AK-47, harsasai da kayan aikin soja, duka daga wani Laftanar-Kanar da ke cikin wadanda suka kitsa kifar da gwamnati.

Source: Facebook
Juyin mulki: Sunayen sojoji 16 da aka kama
A wani rahoton, kun ji cewa Hedkwatar tsaron Najeriya (DHQ) ta tabbatar da kama sojoji 16 da ake zargi da hannu a yunkurin yi wa shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu juyin mulki.
Hedkwatar ta ce an gano laifuffukan da sojoji 16 suka aikata ciki har da fara shirin kifar da gwamnati mai ci, wanda ya saba wa dokar gidan soja.
Ta bayyana cewa binciken ya duba dukkan al'amuran da suka shafi ayyukan jami’an, inda aka gano cewa da dama daga cikin sojojin suna da laifuffukan da za su amsa a gaban kotu.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
