Sanatoci Sun Fara Aiki a kan Sabon Kudirin da Zai Kara wa Gwamnatin Tarayya Kudi

Sanatoci Sun Fara Aiki a kan Sabon Kudirin da Zai Kara wa Gwamnatin Tarayya Kudi

  • Majalisar Dattawan Najeriya ta fara yunkurin ƙara kaso na kuɗIn shiga da ake bai wa gwamnatin tarayya idan an yi rabo
  • Kudirin yana neman sauya tsarin rabon kuɗIn shiga da ke cikin Kundin Tsarin Mulki na 1999 da aka yi wa kwaskwarima
  • Sanatocin dake Majalisa sun ce nauyin lamarin tsaro, hanyoyi da sauran ayyuka ya yi wa gwamnatin tarayya yawa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja Majalisar Dattawan Najeriya ta fara bibiyar matakan sauya wasu tanade-tanade na Kundin Tsarin Mulki na shekarar 1999.

Ana son kara kason kudin shiga da ake bai wa gwamnatin tarayya a tsarin rabon kuɗin shiga na ƙasa saboda wasu dalilai da aka gano.

An fara duba yiwuwar kara kason kudin gwamnatin tarayya
Wasu daga cikin Sanatocin Najeriya a yayin zamansu a Abuja Hoto: The Nigerian Senate
Source: Facebook

Jaridar The Cable ta wallafa cewa wannan mataki ya biyo bayan ƙorafe-ƙorafen da majalisar ke yi cewa kuɗin da ake bai wa gwamnatin tarayya ya yi kadan.

Kara karanta wannan

Harin 'yan bindiga a Katsina ya girgiza majalisa, ta mika bukata wajen Tinubu

Sanatoci za su kara kason kudin gwamnatin tarayya

Dazu ne jaridar Punch ta wallafa cewa a tsarin rabon kuɗin shiga da ake amfani da shi yanzu, gwamnatin tarayya na karɓar 52.68%.

Ana son kara kason kudin gwamnatin tarayya saboda ayyukan da ke gabanta
Sanatoci yayin zama a majalisar dattawan Najeriya Hoto: The Nigerian Senate
Source: UGC

Haka kuma jihohi 36 na Najeriya na karbar 26.72% yayin da ƙananan hukumomi 774 ke samun 20.60%. Duk da kasancewar gwamnatin tarayya na da mafi girman kaso, majalisar dattawa ta ce akwai buƙatar ƙarin kuɗi saboda nauyin ayyuka da ke wuyanta.

Kara karanta wannan

Zargin ta'addanci: Dalung ya kalubalanci kama Malami da DSS ta yi

Dalilan Sanatoci na neman kara kason gwamnatin tarayya

Yunkurin neman kara kason gwamnatin tarayya na ƙunshe ne a cikin wani ƙudiri da Sanata Sunday Karimi, mai wakiltar Kogi ta Yamma, ya gabatar, kuma tuni ya tsallake karatu na farko.

Da yake magana da manema labarai bayan zaman, Karimi ya bayyana cewa manufar ƙudirin shi ne ceto gwamnatin tarayya daga matsanancin ƙarancin kuɗi.

Sanatan ya ce tsarin rabon kuɗin shiga na yanzu ya tsufa kuma bai dace da halin da ƙasar ke ciki ba saboda gwamnatin tarayya na da aiki da yawa a gabanta.

Karimi ya bayyana cewa ƙarancin kuɗi ya ƙara lalata yanayin hanyoyin gwamnatin tarayya a sassa daban-daban na ƙasar nan.

Haka kuma, ya ce yaki da ’yan bindiga, ta’addanci da sauran barazanar tsaro na ɗaya daga cikin manyan abubuwan da ke cin kuɗin gwamnatin tarayya.

A cewarsa, nauyin tsaron cikin gida, haɗe da gina wa da kula da hanyoyin tarayya a duk faɗin ƙasar, ya yi wa gwamnati yawa ƙarƙashin tsarin rabon kuɗin da ake amfani da shi yanzu.

Kara karanta wannan

Sarki Sanusi II ya fadi dalilan da suka sa ba zai yi shiru a kan harkokin gwamnati ba

Atiku ya soki Sanatoci kan dokar zabe

A baya, mun wallafa cewa tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya bayyana damuwa kan yadda Majalisar Dattawan Najeriya ke jinkirta ƙoƙarin gyara dokar zaɓe ta 2022.

A sanarwar da ya fitar a ranar Alhamis, 22 ga Janairu, 2026, Atiku ya zargi Sanatocin da yin wannan jinkiri da gangan, kuma zai iya kawo tarnaki ga sahihanci da amincin zaɓen 2027.

A cikin sanarwar, Atiku ya bayyana cewa kurakurai da ke cikin dokar zaɓe ta 2022, da kuma jinkirin da ake yi wajen gyara su, sun kawo kalubale ga babban zaben 2023 da ya gabata.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng