Tinubu Ya Sanar da Matsaya kan Janye Cire Tallafi da Sauran Manufofin Tattalin Arziki
- Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya jaddada cewa babu gudu, babu ja da baya a kan sauye-sauyen tattalin arzikin Najeriya
- Tinubu ya nemi Bankin Duniya da ya hanzarta tallafa wa ƙasar nan da sababbin hanyoyin kuɗi domin bunƙasa tattalin arziki
- Bankin Duniya ya ce Najeriya ta zama abin koyi a duniya kan aiwatar da gyare-gyaren tattalin arziki duk da wasu na kuka a gida
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCTA Abuja – Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa babu fashi a kan sauye-sauyen tattalin arzikin da gwamnatinsa ke aiwatarwa a ƙasar nan.
Shugaban ƙasan wanda aka zaba a 2023 ya jaddada cewa Najeriya ta shiga yanayin da dole sai an yi gyara, saboda haka ba za yi wasa da aikin da aka ɗauko ba.

Source: Twitter
Jaridar The Cable ta wallafa cewa Tinubu ya faɗi haka ne a ranar Talata, 4 ga watan Fabarairu 2026 a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja.
Bola Tinubu ya gana da tawagar Bankin Duniya
Ita kuwa Vanguard ta ce Tinubu ya bayyana manufar gwamnatinsa a lokacin da ya karɓi wata tawagar Bankin Duniya ƙarƙashin jagorancin Anna Bjerde, babbar daraktar ayyuka ta bankin, tare da mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima.
A cewar Tinubu, ko da yake matakan farko na gyare-gyaren tattalin arziki sun zo da raɗaɗi da wahala ga ‘yan ƙasa, amma hakan ba zai sa gwamnati ta fasa ba
Ya ce:
“Tun da muka shiga wannan mataki na gyara, mun rike wuta, kuma ba za mu sake duban baya ba."
Shugaban ƙasar ya bayyana manyan abubuwan da gwamnatinsa ta fi ba muhimmanci, daga ciki har da inganta aikin noma ta hanyar amfani da injuna domin cin gajiyar filayen noma masu yawa da kuma matasan ƙasar.
Tinubu ya faɗi manufar gwamnatinsa
Tinubu ya ce gwamnati na ƙoƙarin sauƙaƙa wa manoma ta hanyar kafa cibiyoyin injinan noma, samar da iri da sauran kayan aiki domin ƙara yawan amfanin gona.
Ya bayyana cewa sakamakon sauye-sauyen tattalin arziki ya fara bayyana, ciki har da raguwar hauhawar farashi da kuma daidaituwar darajar Naira.

Source: Facebook
Shugaban ƙasar ya nemi Bankin Duniya da ya ƙara hanzarta haɗin gwiwa da Najeriya ta hanyar samar da sababbin hanyoyin kuɗi da za su taimaka wajen saurin bunƙasar tattalin arziki.
A nata jawabin, Anna Bjerde ta ce Najeriya ta zama abin misali a duniya wajen tattauna sauye-sauyen tattalin arziki da sakamakonsu.
Ta ce shugabanni, masu tsara manufofi da masu zuba jari a sassa daban-daban na duniya na yawan ambaton Najeriya a tattaunawarsu.
Ta ce:
“A cikin waɗannan shekaru biyu, sakamakon da aka samu abin yabawa ne ƙwarai."
Ta yaba wa Tinubu kan dagewa da ci gaba da aiwatar da gyare-gyaren duk da ƙalubale, tana mai cewa babu ja da baya a wannan tafiya.
Bjerde ta bayyana cewa Bankin Duniya na da tsare-tsaren samar da ayyukan yi a Najeriya, wanda ya yi daidai da burin Tinubu na cimma tattalin arzikin da ya kai Dala tiriliyan ɗaya.
Tsare-tsaren sun shafi ababen more rayuwa, noma, ƙananan kasuwanci, da ci gaban ɗan Adam.
Ta ƙara da cewa Bankin Duniya ya tanadi tallafin kuɗi na Dala biliyan 17 ga ɓangaren gwamnati, da kuma kusan Dala biliyan 5 duk shekara ta hannun IFC, domin ƙarfafa samar da ayyukan yi da bunƙasar kamfanoni masu zaman kansu.
Kudin da aka kashe kan tafiye-tafiyen Tinubu
A wani labarin, kun ji cewa an gano kudin da Fadar Shugaban Ƙasa ta Najeriya ta kashe ya kai aƙalla Naira biliyan 34.39 wajen canjin kuɗin waje domin tafiye-tafiye zuwa ƙasashen waje.
Wannan adadi ya fito ne daga bayanan da aka tattara daga GovSpend, wani dandali na bin diddigin kashe-kashen gwamnati da ƙungiyar BudgIT ke tattara wa a kan kashe kuɗin gwamnati.
Rahoton ya ƙunshi dukkannin mu’amalolin kuɗi da suka shafi Fadar Shugaban Ƙasa da jiragen Shugaban Ƙasa, Ofishin Shugaban Ma’aikata da kuma Uwargidan Shugaban Ƙasa, da mataimakansu.
Asali: Legit.ng


