A Rana Guda, 'Yan Bindiga Sun Kashe fiye da Mutane 50 a Wasu Jihohin Arewa 2

A Rana Guda, 'Yan Bindiga Sun Kashe fiye da Mutane 50 a Wasu Jihohin Arewa 2

  • Ana fargabar 'yan bindiga sun kashe fiye da mutane 20 a kauyen Doma dake jihar Katsina tare da kona gidaje da motoci a harin ramuwar gayya
  • A Jihar Kwara mutane fiye da 30 ne ake fargabar sun rasa rayukansu bayan mahara sun farmaki kauyukan Woro da Nuku a yammacin Talata
  • 'Yan majalisar yankin da harin ya shafa sun bukaci gwamnatin tarayya ta tura dakarun sojoji domin kakkabe yan bindiga dake addabar mutane

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Aƙalla mutane 50 ne ake fargabar sun mutu a ranar Talata sakamakon munanan hare-haren 'yan bindiga a jihohin Katsina da Kwara.

Maharan sun ƙaddamar da waɗannan hare-haren ne a ƙauyukan karkara, inda suka ƙona gidaje da motoci tare da tilasta wa mazauna yankunan tserewa.

'Yan bindiga sun kashe bayin Allah a Katsina da Kwara.
Gwamnan Kwara, Abdulrahman Abdulrazaq da Gwamnan Katsina, Malam Dikko Radda. Hoto: @RealAARahman, @dikko_radda
Source: Twitter

Wannan sabon tashin hankali ya zo ne a daidai lokacin da ake tunanin an samu ɗan sauƙi na zaman lafiya a wasu sassan arewacin ƙasar, in ji rahoton Punch.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun bankawa fadar mai martaba sarki wuta, sun kashe bayin Allah a Kwara

Kisan kiyashin 'yan bindiga a jihar Katsina

A Jihar Katsina, aƙalla mutane 20 ne suka riga mu gidan gaskiya lokacin da 'yan bindiga suka farmaki ƙauyen Doma dake karamar hukumar Faskari.

Shugaban ƙaramar hukumar Faskari, Surajo Aliyu, ya bayyana harin a matsayin "mafi muni" da aka taɓa samu a yankin cikin watanni biyar.

Surajo Aliyu ya bayyana cewa:

“Wannan harin na ramuwar gayya ne, kuma gaskiya yana da ban tsoro domin ba mu taɓa samun irinsa ba a kwanan nan.”

Ya ƙara da cewa duk da an sanar da jami'an tsaro, ba su iya isowa akan lokaci ba domin dakile kisan da aka yi wa mutane.

Hare-haren ramuwar gayya a Faskari

Yankin Faskari na ɗaya daga cikin wuraren da aka cimma yarjejeniyar zaman lafiya da 'yan bindiga kimanin watanni biyar da suka gabata a jihar.

Wannan yarjejeniya ta kawo ɗan sauƙi, amma wannan sabon harin ya nuna cewa har yanzu akwai sauran jan aiki wajen tabbatar da tsaro.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kashe mutane 10, sun kona gidaje a sabon harin da suka kai Kwara

An kwashe gawarwakin mamatan domin gudanar da jana'izarsu a safiyar yau Laraba a garin Tafoki kamar yadda shugaban ƙaramar hukumar ya tabbatar.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Katsina bai riga ya fitar da wata sanarwa a hukumance ba game da wannan lamarin.

'Yan bindiga sun ci gaba da kai hare hare Katsina duk da zaman sulhu da aka yi da su.
Wasu gungun 'yan bindiga da aka yi zaman sulhu da su a Katsina. Hoto: @ZagazOlaMakama
Source: Twitter

Tashe-tashen hankula a jihar Kwara

A ɗaya gefen kuma, fiye da mutane mutane 30 ne aka kashe a garuruwan Woro da Nuku dake ƙaramar hukumar Kaiama a Jihar Kwara, cewar rahoton Daily Trust.

Maharan, waɗanda ake zargin sun fito ne daga dajin Borgu dake maƙwabtaka da Jihar Neja, sun shigo garuruwan Kaiama ne da yamma.

Malam Ahmed Yinusa, wani mazaunin yankin Kaiama ya shaida wa manema labarai cewa:

"'Yan bindiga kusan 200 ne suka shigo garin, suka kashe mutane da dama. Rahotannin da muka samu na nuni da cewa an kashe fiye da mutum 10 kuma an kona gidaje."

An kona fadar sarki a Kwara

Tun da fari, mun ruwaito cewa, 'yan bindigar da suka kai hari karamar hukumar Kaimana, jihar Kwara sun bankawa fadar sarkin Woro, Alhaji Saliu Bio Umar wuta.

Kara karanta wannan

Dakarun sojoji sun nuna bajinta, sun hana 'yan bindiga sakewa a Sokoto

Wani mazaunin Kaiama, Malam Idris Mohammed ya ce akwai gawarwakin mutane shida a fadar sarkin kafin 'yan sanda su zo su kona ta kurmus.

'Yan majalisar yankin sun bukaci gwamnatin tarayya ta tura dakarun soji na musamman domin kakkabe yan bindiga dake addabar Kaiama.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com