Bayan Shigar Abba APC, Kwankwaso Ya Ziyarci Babban Sanatan PDP har Gida
- Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya kai ziyara ta musamman ga Sanata Henry Seriake Dickson domin miƙa ta’aziyya kan rasuwar E-Lawrenzi
- Ziyarar ta biyo bayan dawowar Sanata Dickson daga Jihar Bayelsa ne bayan kammala jana’izar marigayi mataimakin gwamnan jihar
- Sanata Dickson ya yaba wa Rabiu Musa Kwankwaso bisa taya shi takaicin rasa mataimakin gwamnan, ya ce ya so zuwa jana'izar da kansa
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya kai ziyarar ta’aziyya ga Sanata Henry Seriake Dickson domin jajanta masa bisa rasuwar mataimakin gwamnan Bayelsa, Dr Lawrence Ewhrudjakpo.
Kwankwaso ya gana da Sanata Dickson ne a Abuja bayan kammala jana'izar Dr Lawrence Ewhrudjakpo da ake kira da E-Lawrenzi a jihar Bayelsa.

Source: Twitter
Sanata Dickson ne ya bayyana hakan ta shafinsa na X, inda ya ce ziyarar ta gudana ne bayan dawowarsa Abuja daga Bayelsa, inda ya halarci jerin shirye-shiryen jana’izar da aka gudanar.
Kwankwaso ya gana da Sanata Dickson
A cewar Sanata Dickson, Kwankwaso ya riga ya kira shi tun farko yana nuna sha’awar halartar jana’izar marigayin, amma wasu dalilai da suka taso a ƙarshe suka hana shi yin hakan.
Sai dai bayan samun labarin cewa Sanata Dickson ya dawo Abuja, Kwankwaso ya ga dacewar kai ziyara kai tsaye domin miƙa ta’aziyya ga 'yan uwa da abokan arziki.
Dickson ya ce ya tarbi Kwankwaso tare da tawagarsa cikin mutuntawa, inda suka yi addu’a tare domin Allah Ya jikansa da rahama, Ya ba iyalansa haƙuri, musamman matar da ya bari.
Maganar Dickson game da jana’izar
Tun da farko, Sanata Henry Seriake Dickson ya bayyana cewa tun ranar Laraba, 29, Janairun 2026, suna Jihar Bayelsa domin halartar jana’izar Dr. Lawrence Ewhrudjakpo.
Ya ce ya halarci ranar yabon da aka shirya domin girmama marigayin, tare da zaman bankwana da aka gudanar washegari, Alhamis. A wannan rana kuma, da yamma, ya halarci taron addu’ar dare.

Kara karanta wannan
Bayan Abba, Kwankwaso ya shiga tattaunawa da APC kan sauya sheka? Gaskiya ta fito

Source: Twitter
A ranar Juma’a, Dickson ya ce ya halarci jana’izar da aka gudanar a Ofoni, mahaifar marigayin, inda tare da iyalai da malaman addini suka birne shi kamar yadda addinin Kirista ya tanada.
Tasirin rayuwar marigayin a Najeriya
A jawabin da ya gabatar yayin jana’izar, Sanata Dickson ya ce lokacin jimamin ya bai wa mutane dama su fahimci girman gudummawar da marigayin ya bayar a rayuwarsa.
Ya ce duk da cewa wasu kaɗan ne suka san irin tasirin da ya yi a baya, yanzu kuwa al’ummar Bayelsa da ma Najeriya baki ɗaya sun fahimci rawar da ya taka a fannoni daban-daban.
Wasu kwamishinonin Kano sun bi Kwankwaso
A wani labarin, mun kawo muku cewa wasu kwamishinonin Kano biyar sun tsaya tare da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso a jam'iyyar NNPP.
Hakan na zuwa ne bayan gwamna Abba Kabir Yusuf ya raba hanya da Kwankwaso ya hada kai da Abdullahi Ganduje a jam'iyyar APC.
Kwamishinonin da suka yi murabus a gwamnatin Abba Kabir Yusuf sun hada da Dr Yusuf Ibrahim Kofarmata da Mustapha Rabiu Kwankwaso.
Asali: Legit.ng
