'Yan Bindiga Sun Bankawa Fadar Mai Martaba Sarki Wuta, Sun Kashe Bayin Allah a Kwara
- 'Yan bindiga kusan 200 sun kai wani mummunan hari a kauyen Woro dake jihar Kwara inda ake zargin sun hallaka fiye da mutane 35
- Maharan sun banka wa fadar Sarkin Woro wuta tare da shagunan dake kusa yayin da har yanzu ba a san inda sarkin ya shiga ba
- 'Yan majalisar yankin sun bukaci gwamnatin tarayya ta tura dakarun soji na musamman domin kakkabe yan bindiga dake addabar Kaiama
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Kwara - Wani mummunan hari da 'yan bindiga suka kai kauyen Woro dake karamar hukumar Kaiama a Jihar Kwara ya yi sanadiyar mutuwar mutane da dama a yammacin ranar Talata.
Maharan, wadanda yawansu ya kai kusan 200, sun shigo garin ne da misalin karfe 6:00 na yamma inda suka rika harbi kan mai uwa da wabi na tsawon sa'a guda.

Kara karanta wannan
'Yan bindiga sun kashe mutane 10, sun kona gidaje a sabon harin da suka kai Kwara

Source: Getty Images
Mazauna yankin sun bayyana cewa rashin kyawun hanya ya hana jami'an tsaro isa wurin akan lokaci domin dakile harin da ake kaiwa, in ji rahoton Daily Trust.
An cinnawa fadar sarki wuta a Kwara
Wani abin tashin hankali da ya faru shi ne yadda maharan suka banka wa fadar Sarkin Woro, Alhaji Saliu Bio Umar, wuta, ta kone kurmus.
Mallam Idris Mohammed ya bayyana cewa an ga gawarwakin mutane shida a harabar fadar kafin maharan su kona ginin fadar gaba daya.
Duk da cewa an tabbatar sarkin baya cikin fadar lokacin da harin ya afku, amma har yanzu ba a san inda yake ba sakamakon rudanin da ya biyo baya.
Baya ga fadar sarkin, 'yan bindigan sun kona shaguna da gidaje masu yawa, lamarin da ya janyo asarar dukiya ta miliyoyin Naira.
Rahotanni kan yawan wadanda suka mutu
Duk da cewa rahotannin farko sun nuna mutum 10 aka kashe, sababbin bayanai daga wakilan yankin sun nuna adadin ya fi haka yawa.
'Dan majalisar jiha mai wakiltar Gwanabe/Gweria/Bani/Adena, karamar hukumar Kaiama, Hon. Sa'idu Baba Ahmed, ya shaida wa manema labarai cewa an gano gawawwaki tsakanin 35 zuwa 45.
Hon. Sa'idu Baba Ahmed ya ce:
"An shaida mana cewa an kirga gawawwakin mutum 35 zuwa 45 duk da cewa ba mu tabbatar da duka ba tukunna."

Source: Original
Kiran gaggawa ga gwamnatin tarayya
Shi ma dan majalisa Hon. Halidu Danbaba, mai wakiltar Kaiama/Kemanji/Wajibe a majalisar jihar, ya yi kira ga gwamnatin jiha da ta tarayya da su gaggauta tura dakarun soji na musamman zuwa Kaiama.
A zantawarsa da BBC Hausa, dan majalisar ya bayyana cewa yankin yana bukatar irin farmakin da aka kai wa 'yan bindiga a kudancin Kwara domin tabbatar da tsaron makarantu.
A cewarsa, barazanar 'yan bindiga tana neman durkusar da harkar ilimi da kasuwanci a dukkan kauyukan dake makwabtaka da dajin na Kaiama.
Wannan harin na zuwa ne kwanaki kadan bayan 'yan bindiga sun kaddamar da makamancin sa a kauyen Nuku dake yankin.
Mutane sun tsere daga gidajensu
A wani labari, mun ruwaito cewa, fiye da mutane 6,000 ne suka tsere daga gidajensu a jihar Gombe sakamakon hare-haren 'yan bindiga da suka lakume rayuka da dukiya.
Hare-haren sun shafi Garin Galadima da wasu kauyuka dake karkashin karamar hukumar Akko, inda jama'a suka yi hijira domin tsira da rayukansu.
Hukumomi sun fara tantance wadanda hare-haren suka shafa a masarautar Pindiga domin samar musu da abinci da matsugunan wucin gadi.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

