Tambuwal Ya Shiga Uku, Gwamnatin Sokoto Ta Taso Shi a gaba kan ‘Badakalar’ da N117bn

Tambuwal Ya Shiga Uku, Gwamnatin Sokoto Ta Taso Shi a gaba kan ‘Badakalar’ da N117bn

  • Kwamitin bincike a Sokoto ya zargi gwamnatin tsohon gwamna Aminu Waziri Tambuwal da almundahanar fiye da ₦117bn
  • Rahoton ya nuna karya dokokin saye da sayarwa, cin zarafin ofis da gazawar wurin bin ka’idojin kudade a lokacin mulkinsa
  • Gwamna Ahmed Aliyu ya ce za a kafa kwamiti na musamman domin daukar mataki cikin adalci, yana jaddada cewa binciken ba siyasa ba ne

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Sokoto - Gwamnatin Jihar Sokoto ta karɓi rahoton wani kwamitin bincike da ya zargi cewa an yi almundahanar fiye da Naira biliyan 117.

Ana zargin badakalar a lokacin mulkin tsohon gwamna, Aminu Waziri Tambuwal, na tsawon shekaru takwas da ya yi.

Gwamnatin Sokoto na zargin Tambuwal da badakala a mulkinsa
Tsohon gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal. Aminu Waziri Tambuwal Media Team.
Source: Facebook

Rahoton da ke zargin Tambuwal da badakala

An mika rahoton ne a hukumance ga Gwamna Ahmed Aliyu Sokoto a fadar gwamnati, lamarin da ya kara zafafa muhawara kan gaskiya, sauye-sauyen mulki da yaki da cin hanci a Najeriya, cewar Vanguard.

Kara karanta wannan

Malami ya sanar da kotu hanyoyin da ya samu kudadensa a shari'arsa da EFCC

Shugaban kwamitin, Mai Shari’a Mu’azu Abdulkadir Pindiga (mai ritaya), ya bayyana cewa an kafa kwamitin ne domin binciken ayyukan gwamnatin da ta gabata ta hanyar takardu ingantattu da shaidun rantsuwa, bisa tanadin kundin tsarin mulki.

Ya ce binciken ya gano manyan kura-kurai na kudi da suka haura ₦117bn, sakamakon rashin bin dokokin sayen kaya, raunin kulawa da kudi da kuma cin zarafin ikon ofishin gwamnati.

A cewarsa, rahoton ya kasu kashi biyar da suka hada da tarihin binciken, hujjojin da aka karba, cikakkun bayanan sakamakon bincike, shawarwari, da kuma takaitaccen kammala aiki domin jagorantar matakan gwamnati.

Tambuwal na tsaka mai wuya kan zargin badakalar N117bn
Tsohon gwamna a Sokoto, Sanata Aminu Waziri Tambuwal da Gwamna Ahmed Aliyu. Hoto: Aminu Waziri Tambuwal Media Team, Sokoto State Government.
Source: Facebook

Tambuwal: Abubuwan da kwamitin ya duba

Mai Shari'a Pindiga ya ce kwamitin ya duba kwangiloli, takardun kudi da bayanan asusu, tare da sauraron shaidu daga ma’aikatu, hukumomi da sauran masu ruwa da tsaki da suka shafi gwamnatin da ake bincike.

Ya yaba wa mambobin kwamitin bisa jajircewa, kwarewa da gaskiya, yana mai cewa sun gudanar da aikinsu ba tare da tsoro ko son zuciya ba.

Ya kuma gode wa jama’a da hukumomin da suka bayar da hadin kai, yana mai cewa gudummawarsu ta taimaka wajen samar da rahoto mai amfani ga makomar Jihar Sokoto, cewar Daily Post.

Kara karanta wannan

Zaben 2027: An bukaci Shugaba Tinubu ya kori ministoci 2 kan wasu zarge zarge

Da yake karɓar rahoton, Gwamna Ahmed Aliyu ya gode wa kwamitin bisa sadaukarwa da amana wajen aiwatar da wannan aiki mai sarkakiya.

Gwamnan ya jaddada cewa kafa kwamitin ba domin bita da kullin siyasa ba ne, illa cika nauyin da kundin tsarin mulki ya dora wa gwamnati.

Ya ce za a kafa wani kwamitin domin duba rahoton tare da daukar matakai bisa gaskiya da adalci ga duk wanda aka samu da laifi.

Tambuwal ya gano matsalar zaben Najeriya

Kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal ya yi maganganu kan tsarin zabe a Najeriya da ke da wahalar sha'ani.

Aminu Tambuwal ya bayyana cewa akwai tarin matsaloli da kura-kurai wajen gudanar da zabubbuka a kasar nan wanda ya ke jawo matsaloli.

Tsohon shugaban majalisar wakilai ya kuma koka da cewa jam'iyyun siyasa ba su da wata tsayayyar akida da suke amfani da ita.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.