Zargin Kisan Kiristoci: Dan Majalisar Amurka Ya Gana da Gwamnan Plateau, an Ji Abin da Suka Tattauna
- 'Dan majalisar Amurka mai yada zargin kisan kare dangi ga Kiristoci a Najeriya, ya gana da Gwamnan jihar Plateau, Caleb Mutfwang
- Riley Moore ya bayyana muhimmancin aiki tare tsakanin Najeriya da Amurka domin kare rayukan Kiristocin da ake zargin ana muzgunawa
- Ganawar tasu dai na zuwa ne yayin da Najeriya da Amurka suka yi hadin gwiwa domin yaki da ta'addanci a kasar nan
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Kasar Amurka - Wani dan majalisar wakilan Amurka, Riley Moore, ya sake jaddada kudirinsa na hada kai da gwamnatin Najeriya domin magance matsalolin rashin tsaro da kuma tsananta wa Kiristoci, musamman a yankin Arewa ta Tsakiya.
Riley Moore ya bayyana hakan ne bayan wata ganawa da ya yi da Gwamnan jihar Plateau, Caleb Mutfwang.

Source: Twitter
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Riley Moore ya wallafa a shafinsa na X a ranar Talata, 3 ga watan Fabrairun 2026.
Me Riley Moore ya tattauna da Mutfwang?
Riley Moore da Gwamna Mutfwang sun tattauna hanyoyin kara zurfafa hadin gwiwa tsakanin kasashen Amurka da Najeriya.
'Dan majalisar na Amurka ya jaddada muhimmancin tattaunawa kai tsaye da manyan shugabanni a jihohi.
“Abin girmamawa ne a gare ni na gana da Gwamnan jihar Plateau a Najeriya, Caleb Mutfwang, jiya."
- Gwamna Caleb Mutfwang
'Dan majalisa da gwamna sun tattauna mai ma'ana
Ya bayyana tattaunawar a matsayin mai ma’ana kuma mai hangen nesa, inda ya ce an mayar da hankali ne kan karfafa hadin kai tsakanin kasashen biyu.
Hakazalika dan majalisar ya jaddada bukatar karfafa dangantakar diflomasiyya, tsaro da tattalin arziki.
"Mun yi tattaunawa mai amfani da armashi kan kara dankon zumunci tsakanin kasashenmu biyu."
- Riley Moore
Amurka na son tallafa wa Najeriya
Riley Moore ya kuma sake nanata kudirin Amurka na tallafa wa Najeriya wajen magance manyan kalubalen tsaro da ke addabar kasar.
'Dan majalisar ya nuna damuwa ta musamman ga al’umma masu rauni a yankin Arewa ta Najeriya na Najeriya.

Kara karanta wannan
Wasu kwamishinoni sun rikita gwamnatin Kano bayan komawar Abba APC? Gaskiya ta fito
"Ina nan daram wajen aiki tare da gwamnatin Najeriya cikin hadin kai da fahimta domin magance wadannan matsalolin tsaro da tattalin arziki, musamman muzgunawar ’yan’uwanmu Kiristoci ke fuskanta."
"Allah Ya yi maka albarka, Gwamna, kan abin da kake yi wajen kare Kiristoci da sauran al’umma masu rauni a Arewa ta Tsakiya na Najeriya."
- Riley Moore

Source: Facebook
Amurka da Najeriya sun yi hadin gwiwa
Wannan jaddadawar ta biyo bayan kaddamar da kwamitin hadin gwiwa na Amurka da Najeriya, wanda gwamnatin tarayya ta bayyana a matsayin “babbar dama ta tarihi” domin dakile ta’addanci da kuma kawo karshen muzguna wa Kiristoci a Najeriya.
Tawagar gwamnatin tarayya, karkashin jagorancin Mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu, ta gana da wakilan Amurka a Abuja a yayin zaman farko na wannan kwamitin hadin gwiwa.
Sanata ya koka kan harin Amurka a Najeriya
A wani labarin kuma, kun ji cewa Sanata mai wakiltar Bauchi ta Tsakiya, Abdul Ningi, ya yi magana kan harin da Amurka ta kawo a Najeriya.
Abdul Ningi, ya soki hare-haren sama da Amurka ta kai tare da haɗin gwiwar sojojin Najeriya kan kungiyoyin ta’addanci a wasu sassan ƙasar, ciki har da jihar Sokoto.
Sanatan ya yi zargin cewa Shugaban kasa, Bola Tinubu ya gaza sanar da ’yan majalisa kafin da kuma bayan aiwatar da harin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
