Ana Shirin Zanga Zanga, Gwamnatin Tinubu Ta Rufe Bakin Matasan N Power
- Gwamnatin tarayya ta fito ta bayyana shirinta ga wadanda suka ci gajiyar shirin matasa na N-Power a Najeriya
- Ministan jin-kai, Dr. Bernard Doro ya ce za a biya su kudaden alawus din da suke bin gwamnati bayan kammala duba shirin
- Gwamnati ta ce tana sake fasalin shirin N-Power domin ya dore, tare da tsarin ficewa, bisa manufar Renewed Hope ta Bola Tinubu
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Gwamnatin tarayya ta tabbatar wa masu cin gajiyar shirin N-Power cewa za a biya su dukkan alawus din da suke bi.
Wannan tabbaci na zuwa ne yayin da ake duba shirin gaba daya domin tabbatar da dorewar shirin duba da amfaninsa ga matasa.

Source: Twitter
Hakan na cikin wani faifan bidiyo da shafin ma'akatar jin kai darage talauci ta wallafa a Facebook wanda minista Bernard M Doro ya ba da tabbacin kawo sauyi.

Kara karanta wannan
A karshe, an ji abin da ya taimaka aka gano shirin yi wa Tinubu juyin mulki a Najeriya
Gwamnatin Tinubu ta shirya biyan matasan N-Power
Hakan ya zo ne sa’o’i kadan kafin masu cin gajiyar N-Power su gudanar da zanga-zangar kasa baki daya da suka shirya yi a ranar 4 ga Fabrairu, 2026.
Ma’aikatar Harkokin Jin-Kai da Rage Talauci ta Tarayya, karkashin jagorancin Dr. Bernard M. Doro, ta ce ana aiki tukuru domin warware matsalolin da ke addabar shirin.
Ministan ya bayyana cewa duk masu cin gajiyar N-Power da aka tantance kuma aka tabbatar suna bin gwamnati bashi, za su karbi kudinsu ba tare da tangarda ba.
Ya ce ma’aikatar tana aiki tare da Hukumar Shirye-shiryen Tallafin Jama’a ta Kasa (NSIPA) domin duba shirin da kuma gyara gibin da ke hana shi aiki yadda ya kamata.
Dr Doro ya ce ya fahimci damuwar da masu cin gajiyar shirin ke fuskanta, tare da tabbatar musu cewa an saurare su.
Ya kara da cewa ya gana da wakilan masu cin gajiyar N-Power kai tsaye, inda suka tattauna matsalolin da ke addabar shirin dalla-dalla.

Source: Facebook
Fasalin da ake son mayar da N-Power
Dr. Doro ya ce duk wadanda aka tabbatar suna da matsala za a biya su kudinsu nan ba da jimawa ba, yayin da ake kammala shirye-shiryen biyan alawus din.
Ministan ya kuma jaddada kudirin gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na sake fasalin shirin N-Power domin ya zama mai dorewa.
Ya ce za a tsara shirin da tsarin ficewa yadda zai dace da manufar Renewed Hope, domin taimaka wa matasa su samu dogon mafita daga talauci.
Ya ce:
“Mun kuduri aniyar sake fasalin shirin domin ya zama mai dorewa, tare da ingantaccen tsari yayin ficewarsu, bisa hangen nesan Shugaban Kasa.”
Gwamnati ta ce ana kammala shirye-shirye domin fara biyan kudaden alawus ga dukkan masu cin gajiyar N-Power da suka cancanta a fadin Najeriya.
Alkawuran gwamnatin Tinubu ga matasan N-Power
A baya, an ji cewa Gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta bayyana shirinta na biyan haƙƙokin ƴan N-Power da aka riƙe masu tun 2022.
Mataimakin shugaban Majajalisar Dattawa, Sanata Barau Jibrin ne ya sanar da hakan bayan wani taron sasanci da ya jagoranta a Abuja.
Ministan harkokin jin kai ya ce sun tarar da an sa kuɗin da za a biya ƴan N-Power a kasafin 2022 da na 2023 amma kuma ba a fitar da kuɗin ba.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

