Wata Sabuwa: Lauya Ya Kawo Rudani game da Wadanda Suka Shirya Yi Wa Tinubu Juyin Mulki

Wata Sabuwa: Lauya Ya Kawo Rudani game da Wadanda Suka Shirya Yi Wa Tinubu Juyin Mulki

  • Babban lauya a Najeriya, Femi Falana (SAN) ya kawo rudani game da shirin gurfanar da sojojin da ake zargi da hannu a yunkurin juyin mulki
  • Falana, lauya mai fafutukar kare hakkin dan adam ya ce bai kamata a gurfanar da wadanda ake zargi a gaban kotun gidan soja ba
  • Ya ce a tanadin doka, an kirkiri kotun sojoji ne domin ladabtarwa amma wannan laifi da ake zargin jami'an da su ya shafi kasa ne baki daya

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Babban Lauya a Najeriya kuma mai fafutukar kare hakkin dan adam, Femi Falana, SAN, ya tsoma baki kan batun sojojin da ake zargi da hannu a kitsa juyin mulki.

Falana ya ya bayyana cewa ba za a iya gurfanar da sojojin da ake zargi da shirya juyin mulki kan gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu a gaban kotun soji ba a tsarin dimokuraɗiyyar Najeriya.

Kara karanta wannan

A karshe, an ji abin da ya taimaka aka gano shirin yi wa Tinubu juyin mulki a Najeriya

Femi Falana.
Fitaccen lauya mai fafutukar kare hakkin dan adam, Femi Falana, SAN Hoto: @Royalblogg
Source: Twitter

Ya bayyana hakan ne yayin wata hira da ya yi a tashar Channels tv, inda ya yi tsokaci kan ce-ce-ku-cen da ake yi game da irin tsarin da ya dace a bi wajen shari’ar yunkurin juyin mulki.

Juyin mulki: Femi Falana ya hango kuskure

Falana ya jaddada cewa dole ne a gurfanar da irin waɗannan mutanen a gaban kotunan farar hula, kamar yadda Kundin Tsarin Mulkin Kasa ya tanada.

A cewar Falana, Najeriya ba a ƙarƙashin mulkin soja take ba, kuma kundin tsarin mulki ya fayyace yadda za a gurfanar da duk wanda ya aikata laifi a kan zababbiyar gwamnati.

“Muna ƙarƙashin gwamnatin dimokuraɗiyya ne, kuma bisa tanadin kundin tsarin mulki, dole ne a kai su gaban babbar kotu."
“A doka ba za a kai sojojin da ake zargi gaban kotun soji ba, domin ba yunkurin kifar da mulkin soja suke yi ba. Yunƙuri ne na kifar da gwamnati zaɓaɓɓiya, halastacciyar gwamnati, da kuma rusa tsarin mulki.

Kara karanta wannan

Juyin mulki: Yadda aka tsara harbe ministan tsaro, Janar Christopher Musa

Falana ya kaffa hujja da kundin tsarin mulki

Lauyan kare hakkin ɗan adam ɗin ya bayyana cewa kotun soji an tanade ta ne musamman don ladabtarwa da laifuffukan ladabi da suka shafi tsarin aikin soja kawai.

“Amma idan laifin da ake zargi ya kai matsayin cin amanar ƙasa ko yunƙurin kifar da gwamnatin da aka zaba ta hanyar dimokuraɗiyya, to wannan laifi ya wuce batun ladabtarwar soji, ya koma babban laifi na kundin tsarin mulkin ƙasa,” in ji shi.
Janar Oluyede.
Babban hafsan tsaron Najeriya, Janar Olufemi Oluyede tare da jami'an sojoji Hoto: @DHQNigeria
Source: Facebook

Falana ya ce gurfanar da irin waɗannan masu laifuffuka a gaban kotun sojoji ya sabawa ƙa’idojin dimokuraɗiyya kuma zai iya raunana martabar kundin tsarin mulki, cewar rahoton Vanguard.

“Cin amanar ƙasa da laifin yunƙurin cin amanar ƙasa laifuffuka ne da doka ta fayyace su karara, kuma suna ƙarƙashin hurumin kotunan farar hula,” in ji Falana.

Yadda aka gano shirin juyin mulki a Najeriya

A wani labarin, kun ji cewa Janar Christopher Musa ya yi bayanin yadda jami'an tsaro suka hada kai, har suka gano shirin da aka yi na kifar da gwamnatin Bola Tinubu.

Kara karanta wannan

Juyin mulki: Ministan tsaro ya faɗi hukuncin da ke jiran sojojin, ya yi albishir ga iyalansu

Ministan na tsaro wani Kanal da ya ji haushin faduwa jarabawar karin girma zuwa mukamin Birgediya Janar, shi ne ya kaddamar da shirin juyin mulkin tare da jawo wasu mutane ciki.

Binciken da aka yi, ya nuna cewa an fara tsara yunkurin juyin mulkin tun kafin zuwan gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu a 2023.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262