Mutane Sun bada Mamaki a Jana'izar Sheikh Rigi Rigi, An Ji Sunaye 3 da Ake Kiransa da Su

Mutane Sun bada Mamaki a Jana'izar Sheikh Rigi Rigi, An Ji Sunaye 3 da Ake Kiransa da Su

  • An gudanar da sallar jana'izar tare da birne Sheikh Khalifa Usman Idris, wanda aka fi sani da Sheikh Rigi-Rigi a Zaria, jihar Kaduna
  • Daruruwan mutane daga ciki da wajen Kaduna ne suka halarci jana'izar malamin, wacce aka gudanar a gidansa ranar Litinin
  • A daren ranar Lahadi ne malamin ya rasu a asibitin 44 da ke cikin garin Kaduna bayan shafe tsawon lokaci yana jinya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Zaria, Kaduna - Daruruwan musulmi sun halarci jana'izar fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Khalifa Usman Idris, wanda aka fi sani da Sheikh Rigi-Rigi a Zaria, jihar Kaduna.

Kara karanta wannan

Zargin lalata da matar aure: Magidanci ya sassara wani mutum da adda har lahira

Rahotanni sun nuna cewa yawan jama'a da aka tara a jana'izar malamin ya ba mutane mamaki, a ranar Litinin, 2 ga watan Fabrairun 2026.

Sheikh Rigi Rigi.
Daruruwan mutane a wurin jana'izar Sheikh Khalifa Usman Kusfa Hoto: Sheikh Hafram Khaleel
Source: Facebook

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa Sheikh Rigi-Rigi ya rasu ne a ranar 1 ga Fabrairu, 2026, yana da shekara 57 a duniya, bayan fama da doguwar rashin lafiya.

Ɗansa uwansa, Malam Abubakar Danyaro, ya bayyana cewa malamin ya rasu ne a daren Lahadi a wani asibiti mai zaman kansa da ke birnin Kaduna.

An yi jana'izar Sheikh Rigi-Rigi

An gudanar da sallar jana’izar marigayi Sheikh Rigi-Rigi ne a gidansa da ke unguwar Kusfa, cikin birnin Zariya, da yammacin ranar Litinin.

Sallar ta samu halartar manyan malamai, shugabannin al’umma da masoyansa daga ciki da wajen jihar Kaduna. Marigayin ya bar mata hudu, ’ya’ya 37 da jikoki da dama.

Kara karanta wannan

An ji yadda Sheikh Rigi Rigi ya rasu a gadon asibiti da wasiyyar da ya bar wa Musulmai

Sheikh Rigi-Rigi ya shahara sosai wajen wa’azi mai ɗauke da barkwanci da nishadi, inda bidiyoyin karatuttukansa ke yawo sosai a kafafen sada zumunta tare da samun karɓuwa a tsakanin al’umma.

Yadda Sheikh Rigi-Rigi ya shahara

Ya yi fice musamman wajen koyar da falalar waliyyai da muridan Sheikh Ibrahim Inyass, tare da iya bayyana manyan batutuwan addini cikin salo mai sauƙi, ban sha’awa da fahimta.

Haɗa barkwanci da hikima a wa’azi na daga cikin abubuwan da suka sa ya samu dimbin mabiya, musamman daga cikkn matasan Musulmai a fadin ƙasar nan

Baya ga mabiyansa a cikin al’ummar Musulmi, Sheikh Rigi-Rigi ya kuma yi fice sosai a kafafen sada zumunta kamar TikTok da sauran makamantansu.

Sheikh Rigi Rigi.
Babban malamin darikar Tijjaniyya, Sheikh Khalifa Usman Rigi-Rigi Hoto: Sheikh Hafram Khaleel
Source: Facebook

Sunaye 3 da aka fi kiran malamin da su

Masoyansa suna yi masa laƙabi da sunaye daban-daban kamar “Rigirigi”, “Rugum” da “Attalili Attaghazuti”, laƙabban da ke nuna jarumtaka, kwarin gwiwa da faɗin gaskiya ba tare da tsoro ba.

Kara karanta wannan

An sanya lokacin jana'izar Sheikh Usman Rigi Rigi, 'masoyin Annabi ya rasu'

Daga cikin manyan abubuwan da ya bari a tarihi akwai bunƙasa ilimin Musulunci, aikin Da’awah na Darikar Tijjaniyya, da yaɗa koyarwar addini, kamar yadda Leadership ta kawo.

Wasiyyar da Sheikh Rigi-rigi ya bari

A wani labarin, kun ji cewa iyalan marigayi Sheikh Usman Rigi-Rigi sun bayyana wasiyyar da malamin yake yawan maimaita wa kafin Allah ya masa rasuwa.

Daya daga cikin matakn malamin ta tabbatar da cewa Sheikh Rigi-Rigi ya dade yana jinya kafin Allah SWT ya karbi ransa a daren Lahadi, 1 ga watan Fabrairu, 2026.

Ta bayyana cewa Shehu yana da masoya da yawa a cikin Tijjaniya da ma wadanda ba musulmi ba, ta roki kowa da ya yi hakuri domin mutuwa tana kan kowa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262