Za a Dauke Wuta na Kwana 4 a Najeriya, TCN Ya Fadi Jihar da Za Ta Shiga Duhu
- Hukumar TCN za ta gudanar da aikin gyaran wuta a tashar Ife da Ondo daga Litinin zuwa Alhamis domin inganta rarraba lantarki a yankin
- Yankunan Okitipupa da garin Ondo za su shiga duhu tsakanin karfe 8:00 na safe zuwa karfe 3:00 na yammacin kowace rana
- Wannan aikin gyaran na daya daga cikin kokarin gwamnati na karfafa rumbun adana wutar lantarki na kasa domin samar da tsayayyiyar wuta
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Hukumar rarraba wutar lantarki ta ƙasa (TCN) ta sanar da shirin gudanar da aikin gyara a tashoshin ta na Ife da Ondo.
Wannan aiki zai gudana ne daga ranar Litinin, 2 ga Fabrairu, zuwa ranar Alhamis, 5 ga watan Fabrairu, 2026, a cewar hukumar.

Source: UGC
TCN za ta yi gyaran wutar lantarki
Hukumar ta fitar da sanarwar ne a ranar Litinin, 2 ga Fabrairu, 2025 ta hannun shugaban sashenta na hulda da jama'a, Ndidi Mbah, cewar rahoton Punch.
Za a riƙa gudanar da aikin gyaran ne kowace rana tsakanin ƙarfe 8:00 na safe zuwa ƙarfe 3:00 na yamma da nufin inganta ƙarfin rarraba wutar lantarki da kuma tabbatar da ingancin kayan aiki a shiyyar.
A cikin sanarwar, TCN ta ce:
“Manufar gyaran ita ce inganta amincin rarraba wutar lantarki a wannan yankin baki ɗaya.”
Abubuwan da gyaran zai kunsa
Yayin aikin, ƴan kwangilar TCN za su cire tsohuwar na'urar da ake kira wave trap a turance su maye gurbin ta da sabuwa a tashar Ife/Ondo.
Har ila yau, za a sauya wasu tsofaffin turakun wuta da ke daukar layi daya na wutar a hanyar wuta ta Ife/Ondo a sanya sababin masu daukar layi biyu na wutar .
Hakan, wannan gyaran zai ba wa kamfanin rarraba wuta na Benin (BEDC) damar samun ƙarin ƙarfin rarraba wuta ga masu amfani da ita.
Yankunan da za su shiga cikin duhu
Sakamakon wannan aiki, za a dauke wutar lantarki a garuruwan Okitipupa, Ondo, da dukkan yankunan dake maƙwabtaka da su.
TCN ta bayyana cewa:
“Wannan aiki zai hana kamfanin BEDC kai wuta ga abokan cinikinsu dake Okitipupa da Ondo a tsawon kwanakin.”
Hukumar ta ba da haƙuri kan rashin jin daɗin da wannan ɗaukewar wuta za ta haddasa wa mazauna waɗannan yankuna.

Source: Facebook
Aikin gyaran wuta a Katampe, Abuja
Wannan sanarwa na zuwa ne kwanaki biyu bayan TCN ta kammala makamancin wannan aiki a tashar Katampe dake birnin Abuja.
An gudanar da aikin Abuja ne a ranar Asabar, 31 ga Janairu, inda aka sanya sabuwar na'urar rarraba wuta mai karfin 300MVA, cewar sanarwar da aka wallafa a shafin TCN na X.
Wannan ya shafi rarraba wuta a yankunan Jahi, Mpape, Bwari, Jabi, da Suleja sakamakon raguwar nauyin wuta da aka samu.
Wutar lantarkin Najeriya ta samu matsala
A wani labari, mun ruwaito cewa, tushen samar da wutar lantarki a Najeriya ya durkushe, lamarin da ya jefa 'yan kasa a cikin duhu ranar Juma'a, 23 ga watan Janairu, 2026.
Rahotanni sun nuna cewa zuwa karfe 1:00 na rana, babu wani kamfanin raba wuta da ya mu ko digo daga babban tushen samar da wuta na kasa.
Wannan dai shi ne karo na farko da aka samu irin wannan matsala a 2026, duk da dai an sha fama da lalacewar wuta a shekarar da ta gabata.
Asali: Legit.ng

