Harin Yelwata: Ministan Tinubu Ya Sa Kayan Lauyoyi, Ya Jagoranci Gurfanar da Mutane 9 a Kotu

Harin Yelwata: Ministan Tinubu Ya Sa Kayan Lauyoyi, Ya Jagoranci Gurfanar da Mutane 9 a Kotu

  • Ministan Shari'a, Lateef Fagbemi ya shiga tawagar lauyoyin gwamnatin tarayya wajen gurfanar da mutanen da ake zargi da kashe-kashen Yelwata
  • A watan Yuni, 2025 ne aka kai wani hari garin da ke jihar Benuwai, inda aka kashe mata, yara da magidanta sama da 150
  • Gwamnatin tarayya ta gurfanar da wadanda ake zargi da hannu a aikata wannan danyen aiki a gaban babbar kotun tarayya da ke Abuja

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Gwamnatin tarayya ta gurfanar da mutanen da aka kama bisa zargin hannu a kashe-kashen rashin imani da aka yi a jihar Benuwai da ke Arewacin Najeriya.

Antoni Janar na Tarayya (AGF) kuma Ministan Shari’a, Prince Lateef Fagbemi (SAN), shi ne ya jagorantar tawagar lauyoyin gwamnati wajen gurfanar da wadanda ake zargi su tara.

Fagbemi.
Antoni Janar na Tarayya kuma Ministan Shari'a, Lateef Fagbemi, SAN Hoto: @LateefFagbemi
Source: Twitter

An gurfanar da masu hannu a kisan Yelwata

Kara karanta wannan

Tofa: Gwamna ya rufe dukkan makarantu, ya sanya dokar zaman gida ta awanni 20

Jaridar Tribune Nigeria ta rahoto cewa Ministan ya jagoranci gurfanar da mutanen ne a yau Litinin kan zargin hannu a kisan gilla na mutane kusan 150 a Yelwata, wani gari a jihar Benuwai.

Rahotanni sun nuna cewa, ana zargin wadanda ake kara da kashe mutane sama da 150 a yankin Yelwata da ke Karamar Hukumar Guma a jihar Benuwai a ranar 13 ga watan Yuni, 2025.

Gwamnatin Tarayya ce ta gurfanar da su a gaban Mai shari’a Joyce Abdulmalik na Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja.

Gurfanar da wadanda ake zargin kan kisan na Benuwai ya zo ne bayan faffadan bincike da hadin gwiwa tsakanin hukumomin gwamnati.

Mutanen da ake zargi sun musanta a kotu

An karanta wa wadanda ake karan kunshin tuhume-tuhume guda 57 da aka yi wa gyaran, wadanda suka shafi kisan gillar da aka yi a Yelwata a jihar Benuwai a watan Yunin shekarar da ta gabata.

Wadanda ake kara sun hada da Ado Mohammed Dono, Mohammed Saidu, Alh Haruna Abdullahi, Yakubu Adamu, Mohammed Musa, Abubakar Adamu, Shaibu Ibrahim, Saleh Mohammed, da Bako Jibril.

Bayan gurfanar da su a kotun tarayya mai za a Abuja, duka mutanen sun bayyana cewa ba su da laifi dangane da tuhume-tuhumen da Gwamnatin Tarayya ke yi musu.

Kara karanta wannan

Ba rufa rufa: Sunayen mutum 40 da aka kama bisa shirin yi wa Tinubu juyin mulki

Babbar kotun tarayya.
'Yan sanda da ke aiki a harabar babbar kotun tarayya da ke Abuja Hoto: Federal High Court
Source: Getty Images

A wata sanarwa da ofishin Antomi Janar ya fitar a ranar Lahadi, ya tabbatar wa ’yan Najeriya cewa za a tabbatar da adalci a wannan lamari domin aika sako mai karfi ga makiya kasar nan, wadanda ke aikata barna a kowane irin salo, in ji Punch.

“Gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta himmatu wajen kare rayuka da dukiyoyin kowa kamar yadda kudin tsarin mulki ya tanada,” in ji Fagbemi.

Kotu ta kwace kadarorin Malami

A wani rahoton, kun ji cewa babbar kotun tarayya ta bayar da umarnin wucin gadi na ƙwace kadarori 57 da ake zargin suna da alaka da tsohon Antoni Janar na Tarayya (AGF), Abubakar Malami.

EFCC ce ta shigar da bukatar kwace kadarorin bisa zargin cewa Malami, tsohon ministan shari'a ya mallake su ta hanyar amfani da kudin haram.

Kwafin umarnin kotun da aka samu a ranar Laraba ya nuna cewa kadarorin da suka kunshi filaye da gine-ginen da abin ya shafa suna a Abuja, Kebbi, Kano da Kaduna.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262