Fitaccen Malamin Musulunci Sheikh Usman Kusfa Rigi Rigi Ya Rasu

Fitaccen Malamin Musulunci Sheikh Usman Kusfa Rigi Rigi Ya Rasu

  • Al’ummar Musulmi a Zariya da sassan Arewa sun shiga jimami bayan rasuwar fitaccen malamin Musulunci Sheikh Khalifa Usman Kusfa, wanda aka fi sani da Rigi-Rigi
  • An tabbatar da cewa za a gudanar da Sallar Jana’izarsa a yau Litinin da misalin ƙarfe 4:30 na yamma a Babban Filin Low-Cost da ke Zariya, bisa koyarwar addinin Islama
  • Sheikh Rigi-Rigi ya shahara wajen wa’azi kan ƙaramomin waliyyai da manyan malamai, tare da barin gagarumar tasiri, musamman a kafafen sada zumunta

Jihar Kaduna – Al’ummar Musulmi a Arewacin Najeriya sun shiga wani yanayi na alhini da jimami bayan rasuwar shahararren malamin Musulunci, Sheikh Khalifa Usman Kusfa, wanda aka fi sani da Sheikh Rigi-Rigi.

Rasuwar malamin ta girgiza al’ummar Zariya da kewayenta, inda malamai, dalibai da mabiya addini suka fara aika wa da sakonnin ta’aziyya da addu’o’i, suna roƙon Allah Ya ji kansa.

Sheikh Usman Kusfa Rigirigi
Marigayi Sheikh Usman Kusfa yayin wani wa'azi. Hoto: Sheikh Usman Kusfa Rigirigi
Source: Facebook

Rahoton Aminiya ya nuna cewa Sheikh Rigi-Rigi ya kasance daya daga cikin fitattun malaman Musulunci da suka shahara da salon wa’azi na musamman, wanda ya sa ya samu karbuwa a kafafen sada zumunta.

Kara karanta wannan

'Ba talauci ba ne,' Peter Obi ya fadi ainihin matsalar da ke addabar Najeriya

Sheikh Usman Rigi-Rigi ya yi jinya

Surikin marigayi malamin, Malama Abubakar Ɗanyaro, ya tabbatar da rasuwar Sheikh Rigi-Rigi ga manema labarai, inda ya bayyana cewa malamin ya rasu ne a wani asibiti da ke birnin Kaduna a daren Lahadi, 1 ga Fabrairun 2026.

Abubakar Ɗanyaro ya ce Sheikh Rigi-Rigi ya kwashe tsawon lokaci yana jinya, inda aka fara kwantar da shi a Asibitin Sojoji na 44 da ke Kaduna.

Daga bisani, saboda tsananin rashin lafiyar, aka mayar da shi wani asibiti mai zaman kansa a unguwar Barnawa, inda Allah Ya karɓi rayuwarsa da misalin ƙarfe 3:30 na dare.

Jana'izar Sheikh Rigi-Rigi a Zariya

Abubakar Ɗanyaro ya kara da cewa za a gudanar da sallar jana’izar marigayin a yau Litinin, 2 ga watan Janairun 2026 kamar yadda addinin Musulunci ya koyar.

Ya ce za a yi jana'izar bayan La’asar, inda za a yi addu’o’i a gidansa da ke unguwar Kusfa a Zariya, kafin daga bisani a kai shi makwancinsa na ƙarshe.

Kara karanta wannan

Makamai, motoci da aka bankado a shirin juyin mulki, an gano soja 1 a Amurka

Haka zalika, tashar kasar Turkiyya ta TRT Afrika Hausa ta tabbatar da mutuwar malamin a wani sako da ta wallafa a shafinta na Facebook.

Rayuwar Marigayi Sheikh Rigi-Rigi

Sheikh Usman Kusfa Rigi-Rigi ya yi fice wajen wa’azi da koyarwar addinin Musulunci, musamman a bangaren bayani kan ƙaramomin waliyyai da tarihin manyan malamai.

Salon koyarwarsa ya bambanta da na wasu malamai, lamarin da ya sa jama’a da dama ke sha’awar sauraron wa’azinsa musamman a kafafen sada zumunta.

Sheikh Usman Kusfa Rigirigi
Sheikh Usman Kusfa yana gabatar da wa'azi kafin rasuwarsa. Hoto: Sheikh Usman Kusfa Rigirigi
Source: Facebook

Malamin ya kasance kullum cikin fara'a, ba ya bari ran shi ya baci musamman a wurin karatu.

A shekarun baya-bayan nan, bidiyoyin wa’azin Sheikh Rigi-Rigi sun fara yaduwa sosai a kafofin sada zumunta, inda yake bayani kan ƙaramomin waliyyai da almajiran Sheikh Ibrahim Inyass, musamman waɗanda ba kasafai ake jin labarinsu ba.

Sheikh Albani ya yi kira ga Rarara

A wani labarin, kun ji cewa Sheikh Adam Muhammad Albani Gombe ya yi kira ga mawaki Dauda Kahutu Rarara kan taimakon masu wa'azi.

Albani ya bukaci Dauda Rarara ya taimakawa Baban Chinedu da Adam Ashaka da kayan wa'azi domin shiga kauyuka suna isar da sakon Musulunci.

Ya kara da cewa yana da labarin yadda Rarara ke taimakawa Baban Chinedu, amma watakila ba a taba masa irin wannan kira na musamman ba.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng