Katsina, Kano da Jihohi 16 da Amurka Ta Ce Suna da Hatsarin Gaske a Najeriya

Katsina, Kano da Jihohi 16 da Amurka Ta Ce Suna da Hatsarin Gaske a Najeriya

  • Amurka ta fitar da gargadin balaguro inda ta bukaci 'yan kasarta da su guji ziyartar jihohin Najeriya 18 saboda ayyukan 'yan ta'adda da masu garkuwa
  • Gargadin ya nuna cewa kungiyoyin 'yan ta'adda na kai hare-hare a wuraren taron jama'a kamar kasuwanni da otal-otal da kuma coci-coci da masallatai
  • Gwamnatin Amurka ta bayyana cewa 'yan bindiga suna bibiyar 'yan kasashen waje a Kano, Katsina da wasu jihohi don sace su, da nufin karbar kudin fansa

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Gwamnatin Amurka ta fitar da wani sabon gargaɗin balaguro inda take kira ga ƴan ƙasarta da su sake tunani kafin su ziyarci Najeriya saboda barazanar aikata laifuffuka, ta'addanci, tarzoma, garkuwa da mutane, da kuma rashin ingancin ayyukan lafiya.

Hukumomin ƙasar sun bayyana cewa dukkan sassan Najeriya na tattare da gagarumar kasadar tsaro, kodayake wasu jihohin sun fi sauran haɗari.

Kara karanta wannan

Sojoji sun yi lalata da mata, sun tatsi talakawa a Cross River? Gaskiya ta fito

Amurka ta gargadi 'yan kasarta kan ziyartar wasu jihohin Najeriya a 2026
Lt. Gen. Joshua Rudd, wani jagoran sojojin Amurka da Bello Turji, wani jagoran 'yan ta'adda a Najeriya. Hoto: Chip Somodevilla/Getty
Source: Getty Images

Jihohin da Amurka ta hana a ziyarta

A cikin gargaɗin da aka wallafa a shafin yanar gizo na Travel.State.Gov, Amurka ta lissafo jihohi daban-daban waɗanda ba a buƙatar ƴan ƙasarta su ziyarta:

  • Borno, Yobe, Kogi, da arewacin Adamawa saboda ta'addanci da garkuwa.
  • Bauchi, Gombe, Kaduna, Kano, Katsina, Sokoto, da Zamfara saboda garkuwa da mutane.
  • Abia, Anambra, Bayelsa, Delta, Enugu, Imo, da Rivers (ban da birnin Port Harcourt) saboda laifuffuka da ƙungiyoyin asiri masu rike da makami.

Wuraren da 'yan ta'adda suke farmaka

Gwamnatin Amurka ta bayyana cewa ƙungiyoyin 'yan ta'adda na ci gaba da ƙulla makirci da kai hare-hare a Najeriya, galibi suna haɗa kai da masu basu bayanai na cikin gida domin faɗaɗa ayyukansu.

Wuraren da suke kai wa hari sun haɗa da kasuwanni, otal-otal, gidajen abinci, makarantu, gine-ginen gwamnati, da kuma wuraren ibada kamar coci da masallatai.

A cewar gargaɗin:

Kara karanta wannan

Minista ya dauko da zafi, ya fara shirin garkame ma'aikatan Abuja a gidan yari

"Tarzoma da ƙungiyoyin asiri masu makami suna da tasiri a sassan Kudancin Najeriya, musamman a yankin Neja-Delta da Kudu maso Gabas.
Laifuffukan masu amfani da makami sun zama ruwan dare, waɗanda suka haɗa da fashi da makami, sace mutane don kuɗin fansa, da harin kwantan ɓauna a kan manyan hanyoyi."
Amurka ta ce jihohin Najeriya 18 na da matukar hatsari ga 'yan kasarta
Wasu sojojin kasar Amurka a bakin aiki. Hoto: Anderson White/Getty
Source: Getty Images

Barazana ga 'yan kasashen waje

Hukumomin Amurka sun ja kunnen cewa masu garkuwa da mutane suna kai hari ne ga waɗanda suke ganin suna da dukiya, ciki har da ƴan ƙasar Amurka da kuma waɗanda suke da shaidar ɗan ƙasa biyu dake kai ziya Najeriya.

Sanarwar gargaɗin ta jaddada cewa:

"Sace mutane don kuɗin fansa na faruwa akai-akai. Masu garkuwar suna tare mutane har a manyan hanyoyin dake haɗa jihohi."

Amurka ta buƙaci dukkan ƴan ƙasarta da su karanta dukkan bayanan gargaɗin kafin su yi tunanin kowane irin balaguro zuwa Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com