'Yan Bindiga Sun Tafka Sabuwar Ta'asa a Neja, Sun Kona Coci, Ofishin 'Yan Sanda

'Yan Bindiga Sun Tafka Sabuwar Ta'asa a Neja, Sun Kona Coci, Ofishin 'Yan Sanda

  • Wasu miyagun 'yan bindiga sun yi amfani da abubuwan fashewa wajen kona ofishin yan sanda da coci a garin Agwara dake jihar Niger
  • Akalla mutane biyar ne maharan suka yi awon gaba da su zuwa daji bayan sun fatattaki jami'an tsaro dake bakin aiki a wannan hari da suka kai
  • Rundunar yan sandan Neja ta tabbatar da cewa babu wanda ya rasa ransa a harin amma mazauna garin da dama sun tsere daga gidajensu

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Neja - Wasu miyagun 'yan bindiga sun kaddamar da wani mummunan hari a garin Agwara, hedkwatar karamar hukumar Agwara dake Jihar Niger.

A yayin wannan hari, an ce 'yan ta'addar sun kona ofishin yan sanda na yankin da kuma wani sashe na coci tare da sace akalla mutane biyar.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kai hare hare a Zamfara, an kashe bayin Allah

'Yan bindiga sun kai sabon hari Neja, sun sace mutane
Taswirar jihar Neja, inda 'yan bindiga suka kona coci da ofishin 'yan sanda. Hoto: Legit.ng
Source: Original

'Yan bindiga sun kona ofishin 'yan sanda

Wannan hari, wanda ya auku a daren ranar Lahadi, ya sake jefa mazauna yankin cikin fargaba, musamman ganin cewa wannan ne yankin da aka taba sace dalibai da malamai kusan 300 a 2025, in ji rahoton Daily Trust.

Majiyoyi daga garin Agwara sun tabbatar da cewa maharan sun kai harin ne da misalin karfe 4:00 na Asuba, inda suka far wa ofishin yan sandan yankin da harbi.

Kakakin rundunar yan sandan Jihar Niger, SP Wasiu Abiodun, ya tabbatar da aukuwar lamarin inda ya ce:

“Maharan sun yi amfani da abubuwan fashewa da ake zargin nakiyoyi ne wajen cinna wa ofishin wuta bayan sun rinjayi jami'an dake bakin aiki.”

'Yan bindiga sun farmaki cocin Neja

Bayan sun gama da ofishin yan sandan, maharan sun nufi cocin United Methodist (UMC) dake cikin garin, kamar yadda rahoton Vanguard ya nuna.

Shugaban cocin, Reverend Yakubu Yohanna, wanda ya bayyana yadda suka tsira, ya ce:

Kara karanta wannan

Dubu ta cika: 'Yan sansa sun cafke gawurtaccen jagoran 'yan daba a Kano

“Sun zo garin sannan suka kai hari cocinmu. Ba su iske kowa ba, amma sun kona ginin da duk abin da ke ciki kurmus.”

Ya kara da cewa mambobin cocin na ci gaba da dawowa domin tantance barnar da aka yi musu.

Rundunar 'yan sanda ta tabbatar da sabon harin da 'yan bindiga suka kai Neja.
Sufeta Janar na rundunar 'yan sandan Najeriya a ofishinsa yana aiki. Hoto: @PoliceNG
Source: Twitter

Fargaba ta karu tsakanin mazauna gari

Wani mazaunin garin, Mallam Hussaini Mohammed, ya bayyana cewa halin rashin tabbas ya mamaye yankin, yayin da jama'a ke kira ga gwamnati da ta kara tsaurara matakan tsaro.

SP Wasiu Abiodun ya kara da cewa:

“Yan ta’addan sun zarce zuwa wasu sassan garin inda suka yi awon gaba da mutane kusan biyar wadanda har yanzu ba mu tantance ko su wane ne ba.”

Rundunar ta ce tana ci gaba da sanya ido tare da gudanar da bincike domin gano inda mutanen suke.

'Yan bindiga sun kashe mutum 60 a Neja

A wani labari, mun ruwaito cewa, akalla mutane 60 ne suka rasa rayukansu bayan wani mummunan hari da ’yan bindiga suka kai a Kasuwan Daji da ke Borgu a Jihar Nijar.

Kara karanta wannan

Yadda aka kama kayan hada bama bamai masu yawa za a kai wa ƴan bindiga a Zamfara

Rahotanni sun nuna cewa maharan sun fito ne daga dajin Kainji, inda suka kewaye kasuwar, suka sace mutane da dama musamman mata da yara, tare da banka wa kasuwa wuta.

Bayan fiye da sa'o'i 12 da harin, ana ci gaba da gano gawarwaki a dazuka da ke kewaye da wajen, yayin da gwamnati ta dauki matakan dakile irin waɗannan hare-hare.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com