Akwai Matsala: Manoma 3,500 Za Su Daina Noman Shinkafa a Najeriya, An Ji Dalili
- Manoman shinkafa dubu uku da dari biyar na shirin barin aikin noma bayan tafka asarar Naira biliyan 93 sakamakon shigo da shinkafar waje
- Rahoton fadar shugaban kasa ya nuna cewa manoma da dama sun koma noman ridi da waken soya wadanda suka fi riba a kasuwar duniya
- Masana sun ba wa gwamnatin tarayya shawararwarin yadda za a kare manoman kasar daga asara da kuma kare kasar daga karancin abinci
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Wani kwamitin fadar shugaban ƙasa kan manufofin noma (NAPM) ya bayyana cewa kimanin manoman shinkafa 3,500 ne ke shirin daina noma, sakamakon asarar Naira biliyan 93 da aka tafka a daminar 2025.
Wannan bayani ya fito ne daga wani binciken jin ra'ayin manoma na lokacin rani, inda aka tantance manoma 33,507 a jihohi 13 a matakin gwaji.

Source: Getty Images
Manoman shinkafa sun tafka asara
Jaridar Punch ta rahoto cewa wannan bincike ya nuna cewa kashi 10.6 na manoman shinkafar ba su da niyyar ci gaba da noman a kakar rani ta 2025/2026.
Rahoton ya nuna cewa manoman shinkafa sun tafka asarar Naira 20,220 a kowace hekta ɗaya a daminar 2025. Idan aka yi la'akari da cewa Najeriya tana da kimanin hekta miliyan 4.6 na noman shinkafa, asarar baki ɗaya ta kai Naira biliyan 93.
Babban abin da ya janyo wannan koma-baya shi ne matakin da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta ɗauka a watan Yulin 2024 na ba da damar shigo da shinkafa daga ƙasashen waje ba tare da haraji ba, domin rage tsadar abinci da ya haura kashi 40 a lokacin.
Manoma sun koma noman waken soya
Sakamakon faduwar farashin shinkafa a gida, manoma da dama sun fara sauya sheka zuwa noman amfanin gona na fitarwa waɗanda suka fi riba.
- Waken Soya: Noman waken soya ya ƙaru da kashi 38 yayin da manoma ke gudun shinkafa.
- Ridi: Najeriya ta fitar da ridi na Naira biliyan N700 a 2024, inda ta zama ta biyu a Afirka da kuma ta huɗu a duniya.
- Canji: Kashi 23 na manoman shinkafa sun bayyana niyyar komawa noman ridi ko waken soya saboda gasar da shinkafar waje ke yi musu.
Shawarwari ga gwamnatin tarayya
Kwamitin ya lura cewa shigo da tan miliyan 2.4 na shinkafa a 2025 ya janyo asarar kuɗaɗen ƙasashen waje masu yawa, kamar yadda rahoton Business Day ya nuna.
Tun da yake hauhawar farashin abinci ya sauko ƙasa da kashi 14, kwamitin ya ba da shawarar:
- Rufe kofofin shigo da shinkafa: Gwamnati ta daina ba da damar shigo da shinkafa daga waje domin kare manoman gida.
- Tallafawa manoman rani: Samar da tsare-tsaren da za su ƙarfafa gwiwar manoma 3,500 da ke shirin fita daga harkar.
Wannan matsin lamba ya sanya noman masara ya ragu da kashi 2.8, shinkafa kashi 7.9, yayin da gero ya ragu da kashi daya, lamarin da ke barazana ga wadatar abinci idan ba a ɗauki mataki ba.
An shigo da tan miliyan 2 na shinkafa
A wani labari, kun ji cewa, wani kwamitin manufofin noma da ke samun goyon bayan fadar shugaban kasa ya nuna damuwarsa kan adadin shinkafar da ke cikin Najeriya.
Alkaluman kasuwannin duniya sun nuna cewa 'yan Najeriya sun shigo da shinkafa sama da tan miliyan 2 kan makudan kudade, kamar yadda binciken kwamitin ya nuna.
Da wannan bincike, kwamitin ya fara neman gwamnatin tarayya karkashin Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ta dakatar da shigo da shinkafa daga kasashen ketare don kare manoman gida.
Asali: Legit.ng


