Mutane Sun Fusata, Sun Bankawa Wani Matashi Wuta a Jihar Kano
- An kama matashi da ake zargin barawo ne bayan ya yi kokarin kwace wayar wata mata a Dorayi Karshen Waya a cikin birnin Kano
- Matasa sun fusata saboda yadda barayon ya nemi hallaka matar, sun lakada masa dukan tsiya sannan suka banka masa wuta
- Rahotanni sun nuna cewa jami'an tsaro sun kai dauki wurin daga baya, sun tafi da wanda ake zargin domin ci gaba da bincike
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kano, Nigeria - Yayain da ake ci gaba da jimamin kisan matar aure, Fatima da yaranta shida, matasa sun fusata da aka kama wani matashi da laifin yunkurin satar wayar salula a Kano.
Rahotanni sun nuna cewa matasa sun banka wa matashin da ake zargi da satar waya wuta a unguwar Dorayi, yankin Karshen Waya da ke jihar Kano.

Source: Original
An kama barawon waya a Dorayi
Jaridar The Nation ta ruwaito cewa an kama barawon ne bayan ya yi yunkurin kwace wa wata mata wayar salula, amma dai bai samu nasara ba.
Rahotanni sun nuna cewa lamarin ya faru ne bayan wanda ake zargin ya farmaki matar, inda ya daba mata wuka a kirji.
Wannan danyen aiki ya tunzura mazauna unguwar Dirayi, musamman matasa, wadanda suka kama wanda ake zargin suka yi masa dukan tsiya sannan suka kone shi.
Barawo ya illata wata mata a Kano
Bayanai daga mazauna Dorayi sun nuna cewa an gaggauta kai matar da aka raunata zuwa asibiti mafi kusa domin ba ta kulawar gaggawa.
A gefe guda kuma, jami’an tsaro sun isa wurin daga baya inda suka tafi da wanda ake zargin domin ci gaba da bincike.
Har zuwa lokacin hada wannan rahoto, rundunar ’yan sandan jihar Kano ba ta fitar da wata sanarwa a hukumance kan lamarin ba.

Kara karanta wannan
Wasu kwamishinoni sun rikita gwamnatin Kano bayan komawar Abba APC? Gaskiya ta fito
Rundunar yan sanda ta yi shiru
Haka kuma, duk wani yunkuri na jin ta bakin jami'in hulda da jama'a na rundunar 'yan sandan jihar Kano, CSP Abdullahi Haruna Kiyawa, bai kai ga nasara ba har zuwa lokacin hada wannan rahoto.
Jihar Kano dai na fama da irin wadannan matsaloli na satar waya, inda 'yan daba ke amfani da makami wajen kwace muhimman abubuwa daga hannun mutane.

Source: Facebook
'Yan daban na iya kashe mutum don kawai su kwace wayarsa, to sai dai gwamnatin Kano da rundunar 'yan sanda sun dauki matakai, wadanda suka kawo saukin matsalar.
Matasan Dorayi sun rufarwa barawon musamman bayan yadda ya nemi kashe matar domin karbe wayarsa, daga bisani suka banka masa wuta, kamar yadda Aminiya ta kawo.
An kashe matar aure da yaranta 6 a Kano
A wani labarin, kun ji cewa waua tsageru sun haura har cikin gida, sun kashe matar aure da yaranta shida a unguwar Dirayi Chiranci a cikin birnin Kano.

Kara karanta wannan
Jirgin sama dauke da fasinjoji ya gamu da tsautsayi, 'dan Majalisa da mutane 14 sun mutu
Mazauna unguwar Dorayi Chiranci sun shiga tsahin hankali da firgici bayan kisan rashin imani da aka yi wa wata matar mai suna Fatima da 'ya'yanta.
Mutanen yankin sun bayyana lamarin a matsayin abin firgici da ban tsoro, wanda ba a taɓa ganin irinsa ba, inda suka nuna alhini da fargaba kan asarar rayukan da aka yi.
Asali: Legit.ng
