Yadda Aka Gyara Tudun Biri bayan Sojojin Najeriya Sun Yi Kuskuren Jefa Bam a Taron Maulidi

Yadda Aka Gyara Tudun Biri bayan Sojojin Najeriya Sun Yi Kuskuren Jefa Bam a Taron Maulidi

  • Gwamna Uba Sani ya bayyana yadda aka sake gina kauyen Tudun Biri bayan kuskuren da sojoji suka yi na jefa bam a taron Maulidi a 2023
  • Uba Sani ya yaba wa Shugaba Tinubu bisa sanya garin a matsayin na farko da ya amfana da shirin sake gina matsugunan da rikici ya shafa
  • Ya ce an gina titi mai tsawon kilomita 6, sabon asibiti da cibiyar koya wa matasa sana'o'i domin inganta rayuwar al'ummar Tudun Biri

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kaduna, Nigeria - Gwamna Uba Sani ya jinjinawa Shugaba Bola Tinubu saboda zaben kauyen Tudun Biri a matsayin wanda ya fara amfana da shirin sake gina garuruwan da rigingimu suka shafa.

Gwamnan na Kaduna, wanda ya bayyana hakan a ranar Juma’a, ya nuna cewa an zabi kauyen ne biyo bayan kuskuren harin bam da ya yi sanadiyyar mutuwar mahalarta taron Mauludi da dama a watan Disambar 2023.

Kara karanta wannan

Sanusi II ko Aminu Ado: Gwamna Abba ya bayyana wanda zai ci gaba da zama Sarkin Kano

Gwamna Uba Sani.
Gwamnan jihar Kaduna, Malam Uba Sani a taron kaddamar da ayyuka a Tudun Biri Hoto: Uba Sani
Source: Facebook

Daily Trust ta ce Uba Sani ya fadi haka ne yayin da yake jawabi wajen kaddamar da gidaje, hanyar kilomita 6, Cibiyar Kiwon Lafiya matakin farko, da kuma Cibiyar Koya wa Matasa Sana’o’i a Tudun Biri.

Gwamnan Kaduna ya yabawa Tinubu

Gwamna Uba Sani ya ce umarnin shugaban kasar ya sake gina gaba daya kauyen Tudun Biri, tare da samar da wani tsari na cigaba mai dorewa a kauyen.

"Wannan yunkuri ya wuce batun ba da agajin gaggawa na dan lokaci, sake gina garin aka yi, an samar da gidaje na zamani tare da muhimman ababen more rayuwa," in ji shi.

Gwamnan ya kara da cewa Jihar Kaduna ta taka muhimmiyar rawa wajen sake gina Tudun Biri tun daga matakin farko na faruwar bala’in har zuwa kaddamar da wadannan ayyuka.

Gudunmuwar gwamnatin Kaduna

A cewarsa, gwamnatin jihar Kaduna ta yi amfani da wasu sassa na gonaki domin gina gidajen zama da sauran ababen more rayuwa na al'umma don tabbatar da tsarin rayuwa da tsaron jama'a sun inganta.

Kara karanta wannan

Shettima ya kaddamar da gidaje 133 a Tudun Biri, garin da aka kashe masu mauludi

Ya bayyana cewa an tuntubi manoman da abin ya shafa kuma an ba su tallafi ta hanyoyi daban-daban, ciki har da kayan aikin gona, shirye-shiryen dogaro da kai, da kuma samar musu da wasu hanyoyin neman abinci.

Muhimman ayyukan da aka yi a Tudun Biri

Daga cikin ayyukan da aka yi a garin Tudun Biri akwai gina hanyar kwalta mai tsawon kilomita 6 wadda ta hada garin da hanyar Filin Jirgin Sama na Kasa-da-Kasa na Kaduna.

Haka nan gwamnati ta gina sabon asibiti tare da zuba kayan aiki, wadda ke da gadaje 25 kuma ana ayyyka da dama ciki har da kula da mata masu juna biyu, kananan tiyata, da duba idanu, in ji rahoton Vanguard.

Tudun Biri.
Taron kaddamar da ayyuka da aka gudanara kauyen Tudun Birida ke Kaduna Hoto: Uba Sani
Source: Facebook

Shettima ya kaddamar da gidaje a Tudun Biri

A wani rahoton, kun ji cewa mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima ya kaddamar da sababbin gidaje 133 a Tudun Biri domin sake tsugunar da mutanen garin.

Wannan mataki ya cika alkawarin da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ɗauka na sake gina al'ummar garin bayan kuskuren da jirgin yakin sojoji ya yi a 2023.

Shettima ya tuna yadda ya ziyarci Tudun Biri a watan Disambar 2023 jim kaɗan bayan harin, inda ya isar da saƙon Tinubu na cewa lallai za a gina garin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262