Makamai, Motoci da Aka Bankado a Shirin Juyin Mulki, an Gano Soja 1 a Amurka

Makamai, Motoci da Aka Bankado a Shirin Juyin Mulki, an Gano Soja 1 a Amurka

  • Bayanai sun bankado makamai, motoci da kudade da aka kwato daga jami’an soja da fararen hula da ake zargi da shirya juyin mulki
  • Bincike ya gano shirin wani makirci, inda aka tanadi manyan makamai, motocin aiki, da shirye-shiryen kashe manyan shugabanni
  • Akalla jami’an soja 25 da wasu fararen hula za su fuskanci shari’a, yayin da ake zargin tsohon gwamna Timipre Sylva da hannu a batujn

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja – An samu cikakkun bayanai na musamman kan makamai, harsasai, motoci da kuɗaɗe da aka ƙwato daga wasu jami’an soja da fararen hula.

Binciken na da alaka zargi da yunƙurin kifar da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu a shekarar da ta gabata.

Ana binciken sojoji da ake zargi da yunkurin juyin mulki
Ministan tsaro, Christopher Musa da Shugaba Bola Tinubu. Hoto: Bayo Onanuga.
Source: Facebook

Juyin mulki: Ana ci gaba da bankado bayanai

Rahoton Premium Times ta ce wani kwamitin bincike na haɗin gwiwar hukumomin tsaro, wanda gwamnatin tarayya ta kafa ya kammala bincike kan yunƙurin juyin mulkin da bai yi nasara ba.

Kara karanta wannan

Iyalan sojojin da suka shirya juyin mulki sun yi wa Tinubu maganar afuwa

Majiyoyi sun tabbatar da cewa masu bincike sun ƙwato motocin ɗaukar bindiga guda biyu, bindigogin harbo jiragen sama, bindigogin PKT, bama-baman RPG, bindigogin AK-47, harsasai da kayan aikin soja daga wani Laftanar-Kanar.

Baya ga makamai, jami’an tsaro sun kuma ƙwace motoci huɗu na Toyota Hilux, Toyota Prado guda ɗaya, motocin saloon Toyota guda biyu, da kuma motoci 32 na Volkswagen Golf, waɗanda ake zargin an saya su domin ayyukan sirri.

Binciken ya nuna cewa an sayi motocin ne domin zirga-zirgar leƙen asiri da shiga wurare masu matuƙar muhimmanci ba tare da jawo hankalin jama’a ba, ciki har da filayen jiragen sama da wasu muhimman cibiyoyin gwamnati.

Wata majiya ta ce:

“An yi amfani da motocin ne wajen ankarar jami’ai ba tare da an gano su ba, tare da gudanar da ayyukan bincike da ke da alaƙa da shirin juyin mulkin.”
Sojoji da dama sun shiga hannu kan zargin shirya juyin mulki
Shugaba Bola Tinubu na Najeriya. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu.
Source: Twitter

Yadda ake bibiyar sojojin da ke da 'hannu'

Binciken ya kuma gano cewa Manjo Janar mai ritaya, Adamu, na daga cikin manyan mutanen da ke da alaƙa da wannan ƙungiya, inda har yanzu yake gudun hijira tare da wasu mutum uku.

Kara karanta wannan

Bayanai sun kara fitowa, an gano wani shiri da masu yunkurin kifar da Tinubu suka yi

Majiyoyin leƙen asiri sun bayyana cewa an gano ɗaya daga cikin waɗanda suka tsere ya tsallaka zuwa wata ƙasa a Kudancin Amurka, amma ba a bayyana takamaiman wurin da yake ba saboda dalilan tsaro.

Legit Hausa ta ruwaito a baya cewa jami’an soja 16 aka fara kama su bisa zargin shiga kai tsaye, amma bayan kafa kwamitin bincike na musamman ƙarƙashin jagorancin Janar Undiandeye, an kama wasu ƙarin mutane.

Shirin kashe Tinubu, jami'an gwamnati

Rahotanni sun ce an fara tsara juyin mulkin ne domin 29 ga Mayu, 2023, ranar rantsar da Shugaba Tinubu, amma aka dakatar da shirin sakamakon ƙarancin kuɗi da matsalolin kayan aiki.

Sai dai daga bisani, a shekarar 2024, masu shirin suka sake farfaɗo da shirin bayan samun wasu kuɗaɗe.

An ce an yi niyyar kashe manyan shugabannin ƙasa, ciki har da Shugaba Bola Tinubu, Mataimakin Shugaba Kashim Shettima, Shugaban Majalisar Dattawa Godswill Akpabio, da Kakakin Majalisar Wakilai Tajudeen Abbas.

Zarge-zarge kan Birgediya Janar M.A Sadiq

Kun ji cewa Sojojin Najeriya sun tabbatar da yunƙurin juyin mulki da aka shirya kifar da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu, inda aka cafke jami’ai 16.

Kara karanta wannan

Birgediya Janar Sadiq: Bayanan da muka sani kan sojan da ake zargi da hannu a 'juyin mulki'

Daga cikin wadanda aka cafken akwai Birgediya-janar Musa Abubakar Sadiq wanda ake zargin babba ne a yunkurin kifar da gwamnatin.

Bincike ya nuna cewa ana zargin Sadiq da sanin shirin juyin mulkin tun da wuri amma bai sanar da hukumomi ba kamar yadda ya dace.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.