Dakarun Sojoji Sun Samu Nasara, an Kashe Babban Kwamandan ISWAP

Dakarun Sojoji Sun Samu Nasara, an Kashe Babban Kwamandan ISWAP

  • Dakarun sojojin Najeriya sun samu nasara a yakin da suke yi da 'yan ta'adda masu tayar da kayar baya a jihar Borno
  • Sojojin sun samu nasarar hallaka tantirin kwamandan kungiyar 'yan ta'adda ta ISWAP baya an gwabza fada a karamar hukumar Damboa
  • Hakazalika, sojojin sun samu nasarar hallaka karin wasu 'yan ta'adda tare da kwato makamai da dama a hannunsu

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Borno - Dakarun sojojin Najeriya na rundunar Operation Hadin Kai sun kashe wani shahararren kwamandan Boko Haram/ISWAP mai suna Julaibib.

Sojojin sun kashe dan ta'addan ne wanda ke aiki a yankin Gujba na Timbuktu Triangle, a yayin wata arangama da aka yi a jihar Borno.

Sojojin Najeriya sun hallaka 'yan ta'adda a Borno
Kwamandan rundunar Operation Hadin Kai tare da dakarun sojoji Hoto: @HQNigerianArmy
Source: Twitter

Jami’in yaɗa labarai na rundunar OPHK, Laftanar Kanal Sani Uba, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar, 31 ga watan Janairun 2026 a shafin X.

Kara karanta wannan

Dubu ta cika: 'Yan sansa sun cafke gawurtaccen jagoran 'yan daba a Kano

Sojoji sun kashe kwamandan ISWAP

Ya bayyana cewa an yi arangamar ne a a kusa da Kimba a karamar hukumar Damboa ta jihar Borno, a ranar Juma'a 30 ga watan Janairu, 2026.

"A wata muhimmiyar nasara, bayanan sirri sun tabbatar da kashe Julaibib, babban kwamandan ISWAP da ke aiki a yankin Gujba na Timbuktu Triangle."
"An kashe shi ne a yayin wata arangama da aka yi a kusa da Kimba a karamar hukumar Damboa ta jihar Borno, a ranar 30 ga Janairu, 2026."
“Karin bayanan sirri sun kuma nuna cewa kawar da wannan jagoran ’yan ta’adda ya jefa ’yan ISWAP a yankin cikin rudani, inda aka kashe mayaka da dama a yayin wannan aiki.”

- Laftanar Kanal Sani Uba

Rundunar ta bayyana cewa wannan gagarumar nasara ta yi wa tsarin jagoranci da umarni na ISWAP a yankin mummunar illa.

Sojoji sun ragargaji 'yan ta'adda

A wani aiki da ya danganci hakan, sojojin OPHK tare da hadin gwiwar 'yan CJTF sun kashe ’yan ta’adda uku a wani kwanton bauna da aka shirya a tsakanin al’ummomin Ngazalgana da Lamusheri a jihar Borno.

Kara karanta wannan

'Yan ta'addan Boko Haram sun sake kai hari a Borno, an kashe sojoji da fararen hula

Dakarun sojoji sun kashe kwamandan ISWAP
Taswirar jihar Borno, tarayyar Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original
"Aikin ya biyo bayan samun sahihan bayanan sirri kan motsin ’yan tada kayar baya a yankin. Sojoji sun shirya kwanton bauna a kan hanyar da aka gano, inda suka yi musu luguden wuta, lamarin da ya kai ga kashe ’yan ta’adda uku, yayin da wasu suka tsere dauke da raunukan harbin bindiga."
“An kwato bindigogi kirar AK-47 guda biyu a wurin. Wannan aiki na daga cikin kokarin da ake ci gaba da yi domin hana ’yan ta’adda ’yancin motsawa tare da raunana karfinsu na kai hare-hare a yankin."

- Laftanar Kanal Sani Uba

'Yan Boko Haram sun kashe sojoji

A wani labarin kuma, kun ji cewa 'yan ta'addan Boko Haram dauke da makamai sun kai harin ta'adanci a jihar Borno.

Harin na 'yan ta'addan Boko Haram ya ritsa da dakarun sojoji tare da wasu leburori a karamar hukumar Biu ta jihar.

Mummunan harin ya yi sanadiyyar rasa rayukan sojoji guda biyar tare da leburori 15 wadanda ke aikin gina wata gada da ke kan hanya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng