Tsuguno ba Ta Kare ba: Aminu Babba Ɗan Agundi Ya Ja Daga kan Sahihancin Sarautar Kano
- Sarkin Dawaki Babba na Masarautar Kano, Alhaji Aminu Babba 'Dan Agundi ya yi magana a kan batun masarautar Kano
- Yana wannan magana ne a lokacin da gwamnatin Abba Kabir Yusuf a Kano ta bayyana cewa Muhammadu Sanusi II ne Sarkin Kano
- A martaninsa, Alhaji Baffa Babba 'Dan Agundi ya jaddada cewa shari’ar rikicin masarautar Kano tana gaban Kotun Ƙoli
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Alhaji Aminu Babba Danagundi, Sarkin Dawaki Babba na Masarautar Kano, ya sake nanata matsayarsa a kan rikicin sarautar Kano.
Basaraken ya ce babu wata yarjejeniya ta siyasa ko fahimtar juna da za ta iya cire Aminu Ado Bayero daga karagar mulkin Sarkin Kano.

Source: Facebook
A hira da ya yi da Daily Trust, Alhaji Baffa Babba 'Dan Agundi ya ce shari’a na gaban Kotun Ƙoli game da soke dokar masarautu da kuma cire Sarkin Kano.
Babba 'Dan Agundi ya yi watsi da sulhu
Alhaji Baffa Babba 'Dan Agundi ya ce komawar Gwamna Abba Kabir Yusuf zuwa jam'iyyar APC na shi ne zai warware matsalar masarauta ba.
A cewarsa:
"Abin da na sani shi ne muna kotu, kuma shari’ar tana gaban Kotun Ƙoli.”
Ya ce babu wata yarjejeniya da aka sani da za ta iya cire iyalan Ado Bayero ko Aminu Ado Bayero daga sarautar Kano.
Ya ƙara da cewa tunanin wasu mutane na cewa da zarar gwamna ya samu daidaito da gwamnatin tarayya, kowa zai janye ƙara, ba gaskiya ba ne kuma ba zai yiwu ba.

Source: Twitter
Danagundi ya jaddada cewa marigayi Ado Bayero ya yi fiye da shekaru 50 yana mulkin Kano ba tare da aikata wani laifi ba.
A ganinsa, ɗansa ya cancanci gadon sarautar, ba wani daga wani gida ba. Ya ce wannan matsayi ne da ya ɗauka da muhimmanci sosai.
Abin da 'Dan Agundi ke nema a Kotun ƙoli
Dangane da fatan da yake da shi kan shari’ar Kotun Ƙoli, Danagundi ya ce burinsa shi ne gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya gane gaskiya ya kuma naɗa Aminu Ado Bayero a matsayin Sarkin Kano.
Ya bayyana cewa ƙarar da ya shigar ba wai kai tsaye kan cire sarki ba ce, sai dai kan yadda aka bi ka’ida wajen soke dokar masarautu da kafa sabuwar doka.
Dan Agundi ce ya kamata gwamnati ta bi matakan doka, daga ciki har da sauraron ra’ayin jama’a, domin dokar tana shafar mutane kai tsaye, musamman masu rike da mukamai a masarauta.
Ya jaddada cewa ya shigar da ƙara ne bisa tauye masa haƙƙinsa na kundin tsarin mulki, domin sabuwar doka ta cire shi daga mukaminsa.
Gwamnati ta yi magana kan sarautar Kano
A baya, mun wallafa cewa Mai martaba Muhammadu Sanusi II ya dawo jihar Kano a ranar Juma’a, 30, Janairu, 2026, bayan wata tafiya da ya yi zuwa Kudancin kasar nan.
Dawowar tasa ta zo ne jim kadan bayan gwamnatin Jihar Kano ta fito karara ta bayyana cewa shi ne halastaccen Sarkin Kano, ba Aminu Ado Bayero ba duk da komawar Gwamna APC.
A yayin tafiyar da ya yi kafin dawowarsa Kano, Mai martaba Muhammadu Sanusi II ya kai ziyarar gaisuwar ta’aziyya ga iyalan Otunba Adekunle Ojora a jihar Legas.
Asali: Legit.ng

