Halin da Ake Ciki bayan Matashi Ya Rasa Ransa a Masallaci da Ya Farmaki Liman Yana Huduba

Halin da Ake Ciki bayan Matashi Ya Rasa Ransa a Masallaci da Ya Farmaki Liman Yana Huduba

  • Wani mummunan lamari ya faru a masallaci inda aka lakadawa masallaci duka har ya mutu a wurin ibada
  • Rahotanni sun nuna cewa marigayin ya tayar da husuma yayin hudubar liman, inda ya yi yunkurin kai masa hari, lamarin da ya haddasa rikici
  • ‘Yan sanda sun tabbatar da faruwar lamarin, sun ce mutuwar ta faru a kusa da masallacin, yayin da ake ci gaba da bincike

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Osogbo, Osun - Wani mummunan al’amari ya girgiza al’umma a ranar Juma’a 30 ga watan Janairun 2026 a babban Masallacin Ummu Haani Adigun.

Rahotanni sun ce an yi wa wani duka a masallacin da ke Ayedun, Osogbo, babban birnin jihar Osun har ya rasa ransa.

An hallaka wani a masallacin Osun
Taswirar jihar Osun da aka samu iftila'in kisan kai a masallaci. Hoto: Legit.
Source: Original

Matashi ya rasa ransa a masallacin Osun

Rahoton Tribune ya bayyana cewa wani mai ibada mai suna Najeem ya rasa ransa bayan wasu masu ibada sun doke shi a harabar masallacin bayan sallar asuba.

Kara karanta wannan

Barawon motar Naira miliyan 75 ya yi wa 'yan sanda barkwanci a Kano

An gano cewa rikicin ya fara ne bayan sallar Asuba, lokacin da marigayin ya katse hudubar liman, lamarin da ya janyo rudani a cikin masallacin.

Ba a san dalilin wannan mummunan aiki ba a lokacin hada wannan rahoto, amma an ce marigayin ya fusata liman tare da yi masa barazana.

Bincike ya nuna cewa liman ya gudu daga masallacin domin tsira, amma marigayin ya bi shi, lamarin da ya sa sauran masu ibada suka shiga tsakani.

Yadda matashin ya rasa ransa a Osun

A yayin kokarin hana shi kai wa liman hari, rikicin ya rikide zuwa duka da turmutsitsi, inda aka ce an yi masa mugun duka.

Shaidu sun shaida cewa wasu na ganin ya mutu ne a cikin masallacin, yayin da wasu ke cewa ya fadi cikin magudanar ruwa a gaban masallacin.

Wani shaida mai suna Jimoh ya ce marigayin ya cire makirufo a lokacin huduba, ya yi yunkurin kai wa liman hari, kafin ya tsere daga masallacin.

Ya kara da cewa wasu masu ibada sun yi kokarin rike shi, amma rikicin ya tsananta har ya bazu zuwa wajen masallacin.

Kara karanta wannan

Mazauna Kano sun dimauce bayan fashewar abu mai kama da bam

Matashi ya rasa ransa a masallaci
Gwamna Ademola Adeleke na jihar Osun. Hoto: Governor Ademola Adeleke.
Source: Twitter

Abin da yan sanda suka ce kan harin

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan Osun, Abiodun Ojelabi, ya tabbatar da lamarin, amma ya ce mutuwar ba ta faru a cikin masallacin ba.

A cewarsa, gawar marigayin an ajiye ta a dakin ajiyar gawawwaki na Asibitin Koyarwa na Jihar Osun, yayin da aka tura jami’an tsaro.

Ya bayyana wa wakilin Legit Hausa cewa ana ci gaba da bincike domin gano wadanda ke da hannu a wannan mummunan lamari.

"Har yanzu ana kan bincike game da kisan amma ya faru ne a wajen masallaci ba a ciki ba kamar yadda ake zato."

An yi wa ladan yankan rago a Kano

Kun ji cewa al’ummar Hotoro Maraba a Kano sun shiga firgici bayan wani matashi ya kashe ladanin masallaci a lokacin sallar Asubahi.

Rahotanni sun ce rikici ya fara ne bayan ladani ya ce lokacin sallah bai yi ba, lamarin da ya fusata matashin ya yanke makogoronsa.

Yan sanda sun mamaye yankin domin hana barkewar tarzoma bayan fusatattun matasa sun yi kukan kura sun kashe matashin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.