Dubu Ta Cika: 'Yan Sanda Sun Cafke Gawurtaccen Jagoran 'Yan Daba a Kano

Dubu Ta Cika: 'Yan Sanda Sun Cafke Gawurtaccen Jagoran 'Yan Daba a Kano

  • Wani gawurtaccen dan daba da ya addabi mutane a jihar Kano ya fada komar rundunar 'yan sanda bayan an shigar da korafi a kansa
  • Jami'an rundunar 'yan sandan sun cafke jagoran 'yan daban ne bayan an dade ana nemansa ruwa a jallo saboda ayyukan da yake yi
  • Hakazalika, 'yan sandan sun yi caraf da wasu mutane guda tara wadanda aka bayyana a matsayin 'yan kungiyar jagoran na daba

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Kano - Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama wani shahararren jagoran daba da ake nema ruwa a jallo mai suna Sunusi, wanda aka fi sani da Dawa Dan Kamsusi.

Rundunar 'yan sandan ta cafke Sunusi ne tare da wasu mutane tara da ake zargin mambobin kungiyarsa ne, bisa zargin hannu a wasu laifuffuka daban-daban a sassan jihar.

Kara karanta wannan

'Yan ta'addan Boko Haram sun sake kai hari a Borno, an kashe sojoji da fararen hula

'Yan sanda sun kama jagoran 'yan daba da aka nema ruwa a jallo a Kano
Kwamishinan 'yan sandan jihar Kano, Ibrahim Bakori Hoto: Abdullahi Haruna Kiyawa
Source: Facebook

Mai magana da yawun rundunar 'yan sandan jihar Kano, Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa a shafinsa na Facebook a ranar Juma'a, 30 ga watan Janairun 2026.

An shigar da korafi kan jagoran 'yan daba

Kamen ya biyo bayan wani korafi da kungiyar Hannu da Yawa Youth Development Association Bachirawa (HADAYA) ta shigar a ranar 5 ga Janairu, 2026.

A cikin takardar korafin da aka mikawa ’yan sanda, kungiyar ta nuna damuwa kan yadda laifuffuka ke ci gaba da faruwa a yankunan Bachirawa, Kurna, Rijiyar Lemo, Zango, Kunture da makwabtansu a Kano.

A cewar sanarwar ’yan sanda, wani bangare na wasikar na cewa:

“Duk da korafe-korafe da dama da al’umma suka shigar, wadannan laifuka na ci gaba da faruwa kuma alamu na nuna suna kara muni."

Kara karanta wannan

Masu safarar makamai ga tantirin jagoran 'yan bindiga sun shiga hannun jami'an tsaro

"Muna rokon ofishinku da ya gaggauta binciken wadannan zarge-zarge tare da daukar matakin da ya dace bisa doka domin dawo da zaman lafiya da tsaro.”

'Yan sanda sun bazama aiki

Bayan karbar korafin, kwamishinan ’yan sandan jihar, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya umarci jami’an sashen yaki da daba na rundunar da su bi sawun wadanda ake zargi.

Sanarwar ta bayyana cewa bayan dogon bincike na sirri, jami’an suka samu nasarar kama babban wanda ake zargi, Sunusi Dawa Kamsusi, mai shekaru 26, mazaunin unguwar Bachirawa a Kano.

An kwato wukake uku da kuma wasu layu a hannunsa, yayin da daga baya aka bi sawun wasu mambobi tara na kungiyar tare da kama su.

A cewar sanarwar, wanda ake zargin ya amsa laifin aikata fashi da makami, kwacen wayoyin hannu, balle shaguna da gidaje, da sata, da sauransu yayin bincike.

Rundunar ta kara da cewa kimanin mutane 30 ne zuwa yanzu suka shigar da korafi a kan wadanda ake zargin.

'Yan sanda sun kama tantirin dan daba a Kano
Kayayyakin da 'yan sanda suka kama a hannun jagoran 'yan daba a Kano Hoto: Abdullahi Haruna Kiyawa
Source: Facebook

Za a mika su gaban kotu

Rundunar ta ce za a gurfanar da wadanda ake zargin a gaban kotu da zarar an kammala bincike.

Kara karanta wannan

Yadda aka kama kayan hada bama bamai masu yawa za a kai wa ƴan bindiga a Zamfara

Sanarwar ta kara da cewa CP Bakori ya yabawa jami’an da suka gudanar da aikin, tare da jinjinawa al’umma bisa hadin kai da suka bayar, inda ya ce goyon bayansu ya taimaka matuka wajen nasarar binciken.

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta sake jaddada kudirinta na yaki da daba da sauran laifuffuka a fadin jihar.

'Yan sanda sun cafke malamin Musulunci

A wani labarin kuma, kun ji cewa jami'an 'yan sanda sun cafke wani babban limamin masallacin Juma'a a jihar Osun.

'Yan sandan sun kama babban limamin ne na masallacin Jumu'a na Ummu Hanni Adigu da ke yankin Ogo-Oluwa a birnin Osogbo, tare da wasu mutum uku.

Dakarun 'yan sanda sun kama su ne biyo bayan mutuwar wani mai fentin mota, Najeem Hammed, bayan wani rikici da ya faru tsakaninsa da masu ibada.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng