'Yan Ta'addan Boko Haram Sun Sake Kai Hari a Borno, an Kashe Sojoji da Fararen Hula
- An sake shiga jimami a jihar Borno bayan wani sabon harin ta'addanci da 'yan Boko Hram suka kai kan sojoji da fararen hula
- Harin na 'yan ta'addan dai ya ritsa da mutanen ne lokacin da suke aikin gina wata gada a karamar hukumar Biu ta jihar Borno
- Mummunan harin da 'yan ta'addan suka kai ya jawo an samu asarar rayukan sojoji da fararen hula wadanda ke neman na abinci
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Borno - ’Yan ta’addan Boko Haram sun kashe mutane fiye da 20 a wani sabon hari da suka kai a jihar Borno.
'Yan ta'addan na Boko Haram sun kai harin ne a kauyen Wajirko da ke kan hanyar Biu–Damboa a jihar Borno.

Source: Twitter
Rahotan jaridar The Punch ya nuna cewa ’yan ta’addan sun kai harin ne da misalin karfe 12:00 na rana a ranar Alhamis, 29 ga watan Janairun 2026.

Kara karanta wannan
'Yan ta'addan ISWAP sun farmaki sansanin sojoji da jirage marasa matuka, an yi barna
'Yan ta'addan Boko Haram sun yi barna
'Yan ta'addan na Boko Haram sun kuma jikkata wasu da dama da suka samu damar tserewa.
Wani babban jami’in tsaro ya bayyana cewa daga cikin wadanda aka kashe akwai sojoji biyar da kuma mambobi uku na rundunar Civilian Joint Task Force (CJTF).
"Fararen hula suna aikin gine-gine ne a wurin da ake gina gada a ranar Alhamis, kafin ’yan ta’addan su kai musu hari." A yayin harin, an kashe sojoji biyar, an kuma kashe mambobi uku na Civilian Joint Task Force, tare da fararen hula da dama da ke aiki a wurin.”
- Wani jami'in tsaro
'Yan Boko Haram sun kashe mutane
Jaridar Premium Times ta ce da yake tabbatar da harin a wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma’a, 30 ga watan Janairun 2026, sakataren kungiyar Biu Forum na kasa, Bukar Tashkalma, ya bayyana kaduwa da alhini kan lamarin, inda ya ce mutane sama da 20 sun rasa rayukansu.
"Biu Forum ta kadu kuma ta shiga alhini sakamakon sabon harin da ’yan ta’addan Boko Haram suka kai wa sojoji da fararen hula a Wajirko da ke kan hanyar Biu–Damboa a jihar Borno."
"Inda sama da mutane 20 daga Biu suka rasa rayukansu, yayin da wasu da dama suka samu raunuka daban-daban."
“Harin da ya faru a lokacin da ake aikin share daji da sake gina gada ya jefa al’ummar Biu cikin jimami da damuwa.”
"Shugabanni da mambobin Biu Forum sun yi addu’ar Allah Madaukakin Sarki Ya gafarta wa mamatan Ya kuma sanya su Aljanna, tare da fatan samun sauki cikin gaggawa ga wadanda suka jikkata."
- Bukar Tashkalma
An yi wa fararen hula jana'iza
A cewarsa, an riga an yi wa fararen hular da suka rasu jana’iza bisa koyarwar Musulunci.

Source: Original
"Muna mika ta’aziyyarmu ga iyalai, abokai da ’yan uwa na wadanda abin ya shafa, muna kuma kira gare su da su yi hakuri da kaddarar Allah."
"An gudanar da sallar jana’iza a fadar Sarkin Biu, karkashin jagorancin Babban Limamin Masallacin Juma’a na Biu, Nuruddeen Umaru Isa, sannan aka binne mamatan bisa ka’idojin Musulunci a Biu.”
"Muna yaba wa jajircewar jami’an tsaronmu, tare da kira ga Gwamnatin Tarayya da ta kara kaimi wajen magance tushen matsalar ta’addanci, tare da samar da isasshen tsaro ga jihar Borno da daukacin yankin Arewa maso Gabas.”
- Bukar Tashkalma
'Yan ISWAP sun farmaki sojoji
A wani labarin kuma, kun ji cewa 'yan ta'addan Boko Haram dauke da makamai sun kai hari kan wani sansanin sojoji a jihar Borno.
'Yan ta'addan masu dauke da jiragen yaki marasa matuka sun kai harin ne kan wani sansanin sojoji a jihar Borno inda suka kashe sojoji da dama.
Majiyoyi biyu na tsaro sun bayyana cewa akalla sojoji tara da mambobin CJTF biyu ne suka mutu, yayin da kusan mutane 16 suka jikkata.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

