Farashin Litar Man Fetur na Shirin Gagarumin Tashi a Najeriya
- ’Yan kasuwar man fetur sun yi gargadin cewa farashin fetur na iya tashi zuwa kusan N1,000 kan kowace lita sakamakon tashin farashin danyen mai a kasuwar duniya
- Tashin farashin danyen mai zuwa sama da dala 70 kan kowace ganga ya zo ne a daidai lokacin da matatar Dangote ta kara farashin fetur daga N739 zuwa N839
- Kungiyoyin ’yan kasuwa sun ce idan wannan yanayi ya ci gaba, masu saye da masu sayarwa za su fuskanci karin matsin tattalin arziki a sassa daban-daban na kasar
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCt, Abuja – Ana fargabar cewa farashin fetur a Najeriya zai iya kaiwa N1,000 kan kowace lita nan gaba kadan, biyo bayan tashin farashin danyen mai a kasuwar duniya zuwa sama da dala 70 kan kowace ganga.
Wannan bayani ya fito ne daga bakin ’yan kasuwar man fetur da suka ce hauhawar farashin danyen mai a duniya na da tasiri kai tsaye kan farashin man da ake sayarwa a cikin gida.

Source: Getty Images
Punch ta wallafa cewa lamarin na zuwa ne a wani lokaci da ’yan Najeriya ke ci gaba da kokawa da tsadar rayuwa, yayin da karin farashin fetur ke kara nauyi a kan harkokin sufuri da kasuwanci.
Dalilin tashin farashin danyen mai
Rahotanni sun nuna cewa farashin danyen mai ya tashi da kusan kashi 3 kasuwar duniya sakamakon fargabar rikici tsakanin Amurka da Iran, daya daga cikin manyan kasashen da ke samar da danyen mai a duniya.
Masu sharhi kan harkokin mai sun bayyana cewa ana tsoron rikici a yankin Gabas ta Tsakiya, musamman idan Iran ta dauki matakin rufe hanyar Hormuz, wanda ake jigilar kusan ganga miliyan 20 na danyen mai a kowace rana ta nan.
Vanguard ta rahoto cewa wannan yanayi ya sanya farashin Brent, wanda shi ne ma’aunin farashin danyen mai a duniya, ya kai matakin da ba a gani ba tsawon watanni biyar da suka gabata.
Farashin mai zai tashi a Najeriya
Da yake zantawa da manema labarai, kakakin ’yan kasuwar man fetur masu zaman kansu, Chinedu Ukadike, ya ce hauhawar farashin danyen mai da canjin kudin musayar waje ne manyan abubuwan da ke kayyade farashin fetur a Najeriya.
Ya bayyana cewa idan farashin danyen mai bai sauka ba, farashin fetur zai ci gaba da hawa, musamman a yankunan da ke da nisa da manyan ma’adanar ajiya ko matatar Dangote.

Source: Getty Images
Wani babban dillalin man fetur ya tabbatar da cewa kudin shigo da fetur na kara tashi, yana mai cewa idan farashin danyen mai ya ci gaba da hawa, kudin shigo da fetur a Najeriya na iya haura N900 kan kowace lita.
'Dan kasuwar ya ce:
“Maganar lita ta kai zuwa N1,000 ba abin mamaki ba ne. A baya an sayar da fetur a kusan haka, a lokacin da farashin gangar mai ya kai kusan $75,"
Dangote ya kara kudin man fetur
A wani labarin, kun ji cewa matatar Dangote ta sanar da karin kudin mai ga manyan diloli da ke sayen kaya a wajenta bayan shiga 2026.
Rahotanni sun nuna cewa tun bayan karin farashin da matatar Dangote ta yi, yawancin gidajen mai sun kara kudi, inda a Lagos lita ke N830 zuwa N859.
A lokaci guda, ’yan kasuwa sun lura da raguwar sayen mai, inda aka ce mutane na rage yawan amfani da fetur saboda tsadar farashi.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


