Shettima Ya Kaddamar da Gidaje 133 a Tudun Biri, Garin da Aka Kashe Masu Mauludi

Shettima Ya Kaddamar da Gidaje 133 a Tudun Biri, Garin da Aka Kashe Masu Mauludi

  • Mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima ya kaddamar da sababbin gidaje `133 a Tudun Biri domin sake tsugunar da mutanen garin
  • Gwamnatin Tarayya ta gina makarantu da sauran ababen more rayuwa a matsayin cika alkawarin da Shugaba Bola Tinubu ya yi a baya
  • Wannan aiki na Tudun Biri yana daga cikin shirin gwamnati na sake gina yankunan da rikici ya shafa, musamman a wasu jihohi 7na kasar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kaduna - Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, ya ƙaddamar da rukunin gidajen da aka gina don sake tsugunar da mutanen Tudun Biri dake ƙaramar hukumar Igabi a jihar Kaduna.

Wannan mataki ya cika alkawarin da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ɗauka na sake gina al'ummar garin bayan mummunan hatsarin jirgin na soji da ya rutsa da su sama da shekaru biyu da suka gabata.

Kara karanta wannan

Birgediya Janar Sadiq: Bayanan da muka sani kan sojan da ake zargi da hannu a 'juyin mulki'

Shettima ya kaddamar da shirin tsugunar da al'ummar Tudun Biri bayan harin sojojin sama.
Kashim Shettima yayin da yake kaddamar da gidajen da aka gina a Tudun Biri, jihar Kaduna. Hoto: @KashimSM
Source: Twitter

Kashim Shettima ne da kansa ya bayyana hakan a cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook a ranar Juma'a, 30 ga Janairu, 2025.

An kaddamar da gidaje a Tudun Biri

Sakon ya nuna cewa rukunin gidajen ya ƙunshi sabbin gidaje guda 133 da aka kammala, tare da makarantu da sauran ababen more rayuwa a ƙarƙashin tsarin sake tsugunar da mutanen da rikici ya shafa (RSPIC).

Shettima ya tuna yadda ya ziyarci Tudun Biri a watan Disambar 2023 jim kaɗan bayan harin, inda ya isar da saƙon Tinubu na cewa lallai za a gina garin. A watan Yulin 2024 aka fara ginin, wanda a yanzu aka kammala.

"Yau mun nuna cewa adalci shi ne silar da ke haɗa ƙasa, kuma tausayi ba rauni ba ne ga gwamnati, face ƙarfin zuciya ne," in ji Shettima yayin taron.

Ya ƙara da cewa:

"Wannan rukunin gidaje na Tudun Biri wata hanya ce ta samar da fata ga iyalai waɗanda rayuwarsu ta tarwatse. Wannan tabbaci ne cewa Najeriya ba ta yin watsi da ƴan ƙasarta a lokacin wahala."

Kara karanta wannan

Jarumin Nollywood ya shiga hannu a kan zargin shirin juyin mulki

Wasu jihohi da ke cikin irin wannan shiri

Shettima ya bayyana cewa wannan aiki na Kaduna yana ɗaya daga cikin manyan tsare-tsare na tarayya da nufin samar da mafita ga yankunan da rikici ya shafa.

Ya bayyana cewa irin waɗannan ayyukan suna kan gudana a jihohin Kebbi, Sokoto, da Zamfara. Sannan ana aiwatar da su a Niger, Katsina, da kuma Benue.

Haka kuma, mataimakin shugaban kasar ya yaba wa gwamnan Kaduna, Sanata Uba Sani, saboda haɗin kan da ya bayar wajen ganin wannan babban aiki ya tabbata, in ji rahoton Arise News.

Kashim Shettima ya ce an cika alkawarin da Tinubu ya daukar wa al'ummar Tudun Biri.
Kashim Shettima tare da Gwamna Uba Sani wajen kaddamar da sababbin gidaje a Tudun Biri. Hoto: @KashimSM
Source: Twitter

Sauye-sauye a tsarin ginin da aka yi

Shugabar hukumar NEMA, Zubaida Umar, ta bayyana cewa tun farko an tsara gina gidaje 143 ne, amma aka mayar da gidaje 10 zuwa ginin makaranta domin amfanin yaran yankin, wanda hakan ya bar gidajen mutane guda 133.

Mazauna garin, ciki har da Mrs. Aisha Haruna da Solomon John, sun nuna matuƙar godiyarsu ga Shugaba Tinubu da Mataimakin sa bisa cika alkawarin da suka ɗauka na dawo musu da martabarsu da matsuguninsu.

Kara karanta wannan

An 'gano' wani shiri da masu juyin mulki suka yi domin hana Buhari ba Tinubu mulki

Muhimman ayyuka 3 a Tudun Biri

Tun da fari, mun ruwaito cewa, Gwamnan Kaduna, Uba Sani, ya kaddamar da fara muhimman ayyuka uku a kauyen Tudun Biri da ke ƙaramar hukumar Igabi a Kaduna.

Daga cikin ayyukan da gwamnan ya kaddamar da farawa har da ginin titi mai tsawon kilomita 5.5 wanda ya haɗa ƙauyen da titin zuwa filin jirgin sama na jihar.

Waɗannan ayyuka na zuwa ne biyo bayan ibtila'in da ya afku ranar 3 ga watan Disamba, 2023 lokacin da sojoji suka yi kuskuren jefa bam kan ƴan Maulidi a Tudun Biri.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com