Abu Ya Girma: Yan Sanda Sun Kutsa har Masallacin Juma'a, Sun Kama Malamin Musulunci

Abu Ya Girma: Yan Sanda Sun Kutsa har Masallacin Juma'a, Sun Kama Malamin Musulunci

  • An lakadawa wani bawan Allah mai suna, Najeem Hammed duka har lahira a kusa da wani masallacin Juma'a a jihar Osun
  • Rahotanni sun nuna cewa lamarin ya auku ne lokacin da mutumin ya je sallar asubah, 'yan sanda sun kama limamin masallacin
  • Rundunar yan sanda ta ce ta kama mutum hudu kan lamarin ciki har da limamin masallacin domin gudanar da bincike

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Osun, Nigeria - Rundunar ’Yan sandan Jihar Osun ta kama Babban Limamin masallacin Jumu'a na Ummu Hanni Adigu da ke yankin Ogo-Oluwa a birnin Osogbo, tare da wasu mutum uku.

Dakarun 'yan sanda sun kama su ne biyo bayan mutuwar wani mai fentin mota, Najeem Hammed, bayan wani rikici da ya faru tsakaninsa da masu ibada da safiyar yau Juma'a.

Jihar Osun.
Taswirar jihar Osun a Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

The Nation ta ce wannan lamari ya jawo tashin hankali a ranar Juma’a, inda ’yan uwan mamacin suka dakatar da sallar Juma’a a masallacin domin nuna bacin ransu kan abin da ya faru.

Kara karanta wannan

Mutum 2 sun mutu a hanyar zuwa jana'izar mataimakin gwamnan da ya rasu a Najeriya

Yadda aka yi kisa a kusa da masallaci

Rahotanni sun nuna cewa Najeem, ya je masallacin ne da misalin karfe 6:00 na safe domin yin sallar asuba, inda aka samu sabani tsakaninsa da wasu mutane.

Wata majiya a kusa da masallacin ta ce rigimar ta samo asali ne bayan an idar da sallah lokacin da limami ya fara nasiha, wanda hakan ya kai ga dambarwa tsakanin Najeem da wasu masallata.

Majiyar ta ce al'amarin ya kazance har ta kai ga an fitar da Najeem daga cikin masallacin, kuma aka lakada masa dukan kawo wuka a waje.

Jami’an ’yan sanda daga ofishin Ataoja sun isa wurin bayan samun kiran gaggawa, inda suka kwashe shi zuwa asibiti amma daga baya aka tabbatar da mutuwarsa.

Masu zanga-zanga sun hana Sallah

Bayanai sun nuna cewa dangin mamacin sun yi zanga-zanga a kofar shiga masallacin, inda suka dage kan cewa ba za a yi sallah ba sakamakon abin da ya faru.

Kara karanta wannan

Sojoji sun kai hari kasuwa a Yobe bayan samun bayanai kan Boko Haram

Wannan zanga-zanga ta dakatar da harkokin masallacin, wanda hakan ya sa jami’an ’yan sanda suka shiga tsakani tare da tafiya da Babban Limamin domin yi masa tambayoyi.

Bayan hakan, wasu masu zanga-zangar sun mamaye kofar masallacin, sun hana masu ibada shiga tare da yin gargadin kada a yi kokarin gudanar da sallar Juma'a.

Yan sanda.
Jami'an yan sanda suna aikin sintiri a cikin gari a Najeriya Hoto: @PoliceNG
Source: Getty Images

Martanin hukumar 'yan sanda

Kakakin rundunar ’yan sandan jihar Osun, Abiodun Ojelabi, ya tabbatar da faruwar lamarin, kamar yadda jaridar Tribune Nigeria ta kawo.

Ya bayyana cewa:

"Ba a cikin masallaci aka aikata wannan danyen aiki ba, sai da aka fito waje. Mun kama Limamin da wasu mutum uku da ke da alaka da lamarin. Mun kaddamar da bincike domin gano ainihin abin da ya janyo faruwar hakan."

Kotu ta tura limamin masallaci gidan yari

A wani rahoton, kun ji cewa wata kotu a Kasar Ingila ta yanke wa wani limamin masallaci hukuncin zaman gidan yari na makonni 15.

Kotun ta daure limamin masallacin ne bayan kama shi da laifin daura auren yara 'yan shekara 16 da haihuwa a masallacinsa ba tare da bin doka da ka'idoji ba.

A gaban kotu, Osmani ya bayyana cewa bai san dokar kasar ta sauya ba, wadda ta daga mafi karancin shekarun aure a kasar Ingila zuwa shekara 18.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262