Minista Ya Dauko da Zafi, Ya Fara Shirin Garkame Ma'aikatan Abuja a Gidan Yari

Minista Ya Dauko da Zafi, Ya Fara Shirin Garkame Ma'aikatan Abuja a Gidan Yari

  • Nyesom Wike ya fara shirin tura ma'aikatan Abuja gidan yari saboda kin janye yajin aiki kamar yadda kotun masana'antu ta bada umarni
  • Lauyan Wike ya karbo takardar gargaɗi ta Fom 48 wadda ke nuna cewa shugabannin kungiyar JUAC za su fuskanci hukuncin zaman yari
  • Mazauna birnin tarayya Abuja sun shiga tsaka mai wuya yayin da asibitoci da makarantu suka ci gaba da kasancewa a rufe saboda yajin aikin

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Ministan birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya ɗauki zafafan matakan shari'a domin tura shugabannin ma'aikatan FCTA gidan yari sakamakon ƙin bin umarnin kotu na janye yajin aiki.

Duk da umarnin babbar kotun masana'antu na ranar 27 ga Janairu, 2026, wanda ya hana ci gaba da yajin aikin, ma'aikatan sun dage kan lalle ba za su koma aiki ba, tare da dogara da ɗaukaka ƙarar da suka shigar.

Kara karanta wannan

Sojoji sun yi lalata da mata, sun tatsi talakawa a Cross River? Gaskiya ta fito

Wike ya yi barazanar daukar matakin shari'a don garkame ma'aikatan Abuja.
Ministan Abuja, Nyesom Wike yana duba wani aiki da ake gudanarwa a birnin tarayya. Hoto: @GovWike
Source: Twitter

Wike ya yi wa ma'aikatan Abuja gargadin karshe

Wannan taurin kai ya sa Wike, ta hannun lauyansa Dr. James Onoja (SAN), ya karɓo takardar "Fom 48" daga kotu, wadda ita ce matakin farko na gurfanar da mutum kan zargin raina kotu, in ji rahoton The Sun.

Takardar, mai taken "Sanarwa kan sakamakon ƙin bin umarnin Kotu," tana gargaɗin shugabannin ƙungiyar JUAC cewa muddin ba su bi umarnin Mai shari'a E.D. Sublimi ba, za a tura su gidan yari kai-tsaye.

Wasiƙar ta bayyana cewa:

"Ku sani cewa muddin ba ku bi umarnin da alkali ya bayar ranar 27 ga Janairu, 2026 ba, kun aikata laifin raina kotu kuma za a tura ku gidan yari."

Takun-saka tsakanin Wike da ma'aikata

Lauyoyin Wike sun bayyana cewa shigar da ɗaukaka ƙara ba ya nufin ma'aikata su ci gaba da yajin aiki, face idan kotu ta bayar da wani umarnin na musamman na dakatar da hukuncin farko.

Kara karanta wannan

Asiri ya tonu: An fallasa yadda aka shirya kashe Tinubu, Shettima da wasu mutum 2

A gefe guda, Punch ta rahoto shugabannin ƙungiyar JUAC, Rifkatu Iortyer da Abdullahi Umar Saleh, sun bayyana cewa suna da haƙƙin jiran matakin kotun ɗaukaka ƙara kafin su yanke shawara.

Justice Sublimi ya yi amfani da sashi na 18(1)E na dokar takaddamar ciniki, wanda ya bayyana cewa dole ne a dakatar da kowane irin yajin aiki da zarar an kai maganar gaban kotun masana'antu.

Mazauna Abuja sun shiga damuwa saboda rufewar asibitoci sakamakon yajin aiki
Likitoci sun yi layi layi a makarantar koyon aikin jinya. Hoto: @nard_nigeria
Source: Twitter

Me zai faru nan gaba?

Idan har ma'aikatan suka ci gaba da taurin kai bayan an ba su wannan sanarwar, mataki na gaba shi ne fitar da "Fom 49", wanda shi ne umarnin kama su kai-tsaye domin fuskantar shari'ar raina kotu.

Wannan dambarwa ta jefa mazauna Abuja cikin fargaba, musamman ganin yadda asibitoci da makarantu suka kasance a rufe na tsawon kwanaki huɗu duk da umarnin kotun masana'antu.

Yajin aiki: An rufe asibitoci a Abuja

A wani labari, mun ruwaito cewa, marasa lafiya sun shiga garari sakamakon yajin aikin kungiyar JUAC wanda ya jawo janyewar likitoci daga asibitocin gwamnati a Abuja.

Ma'aikatan Abuja karkashin jagorancin Femi Falana sun daukaka kara kan hukuncin kotun masana'antu da ya umarce su da su koma aiki.

Ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike ya yi barazanar daukar mataki kan duk ma'aikacin da ya ki komawa bakin aiki yayin da yajin aikin ke kara tsananta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com