Burgediya Janar Sadiq: Bayanai da Muka Sani kan Zargin Sojan a Yunkurin a 'Juyin Mulki'
- Sojojin Najeriya sun tabbatar da yunƙurin juyin mulki da aka shirya kifar da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu, inda aka cafke jami’ai 16
- Daga cikin wadanda aka cafken akwai Birgediya-janar Musa Abubakar Sadiq wanda ake zargin babba ne a yunkurin kifar da gwamnatin
- Bincike ya nuna cewa ana zargin Sadiq da sanin shirin juyin mulkin tun da wuri amma bai sanar da hukumomi ba
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja – Bayan dadewa ana rade-radin yunƙurin juyin mulki, rundunar sojin Najeriya ta tabbatar da shirin kifar da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Majiyoyi sun bankado cikakkun bayanai kan rawar da Birgediya-Janar Musa Abubakar Sadiq ya taka a lamarin.

Source: Facebook
Janar Sadiq na daga cikin jami’an soji 16 da aka kama kuma aka tsare a watan Oktoban 2025 bisa zargin yunƙurin juyin mulki, cewar rahoton Premium Times.

Kara karanta wannan
Kanal Ma'aji: Abin da muka sani kan sojan da ya jagoranci yunkurin kifar da Tinubu
Yadda aka cafke sojoji kan zargin
Rahotanni sun nuna cewa wannan makirci ne ya sa gwamnati ta soke bikin Ranar ‘Yancin Kai ta 1 ga Oktoba.
Daga cikin jami’an da aka cafke, 14 daga rundunar soji suke, yayin da sauran biyu suka fito daga sojojin sama da kuma na ruwa.
Daga bisani kuma, an sake cafke wasu jami’ai da fararen hula da ake zargi suna da hannu a lamarin.
Da farko, hukumomin soji sun yi ƙoƙarin musanta batun juyin mulkin, suna mai cewa ana binciken jami’an ne kawai kan rashin da’a da karya doka.

Source: Facebook
Zargin da ake yi wa Burgediya Janar Sadiq
Duk da cewa wasu rahotannin leken asiri sun nuna Janar Sadiq a matsayin wanda ake zargi da jagorantar shirin, majiyoyi sun bayyana cewa babban laifin da ake masa shi ne sanin shirin tun da wuri da kuma kasa kai rahoto, ba wai kai tsaye ya shiga ciki ba.
Majiyoyin soji sun ce rawar da ya taka ta fi kama da mai laifi daga gefe fiye da shiga aikata laifin dumu-dumu.
Sun ce an sanar da shi shirin juyin mulkin daga wasu da ke cikin masu tsara makircin, amma bai kai rahoto ga manyan hukumomi ba.

Source: Twitter
Wanene Burgediya Janar Musa Sadiq?
An haifi Musa Abubakar Sadiq a ranar 3 ga Janairu, 1974. Jami’in soja ne mai lambar aiki N/10321, dan Jihar Nasarawa, kuma yana cikin rundunar Infantry.
Ya yi karatu a Kwalejin Tsaro ta Najeriya (NDA) daga 1992 zuwa 1997, a matsayin dalibi na Regular Course 44, ya zama Kanari (Colonel) a 2015, sannan aka ɗaga shi zuwa Birgediya Janar bayan shekaru huɗu.
A aikinsa, ya riƙe manyan muƙamai da dama, ciki har da Kwamandan Birgade ta 3 a Kano da kuma 'Garrison Commander' na Rundunar 81 a Lagos.
Tarihin zarge-zarge a kansa
Ba wannan ne karo na farko da yake fuskantar bincike ba, a watan Oktoban 2024, an tsare shi bisa zargin cin hanci, ciki har da karkatar da shinkafar tallafi da sayar da kayan sojoji.
Ko da yake wadannan zarge-zarge daban suke da batun juyin mulkin, sun sake bayyana yayin da ake sake duba tarihin aikinsa.

Kara karanta wannan
An 'gano' wani shiri da masu juyin mulki suka yi domin hana Buhari ba Tinubu mulki
Har yanzu rundunar soji ba ta fitar da cikakken bayani na hukuma kan halin da shari’ar take ciki ba, amma majiyoyi sun ce bincike na ci gaba.
Juyin mulki: Bayanai game da Kanal Ma'aji
A wani labarin, ana samun wasu bayanai kan yunkurin da wasu sojoji suka yi na kifar da gwamnatin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu.
Majiyoyi sun gano babban jagoran da ya jagorancin yunkurin kifar da gwamnatin yayin da ake ci gaba da gudanar da bincike.
An samu bayanai kan Kanal Mohammed Ma'aji wanda aka gano a matsayin jagoran shirya yunkurin juyin mulkin.
Asali: Legit.ng
